Shugaba Abdul fatah Al-sisi ya kira Sarkin Bahrain ta waya ya taya shi Murnar shirin zaman lafiya mai cike da tarihi
Asabar, Satumba 12, 2020
Shugaba Abdul fatah Al-sisi ya kira Sarkin Bahrain ta waya ya taya shi Murnar shirin zaman lafiya mai cike da tarihi


A yammacin ranar juma'a ne Shugaba Abdul fatah Al-sisi ya kira Sarkin Bahrain Sheikh Hamdi Bn Isa Ali Khalifa domin taya shi murnar shirin zaman lafiya mai cike da tarihi wanda Kasar Bahrain ta yi, wanda hakan zai bude bangarorin cimma zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya da kuma kawo cikakken daidaito a batun kasar Falasdin.
A nasa bangaren Sheikh Hamdi bn Isa ya bayyana cikakkiyar godiya da girmamawa game da wannan abin yabawa da Shugaba Al-sisi ya yi, da kuma kokarinsa a koda yaushe na samar da tsaro da zaman lafiya a yankin domin gudun mawar Misra mai tarihi na wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya