Kamfanin NAHCO Zai Samar Da Tsarin Fitar Da Amfanin Gona kasar Waje
Litinin, 24 Faburairu, 2020
Kamfanin NAHCO Zai Samar Da Tsarin Fitar Da Amfanin Gona kasar Waje

Kamfanin Nigeria Aviation Handling ya jadda da kudurin san a habaka fannin nomad a kuma fitar da amfanin zuwa kasar waje. Hakan ya biyo bayan kara fadada kayan aikinsa don cimma nsarar fitar da amfanin gonar zuwa kasar waje da za su kai kashi 68 a cikin dari. Hakan yana da mahimmanci matuka, musamman ganin yadda gwamnatin tarayya ta sanya ake garkame iyakokin kasar na na kan tudu, inda hakan ya sanya Nijeriya take samar da abinci mai yawa wanda har za a iya fitar dashi zuwa kasar waje. Babbar Manajin Daraktan kamfanin na Nahco Abiance Uwargida Tokunbo Fagbemi c eta sanar da hakan a wajen baje kolin amfanin gonad a kamfanin ya shirya. A taron wanda shine karo na farko, Uwargida Tokunbo Fagbemi  ta cigaba da cewa, manufar kamfanin shi ne, ya dakatar da kin amincewar da akeyi da amfanin gonar da aka numa a kasar nan a wasu kasahen waje. Uwargida Tokunbo Fagbemi ta kuma bayar da tabbacin cewar, shekarar ta bana, zata yiwa kamfanin haske, inda ta kara da cewa, kamfanin zai kuma yi hadaka da wasu hukmi da masu ruwa da tsaki a fannin samar da amfanin gona. Uwargida Tokunbo Fagbemi ta sanar da cewa, kamfanin  na Nahco Abiance ya kuma kara yawan amfanin gonad a ya kai kimanin kashi 68 a cikin dari bayan an kasha dala miliyan 2 don fadada kayan aikin na kamfanin, inda ta kara da cewa, anyi hakan ne don a kara samar da wadataccen abinci. A cewar Uwargida Tokunbo Fagbemi yan watannin da su ka gabata, inda ta kara da cewa, muna kuma kara samun abokan hadda a kan kuurin namu. Ta sanar da cewa, binciken mu ana lalata amfanin gonar da aka fitar dasu zuwa kasar waje don sayarwa tun kafin si isa inda za a sauke su saboda karancin kayan aikin da za a adana su. A cewar Uwargida Tokunbo Fagbemi mun samu amincewar sarrafa kayan aiki na adana amfanin gona, wajen adana su da kuma tattara su waje guda. Uwargida Tokunbo Fagbemi a karshe ta sanar da cewa, hakan zai taimaka wajen magance kalubalen da ake fuskanat wajen fitar da amfanin gona zuwa kasuwannin duniya don sayarwa da kuma amincewa da amfanin gonar a cikin sauki.

Source: a yau