Sudan: sabon karin bayani akan yarjejeniya tsakanin Humaidati da Akkar
Laraba, 18 Disamba, 2019
Sudan: sabon karin bayani akan yarjejeniya tsakanin Humaidati da Akkar

Gwamnati da kungiyar fararen hula na Arewa, bangaren Akkar sun rattaba hannu a garin Juba akan yarjejeniyar kai taimakon jinkai ga yan kasa a kudancin Kurdifan da Ninul Azrak, mataimaki na farko na shugaban Majalisar rikon kwarya shugaban tawagar wakilai Muhammad Hamdan Daklu ne ya sanya hannu a madadin gwamnati, yayin da shugaban Kungiyar fararen hula Malik Akkar ya sanya hannu a madadin kungiyar, wanda ya sanya hannu a madadin mai shiga tsakani shi ne mai ba Shugaban kasar Sudan ta kudu shawara akan harkokin tsaro Tut Kalwak.

Kungiyar ta fararen hula domin kwato 'yancin al'umar Sudan ta Arewa a karkashin jagorancin Akkar ta dauki sanya hannu a yarjejeniyar a matsayin abin da zai magance batun jinkai a yankin na kudancin Kurdifan da Ninul Azrak. Ta ce wannan yana nuna hadin kan masu zanga-zangar da kuma gwamnati zai kuma hanyoyin wasu batutuwa. Arman ya yi kira kan cewa mafita ita ce sanya hannu a yarjejeniyar da kuma hadin gwiwa domin kawo karshen wahalhalun da yan kasa suke sha. Ya bayyana cewa daidai da wannan yarjejeniya za a kafa kwamitin hadin gwiwa domin kula da bukatun jinkai da wadatar da kayan taimako da bude hanyoyi domin isar da kayayyakin bukata na jinkai ga mutanen da yaki ya shafa a wadancan yankuna. Ya kara da cewa yarjejeniyar ta yi magana akan samar da hanyoyin bibiya da kuma domin isar da kayayyakin tallafi a yankunan da kungiyar take da tasiri a kudancin Kurdifan da Jibali Nuba da Nilul Azrak.