Sudan Ta Nemi Amurka Ta Cire Ta a Jerin Kasashe Masu Goyon Bayan Ta'addanci.
Alhamis, 3 Oktoba, 2019
Sudan Ta Nemi Amurka Ta Cire Ta a Jerin Kasashe Masu Goyon Bayan Ta'addanci.

Bayan da ta kwashe watanni tana fama da rikita-rikitar siyasa, wacce ta yi sanadin hambarar da gwanatin Omar Al-Bashir, gwamnatin wucin gadin kasar Sudan, na neman a cire kasar daga jerin sunayen kasashen da Amurka ta yafa masu rigar masu daukan nauyin ayyukan ta’addanci.

A cewar jami’an gwamnatin kasar, cire sunan Sudan daga jerin sunayen, zai taimaka wa tattalin arzikinta wajen farfadowa, wanda yake fuskantar kalubale tun bayan da aka kawar da Al-Bashir.

A shekarar 1993 Amurka ta saka Sudan a jerin kasashe masu goyon bayan ta’addanci, kan wasu tuhume-tuhume da aka yi wa gwamnatin tsohon Shugaba Al-Bashir na mara baya ga ayyukan na ta’addanci.

Sannan Amurka ta sakawa kasar takunkumi kan zargin goyon bayan kungiyoyin ta’addanci irinsu Al Qaida da Hamas da kuma Hezbollah.

Source: VOA