Misra tana tallafa wa zaman lafiya da cigaba a yankin kasashen Larabawa da na Afirka.
Talata, Oktoba 15, 2019
Misra tana tallafa wa zaman lafiya da cigaba a yankin kasashen Larabawa da na Afirka.

Ministan harkokin kasashen wajen Misra Samih Shukry ya tabbatar da cewa shugaba Abdul Fattah Sisi yana da cikakkiyar masaniya dangane da kalu-balen da yake fuskantar Misra, yayin da ya fara gyare-gyare masu fadi musamman a fannin tattalin arziki da zuba jari, da kuma samar da damanmakin aiki da rage yawan masu zaman kashe wando da rashin aikin yi da kyautata farashin kayayyakin masarufi. Ministan harkokin kasashen wajen a jawabinsa da ya yi a ranar Litinin 14- 10- 2019 a babban Birnin kasar Namsa (Vienna) ya ce yana sa ran karin shigowar masu saka hannun jari na kasashen waje zuwa Misra a lokuta masu zuwa.
Ya kuma bayyana damuwar kasar Misra akan rashin kwanciyar hankali da kasashe masu yawa suke fama da shi a yankin kamar: Libiya da Yamen. Ya kuma bayyana cewa siyasar Misra ta kasashen waje ta kafu ne akan rashin yin katsalandan a harkokin wasu kasashe, da zurfafa taimakekeniyar kasa da kasa tare da dukkanin kasashen duniya, ya kuma yi nuni ga wasu shirye-shirye masu burin inganta tattalin arzikin kasar Misra domin samun cigaba mai dorewa.