Shugaba Abdul fatah Al-sisi da Shugaba Macron: tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin shi ne mafi muhimmanci ga Misra da Faransa
Asabar, Satumba 12, 2020
Shugaba Abdul fatah Al-sisi da Shugaba Macron: tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin shi ne mafi muhimmanci ga Misra da Faransa


A yammacin ranar juma'a ne Shugaba Abdul fatah Al-sisi ya Amsa kiran waya daga Shugaban kasar Faransa " Emmanuel Macron.
Mai magana da yawun fadar shugaban kasa ya bayyana cewa kiran wayar ya tattauna batutuwa da dama da suke da muhimmanci tsakanin Misra da Faransa, da kuma musayar ra'ayoyi game da ci gaban yankunan su, haka kuma an tattauna hanyoyin karfafa taimakekeniya tsakanin kasashen biyu a dukkanin bangarori.
A lokacin kiran wayar an tabbatar da batun hadin gwiwar maslahohin da suka hada kasashen biyu a yankin gabas ta tsakiya ba tare da mamaye abin da zai shafi maslahohin yankin ba, sai dai cewa cimma samar da tsaro da zaman lafiyar yankin shi ne abu na farko da zai kawo bukatar hadin gwiwa tsakanin Misra da Faransa. Abin da kuma ya shafi batun Libiya an tabbatar da matsayin kasashen biyu na goyon bayan mafitar siyasa don kawo karshen rikicin kasar ba tare da katsalandan daga kasashen waje ba, tare da maraba da duk wani mataki mai kyau na kokarin kasashe masu kai komo domin samar da zaman lafiya a kasar ta Libiya, daga ciki akwai shirin Alk'ahira wanda ya zo daidai da matakin Berlin.