Buhari Ya Nada Shugabannin Hukumar Nakasassu
Laraba, 26 Agusta, 2020
Buhari Ya Nada Shugabannin Hukumar Nakasassu

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Majalisar Gudanarwa tare da Babban Sakatare na sabuwar Hukumar Kula Da Nakasassu ta Kasa, wato National Commission for Persons with Disabilities, kamar yadda Dokar Hana Wariya Ga Nakasassu ta 2019 ta tanadar.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Femi Adesina, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya bayar a ranar Litinin.

Hukumar za ta kasance ne a karkashin Ma’aikatar Harkokin Agaji tare da Jinkai ta Tarayya inda a yanzu Hajiya Sadiya Umar Faroukh ta ke minista.

Dokar dai ta tanadi cewa za a samar da shugaba tare da membobi shida wadanda dukkan su nakasassu ne daga sassan kasar nan guda shida wadanda za su jagoranci Majalisar Gudanarwar hukumar na tsawon shekara hudu, kuma za a iya kara masu wa’adin shekara hudu na karshe, tare da amincewar Majalisar Dattawa.

Haka kuma dokar ta ce za a nada Babban Sakatare, wanda ke karkashin Majalisar Gudarwar, don aiwatar da ayyuka da tsare-tsaren hukumar, wanda kuma shi ma tilas ya kasance nakasasshe ne, kuma zai yi wa’adin shekara biyar, sannan za a iya dada masa wa’adin shekara biyar na karshe.

Sanarwar daga fadar shugaban kasa ta bada sunaye da mukaman wadanda aka nada da kuma yankin da su ka fito, kamar yadda shugaban kasan ya amince. Su ne kamar haka:

Hon. Dakta Hussaini Suleiman Kangiwa – Shugaba – daga Arewa-Maso-Yamma

Oparaku Onyejelam Jaja – Memba – Kudu-maso-Gabas

a yau