A lokacin ziyararsa zuwa Misra: Ministan harkokin kasashen wajen Armenia ya sanar da hadin gwiwar kasarsa da kuma goyon bayanta ga kasar Girka da Kuburus da Misra akan hakkokinsu a kogin Mutawassid
Litinin, Satumba 14, 2020
A lokacin ziyararsa zuwa Misra: Ministan harkokin kasashen wajen Armenia ya sanar da hadin gwiwar kasarsa da kuma goyon bayanta ga kasar Girka da Kuburus da Misra akan hakkokinsu a kogin Mutawassid


Ministan kasashen wajen Misra " Samih Shukry " da Ministan kasashen Armenia Zohrab Mnatsakanyan sun tabbatar da dangantakar taimakekeniya mai zurfi da ta hada kasashen biyu a bangarori daban daban, hakan ya zo ne a lokacin taron manema labarai wabda ya hada Ministocin biyu a jiya Lahadi, a karshen tattaunawar da suka yi a ma'aikatar kasashen waje.
Yayin da Shukry ya bayyana cewa tattaunawar ta tabo batun dangantaka da ta hada kasashen biyu a fagen siyasa da tattalin arziki da kuma dangantaka mai zurfi a tsakanin al'umar kasashen biyu, da kuma kasancewar wani yanki mai yawa na al'ummar Misra yan asalin kasar ta Armenia wadanda suka zamo wani yanki na al'ummar Misra wanda muke alfahari da su. Ya kuma bayyana cewa an tattauna kokarin kasashen biyu akan yakar annobar Korona da kuma muhimmancin aikin hadin gwiwa domin fuskantar kalu-balen da ke kan iyakokin kasa, bugu da kari yawaita ziyarori da kuma gayyatar da aka yi wa shugaba Abdul fatah Al-sisi domin kai ziyara Kasar Armenia wadda za a sa ranar ta. Shukry ya tabbatar cewa akwai manufar siyasa mai karfi domin karfafa dangantakar siyasa da tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu, yana mai jan hankali cewa akwai mahanga da ta hada kasashen biyu game wasu batutuwa, ya kuma ce za mu ci gaba da hadin gwiwa mai karfi domin tabbatar da dangantakar da hada kasashen biyu.