Hatsabibancin Cutar Bacci (Insomnia)
Litinin, 26 Oktoba, 2020
Hatsabibancin Cutar Bacci (Insomnia)

Masana kimiyya sun tafi a kan cewa cutar bacci wani zaunannen abu ne, wanda a kowacce shekara a kan samu kaso 30 zuwa 40% na mutane da ke fama da wannan cuta. Shi cutan bacci wata alama ce da a ka ganewa, amma ba wai wani sharadi ba ne da a ka samar a kimiyyance. Sai dai shi wanda ke fama da cutar ne zai rika ji a jikinsa cewa wani abu na damunsa.

Cutar bacci ta kaso gida – gida ne. Akwai mutanen da su babban damuwansu shi ne za su iya fara bacci a kowanne hali kuma a kowanne lokaci, wasu kuma su na da matsalar rashin iya samun isasshen bacci, ko kuma farkawa a bacci da sauri ba tare da ya wadace su ba. Haka nan kuma wannan matsaloli da su ka shafi bacci, su na iya zama matsaloli ne na wucin – gadi, ma’ana za su addabi mutum ne na tsawon kwanaki ko makonni, wani lokaci kuma ya kan zama na tsawon zamani ne, daga watanni zuwa shekaru a na fama.
Ita cutar bacci ta ‘Insomnia’ a na daukarta a matsayin barazana ne yayin  da ya zama ta takurawa yanayin tafiyar da rayuwar mutum, misali shi ne mutum ya farka bacci amma ya rika jin wani irin kasala kamar bai yi baccin ba, ko kuma ya wuni cikin wani irin maye na jin bacci. Mutane masu yawan shekaru yanayin baccinsu yak an karanta, ba zai yiwu su rika bacci sosai kamar yadda su ke yi a lokacin da su ke da kananan shekaru ba. rashin bacci da yawa ga manya ba wani abin damuwa ba ne, ba shi da alaka da cutar bacci.
Masana kimiyya sun rarraba yanayin awowin da mutane ke bukata a matakin shekarunsu na haihuwa. Sabbin haihuwa (jarirai) su na bukatar bacci na awowi 13 zuwwa 17, Jarirai ‘yan shekaru 2 su na bukatar bacci na awowi 9 zuwa 13, Yara ‘yan shekaru 10 su na bukatar bacci na awowi 10 zuwa 11, matasa ‘yan shekara 16 zuwa 65 su na bukatar bacci na awowi 6 zuwa 9, haka kuma dattawa ‘yan sama da shekaru 65 su na bukatar baccin awowi 6 zuwa 8 ne.
Dattawa ko tsofaffi wadanda su ka haura shekaru 65 a duniya ba su wani bukatar bacci me yawa, kaso 25% kawai na bacci su ke bukata, ba kamar jarirai da matasa ba wadanda su ke bukatar bacci mai yawa, wanda ya kai kaso 50%.
Akwai wasu abubuwa da dama da ke janyo cutar bacci ta ‘Insomnia’. Cikinsu akwai yawaita tafiya a jirgin sama, masana sun ce musamman ma idan tafiyar ta kasance a na yawan yin ta daga Yammaci zuwa Gabashi ne, damuwa da yawan takaici, shanyewan bangaren jiki, yawan shan giya, abubuwan da ke da sindarin ‘Nicotine’ da ‘Caffeine’, talauci, rashin lafiya ko mutuwar wani makusanci.
Daga cikin alamomin kamuwa da wannan cutar ta bacci ‘Insomnia’ sun hada da mutum ya kasa daukan lokacin da ya dace ya na yin bacci, ko kuma ya kasance ya na yawan farkawa da sassafe, kuma ya gaza komawa baccin. Ko kuma ko da mutum ya kwashe awowi ya na bacci amma kuma ya tashi ya na jin jiri ko kuma baccin bai ishe shi ba. ko kuma mutum ya rika jin ciwon kai da rana kuma ya kasa gudanar da al’amura yadda ya dace.
Rashin samun wadataccen bacci wanda ke kawo cutar ta bacci na iya jefa mutum zuwa ga cutar mantuwa, wanda sai abin ya yi kamari a ke kai wa ga wannan cutar. A bisa al’ada cutar bacci ta ‘Insomnia’ ba ta da alaka da mugayen cututtuka irinsu cutar mantuwa. Cikin manyan cututtukan akwai cutar minshari. Wadanda ke yawan yin mishari a na shawartarsu da su je su ga likita, duk da cewa mutane masu kiba sun fi kamuwa da laruran minshari.
