An Bukaci Trump Ya Cire Sudan Daga Kasashen ‘Yan Ta’adda
Talata, 3 Disamba, 2019
An Bukaci Trump Ya Cire Sudan Daga Kasashen ‘Yan Ta’adda

Manyan shugabannin Sudan sun rattaba hannu kan wata budaddiyar wasika tare da rokon shugaban Amurka Donald Trump ya cire kasar daga jerin kasashen da ke tallafawa ‘yan ta’adda. Wasikar wadda ‘yan siyasa da malaman jami’a da masu fafutuka da kwararru kan harkokin kasashen waje suka rubuta, ta ce bai kamata a hukunta Sudan kan laifin da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir ta aikata ba, wanda aka hambarar da gwamnatinsa bayan kazamar zanga-zangar da aka yi a daukacin kasar.

A shekarar 1993 ne Amurka ta sanya Sudan a jerin kasashen da ke daukar nauyin ‘yan ta’adda, bayan an zarge kasar da tunzura masu ikirarin jihadi. A wancan lokacin shugaban kungiyar al-qa’ida Osama Bin Laden da mambobinsa na daga cikin wadanda ke zaune a kasar Sudan.

Daya daga cikin mutum 79 da suka rattaba hannu kan wasikar ita ce Sara Abdigalil, shugabar kungiyar likitocin Sudan wadda ke Birtaniya ta shaida wa BBC cewa ta ce takunkumin Amurkar ya janyowa tattalin arzikinsu koma baya da janyo masu zuba jari janyewa daga kasar. ”Abubuwa sun sauya,” in ji ta.

Ta kara da cewa ”Janye takunkumin zai yi matukar tasiri da muhimmanci ba wai ga mutanen Sudan kadai ba, har da duniya baki daya. “Idan ana maganar ta’addanci a kasar da tattalin arzikinta ke cikin halin ni ‘ya su, zai yi wuya a iya magance matsalar ta’addancin da a yanzu duniya ta mayar da hankali akai.”

Source: Leadership A Yau