EL-Sisi ya taya yan kungiyar kwallon kafa ta Olympic murna: Matsan Misra sun yi Sabuwar nasara
Lahadi, Nuwamba 24, 2019
EL-Sisi ya taya yan kungiyar kwallon kafa ta Olympic murna: Matsan Misra sun yi Sabuwar nasara

Shugaban Misra Adulfattah El-Sisi ya taya al'ummar Misra murnar da Kungiyar kwallon kafar Olympic ta Misra don lashe Kofin Kasashen Afirka ta yan kasa da shekaru 23, da cancantar zuwa gasar Tokyo Olympic ta 2020.

Shugaban Misra Adulfattah El-Sisi ya faɗi a saƙonsa ta Facebook cewa: "Matasan Misra suna yi sabuwar nasara tare da jajircewa da kuma nacewa domin samun nasara, sabuwar nasara an kara zuwa nasarorin masu zuwa ga wannan grundunar matasa, wadanda su ne tushin girman kai kaunataccen kasarmu".

Kungiyar kasar kwallon kafar Olympic ta Misra ta yi nasarar akan Kungiyar kasar kwallon kafar Olympic ta Cote d'Ivoire da Kwallaye biyu da daya a wasan karshe na Kofin Kasashen Afirka ta yan kasa da shekaru 23.
Da ya tabbata da cewa Kungiyar kasar kwallon kafar Olympic ta Misra zata shiga ciki gasar Tokyo Olympic ta 2020.
Source: Yallakora