Mataimakin ministan harkokin kasashen waje ya bayyana kokarin kasar Misra na fadada harkar Sifiri (Tafiye tafiye) a Afirka a karkashin jagorancin shugaba " Abdul Fattah Sisi".
Laraba, Yuli 17, 2019
Mataimakin ministan harkokin kasashen waje ya bayyana kokarin kasar Misra na fadada harkar Sifiri (Tafiye tafiye) a Afirka a karkashin jagorancin shugaba " Abdul Fattah Sisi".

- Mataimakin Ministan kasashen wajen da suka shafi Afirka "Abubakar Hifini" ya tabbatar da kokarin kasar Misra na fadada harkar Sifiri (Tafiye tafiye) a Afirka a halin yanzu, kamar: hanyar jirgin Kasa ko Mota ko kuma jirgin sama, a karkashin shugabancin shugaba " Abdul Fattah Sisi" a matsayinsa na shugaban Kungiyar kasashen Afirka.

-Hifini ya bayyana muhimmancin yarjejeniyar samar da harkar Sifiri, domin kasancewarta jigo na ko wace yarjejeniyar kasuwanci na bai daya, kuma jigo da ya shafi harkar tafiye tafiye, wannan shine kokarin da kasar Misra take yi ta hanyar tattaunawa ta musamman da wasu kasashe akan ka'idojin samar da harkar Sifirin da kuma yarjejeniyar kasuwancin bai daya a Afirka.

-Ya ce a yanzu kanfanin jirgin sama na Misra (Egypt Airlines) yana gudanar da tafiye tafiye zuwa Birnin (Kigali) na kasar Rwanda, da Birnin (Douala) na kasar Kamaru, kamfanin jirgin sama na Misra yana zagaye Afirka. Ya kuma bayyana cewa ana gudanar da aikin samar da kamfanin Sifirin ruwa na kasa a Afirka, da wata hanyar tafiye tafiyen ta ruwa a Afirka wadda ake kira da suna (Fik mid) wadda zata hada tsakanin kogin ( Victoria) zuwa ( Bahrul mutawassid).

-Mataimakin Ministan ya tabbatar da muhimmancin Kafafen yada labarai a Afirka, domin bibiyar Abubuwan da suke faruwa a Afirka Kafafen yada labaran yamma ne (Turai) ko kuma na gabas (Larabawa) suke kula dasu ba kafafen yada labaran Afirka ba, a karshe labarai maras inganci su rika isuwa garemu daidai da bukatun kasashen da suke mallakar wadannan gidajen Radio, ko kuma kamfanonin yada labarai.

Source: Shorouk