Tattaunawa akan harkar kasuwanci tsakanin Najeriya da kasar Ghana
Lahadi, Satumba 06, 2020
Tattaunawa akan harkar kasuwanci tsakanin Najeriya da kasar Ghana

Gwamnatin tarayyar Najeriya ce za ta bayyana  hanyoyin difulomasiyya domin warware rikicin kasuwanci tsakanin 'yan kasuwar Najeriya da suke Ghana da kuma Mahukuntan kasar, Ministan kasuwanci da zuba jari Otumba Richard Adeni Adebayo ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.
Shafin " Nira Mitrax" na Najeriya ya ambato cewa Ministan ya jagoranci tawagar Najeriya  a lokacin gudanar da tattaunawar kasashen biyu tare da Ministan kasuwanci da kere-kere na kasar Ghana Alan John Kawado Karematin, ya bayyana dangantakar Manyan kasashen biyu masu karfin tattalin arziki a Yammacin Afirka, yana mai nuni da cewa ana bukatar warware batun ne ta hanyar difulomasiyya. Adebayo ya kara da cewa shawarwari suna gudana tsakanin kasashen biyu domin tabbacin kawo karshen wannan lamari cikin ruwan sanyi