Daga cikin barazanar wannan cutar bacci idan ta yi kamari, ta kan jefa mutum ga gazawa a wurin aiki, sannan idan dalibi ne zai zamo ba ya fahimtar karatu yadda ya kamata, sannan kuma zai kasance me fuskantar barazanar hadari idan ya na tukin mota.        Masana sun tafi a kan cewa ita cutar bacci a na gane alamominta, kuma likitoci su na iya gane alamomin tun kafin cutar ta yi kamari. Likita ne zai fahimci ya tsarin baccinka yak e, shin ka na bin sharuddan da a ka gindaya? Likitanka zai sanar da kai cewa ka samarwa kanka da tsarin yin bacci na mako guda kuma ka chanza tsari. Idan kuma cutar ta yi kamari sai a dora mutum kan wasu tsararrun magunguna . sannan za a hana mara lafiyan yawan yin amfani da sinadaran ‘Nicotine’ ko shan giya da sauransu. Sannan za a sanar da mai fama da cutan a kan ya cire duk wata damuwa daga zuciyarsa.
Haka nan kuma masana sun tafi a kan cewa akwai bukatar a yi gwaji ga mutumin da ke fama da wannan cutar. Saboda zai yiwu akwai wasu cututtukan kwakwalwa da ya ke fama da su. Zai iya yiwuwa damuwa ce, ko takaicin wani lamari ya jefa shi ga cutar.
Likita idan ya yi wa mutum gwaji zai tura shi zuwa cibiyar da ke lura da wannan bangare na cutar bacci, su ne za sus a mutumin da ba shi da lafiya ya kwana a wurinsu, sannan su sa ka wasu na’urorin gwaji domin  gwada yanayin matakin da cutar ta ke a kai.
Daga cikin irin matakan da a ke dauka a kan maganace wannan matsalar akwai magungunan da likita ne ke bayarwa, sannan sai a koya mishi yadda zai rika tsara baccinshi da kuma irin abincin da zai rika ci, za a koya mishi yadda zai gyara dabi’unsa na rayuwa don kauracewa fadawa matsalolin da za su jefa shi ga wannan cuta.
Shi samar da tsarin samun bacci yadda ya kamata ya danganci yadda mutum ya ke sarrafa darensa. Haka nan har ma da yadda mutum ya ke sarrafa dabi’unsa.  Mutum na iya sanya wa kansa lokacin da zai fara bacci a farkon dare, wanda kuma zai kasance ba ya saba ma wannan lokacin.
Haka kuma akwai shawarar bai kamata mutum ya rika yawan mu’amala da dakin bacci ba, sai a lokacin da ya da mu’amala da haka. Bai kamata mutum ya ci chakuleti ko shayi ba kafin ya kwanta. Ka da mutum ya kwanta bacci ya na tunanin aiki ko wasu abubuwan damuwa. Mutum na iya karanta littafi ko yin wani aiki da zai taimaka masa ya rage damuwa.
Domin kauracewa wannan cuta mutum ya rika yin bacci a dai dai lokaci guda da ya tsara ko da kuwa a karshen mako ne. Mutum na da bukatar ya ragewa kansa damuwowi yayin da zai kwanta bacci, sannan ya rika yawan tunanin abubuwa masu amfani ba marasa amfani ba. idan kuma mutum na matsalar baya, zai iya kwanta amma sai ya sa matashin kai a kasan kafafunshi. Bai kamata mutum ya sha madara mai dumi, ko ya yi wanka da ruwan dumi ba yayin da ya ke gab da kwantawa.
Daga karshe, mutum na bukatar ya rika motsa jiki, idan motsa jiki cikin dare na hana ka bacci, sai ka mayar da lokacin motsa jikin da safe. Haka kuma mutum ya kaurace wa shan tabar sigari ko shan giya da yammaci ko dare. Sannan ya kamata mutum ya kaurace wa yawan kallon agogo, idan ma sai ya sa lokacin tashi, toh ya sa sai ya kawar da agogon daga yadda zai iya kallo.

a yau