Burkina: Jama'a na nuna goyon baya ga sojoji
Laraba, 26 Janairu, 2022
Burkina: Jama'a na nuna goyon baya ga sojoji
Burkina: Jama'a na nuna goyon baya ga sojoji

kasashen duniya na ci gaba da yin Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Burkina Faso inda suka kifar da gwamnatin mulkin farar hula ta Roch Marc Christian Kaboré. Babban sakataran MDD Antonio Guterres, ya ce ba za su taba amincewa ba da juyin mulkin sojoji ba a yammacin Afirka wanda ya yi kira ga sojoji da su kare kasashensu daga 'yan ta'adda a maimakon kodayen kwatar mulki.Tun farko kungiyar ECOWAS da kungiyar tarayar Afirka sun yi Allah wadai da juyin mulkin. Dubban jama'a a Burkina Faso sun gudanar da gamgami na nuna goyon baya ga sojojin da suka kifar da gwamnatin farar hular.

Source: DW