Kasar Sin Ta Shirya Gabatar Da Wasannin Olympics Na Lokacin Sanyi Mai Sauki, Tsaro Da Kayatarwa
Laraba, 26 Janairu, 2022
Kasar Sin Ta Shirya Gabatar Da Wasannin Olympics Na Lokacin Sanyi Mai Sauki, Tsaro Da Kayatarwa
Kasar Sin Ta Shirya Gabatar Da Wasannin Olympics Na Lokacin Sanyi

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin ta shirya tsaf, don gabatar da gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi mai sauki, tsaro da kayatarwa. Xi ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa (IOC) Thomas Bach, a gidan saukar baki na Diaoyutai dake nan birnin Beijing. Shugaba Xi ya bayyana cewa, komai ya kammala don gudanar da gasar Olympics ta lokacin sanyi a nan birnin Beijing, bayan da aka shafe sama da shekaru shida ana shiryawa. A ranar 4 ga watan Fabrairu ne, za a bude gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na 2022.

Source: Leadership Hausa