Gamammiyar JNI, JIBWIS Da FIN Sun Yi Taron Mika Jagoranci Ga JIBWIS
Litinin, 24 Faburairu, 2020
Gamammiyar JNI, JIBWIS Da FIN Sun Yi Taron Mika Jagoranci Ga JIBWIS

A jiya Lahadi 23/2/2020 daidai da 28/6/1441H kungiyar hadaka ta ‘yan Agajin Jama’atu Nasrul Islam (JNI), da Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis-Sunnah (JIBWIS), da kuma Fityanul Islam Of Nigeria (FIN) dake babban birnin tarayya Abuja F.C.T, sun gabatar da babban taron ganawa da juna gamida miƙa ragamar jagorancin zuwa hannun JIBWIS. kungiyar hadakan dai dai a samar da ita ne sama da shekara goma sha biyu kenan da suka wuce Kuma cikin Ikon ALLAH tunda aka samar da wannan haɗaka sai ƙarin cigaba ake samu gameda ayyukan addini da kuma ƙara fahimtar juna a babban birnin tarayya da ma sauran jahohi. A yau dai jagorancin wannan tafiya ya bar hannun (JNI) inda ya koma hannun (JIBWIS), kuma wanda aka zaɓa a matsayin shugaba shine Alh. AHMAD JINGI ADAMU ( _National Comandant F.A.G JIBWIS. Wannan kujerar dai zai cigaba da jagorantarta ne har na tsawon shekaru hudu masu zuwa insha ALLAHU, kafin kuma a mika shugabancin zuwa ga hannun wata kungiyar. Majalisar hadakan ‘yan agajin (JIFAO) dai tanada wakilai daga kowace Ƙungiyar mutum goma sha daya,(11) inda ake da mutum talatin da uku (33) gaba daya.

Ga sunayensu da muƙamansu kamar haka:

1: Alh. Ahmad Jingi Adamu “JIBWIS” (Chairman)

2: Mal. Yusuf Gado “JNI” (Deputy chairman)

3: Alh. Muh’d Awwal Isa “FIN” (Assistant Chairman)

4: Alh. Mahmud Abdullahi “FIN” (Secretary General)

5: Muh’d Awwal Mu’az “JIBWIS” (Deputy Secretary)

6: Ahmad Baba Ibrahim “JNI” (Assistant Secretary)

7: Alh. Haruna D Yawa “JNI” (Organizing Secretary)

8: Mal. Musa I Isah Dodo “FIN” (Duputy Org. Sec)

9: Mal. Abdulmumin Yahya “JIBWIS” (Assistant Org. Sec)

10: Mal. Iliyasu T Gado “FIN” (Training Officer)

11: Mal. Awwal Adamu Kuje “JIBWIS” (Duputy Training Officer)

12: Muh’d J Muh’d “JNI” (Assistant Training Officer)

13: Mal. Salisu Muhammad “JIBWIS” (Discipline Officer)

14: Alh. Zubairu Ma’aji “FIN” (Deputy Discipline Officer)

15: Alh Haruna Pai “FIN” (Financial Secretary)

16: Alh. Shu’aibu Adamu Sabo “JNI” (Assistant .Fin. Sec)

17: Mal. Yahya Kawu Jibril “JNI” (Treasurer)

18: Awwal Rabi’u Rigachukun “JIBWIS” (General Auditor)

19: Mal. Lawal Musa Bangi “FIN” (Deputy Auditor)

20: Alh. Umar Isma’il “JIBWIS” (Legal Adbicer)

21: Barrister Umar Isah “JNI” (Deputy Legal Adbiser) 22: Alh. Yusuf A Aliyu “FIN” (Assistant Legal Adbiser)

23: Engr. Ahmad Yusuf Kardam “JNI” (Publicity Secretary) 24: Mal. Ibrahim Ahmad “JIBWIS” (Deputy Publicity Secretary)

25: Mal. Zayyanu Muhammad “JNI” (General Parade Commandant)

26: Mal. Hussaini B Adam “FIN”  (Deputy Parade Commandant)

27: Mal. Sulaiman Ahmad Funtua “JIBWIS” (Assistant Parade Cammandant)

28: Alh. Ibrahim A Sulaiman “JNI” (Joint Intelligent Officer) 29: Mal. Isma’il Aliyu “FIN” (Joint Intelligent Officer)

30: Mal. AbdulƘadir Musa “JIBWIS” (Joint Intelligent Officer)

31: Alh. Muh’d Angulu Bello “JNI” (Joint Intelligent Officer)

32: Mal. Muhammad Isa “JIBWIS” (Joint Intelligent Officer)

33: Mal. Sa’idu Danladi Karshi “FIN” (Joint Intelligent Officer)

Source:  a yau