Edward Kallon: Tasiri Da Mahimmancin Kafafen Yada Labarai A Duniya
Litinin, 17 Faburairu, 2020
Edward Kallon: Tasiri Da Mahimmancin Kafafen Yada Labarai A Duniya

Babban jami’in harkokin yada labarai na Majalisar Dinkin Duniya, Mista Edward Kallon, ya bayyana cewa, kafafen yada labarai na da matukar muhimmanci da tasiri a duniya. Kallon ya bayyana haka a bikin ranar kafar yada labarai ta rediyo da a ka gudanar a Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa a Nijeriya. Ya ce; Majalisar Dinkin Duniya ta ware wanan ranar ne da nufin girmama matsayi na rawar da gidajen rediyo su ke takawa wajen fadakar da al’ummomi a duniya bakidaya. Ya kara da cewa kafar yada labarai ta radio itace kan gaba wajen wayar da alumma. Saboda aka sarin mutani dake rayuwa a karkara suna samun mahimman sako da kafar yada labarai na gidan radio ne. Hatta mutanen da su ke gona da ma karkarar da ba su mu’amala da wutar lantarki za ku tarar su na amfani da radiyo wajen jin halin da duniya ke cika. Ya kara da cewa, mutane su na kara samun ilimi da fahimta ta hanyar sauraron gidajen radiyo saboda shirye-shirye masu ilimintarwa da wayar da kai. Shirye-shiryen da gidajen radiyo ke yi ba wai ya kan tsaya a matsayin nishadi ba ne kawai, akwai ilimi mai zurfi a cikinsa.

Ya ce; Shugabannin Majalisar Dinkin Duniya sun nuna farin ciki da wanan ranar da aka ware domin masu sauraron gidajen radio.

Source:  a yau