Shugaba Abdul Fatah Al-sisi ya tarbi takwaransa na Aljeriya Abdul Majid Tabun.
Laraba, 26 Janairu, 2022
Shugaba Abdul Fatah Al-sisi ya tarbi takwaransa na Aljeriya Abdul Majid Tabun.
Shugaba Abdul Fatah Al-sisi ya tarbi takwaransa na Aljeriya Abdul Majid Tabun

A yammacin ranar Litinin 24/1/2022 Shugaba Al-sisi ya tarbi takwaransa Shugaban ƙasar Aljeriya Abdul Majid Tabun a filin jirgin sama na Alƙahira, mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa Jakada Bassam Radi ya yaɗa hotunan tarbar da Shugaba Abdul Fatah Al-sisi ya yi wa takwaransa na Aljeriya Abdul Majid Tabun wanda ya kawo ziyarar aiki ta kwana biyu a Misira. A lokacin da Shugaba Al-sisi yake tarbar takwaran nasa na Aljeriya an rera taken ƙasa, inda wata tattaunawa da ke nuna ƙaunar juna ta wakana a tsakanin Shugabannin biyu.