Kano Ta Sa Hannu A Yarjejeniyar Samar Da Lantarki Mai Karfin KVA-132
Litinin, Fabrairu 17, 2020
Kano Ta Sa Hannu A Yarjejeniyar Samar Da Lantarki Mai Karfin KVA-132

A kokarinsa na kara inganta harkokin tattalin arziki tare da bunkasa harkokin Masana’antu, domin amfanin al’ummar Kano, Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kammala shirye-shiryen samar da karin hasken wutar lantarki, inda ya rattabawa yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da Kamfanin samar da wutar lantarki (TCN), wanda a ka gudanar a masaukin Gwamnatin Jihar Kano da ke Asokoro a babban Birnin Tarayya Abuja, ranar Asabar da ta gabata, kamar yadda Babban Daraktan Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar ya shaida wa Jaridar Leadership A Yau. Gwamna Ganduje ya tabbatar da cewa, “samar da hasken wutar lantarki ga al’ummar Jihar Kano, abu ne wanda ya zama wajibi. Sannan, a shirye muke domin cika dukkanin wasu sharudda da ke cikin wannan yarjejeniya. Kazalika, za kuma mu dauki matakin gaggawa, domin aiwatar da wannan tsari. Don haka, abinda muke fata shi ne, dawo da martabar Jihar Kano ta hanyar farfado da Masana’antunmu.” Mun fahimcin wannan sabuwar yarjejeniyar fahimta ta (MoU), saboda haka yanzu Jihar Kano, za ta ci-gaba da samun hasken wutar lantarki ta hanyoyi uku zuwa hudu, a matsayin wannan Gwamnati, muna yin duk mai yiwuwa domin magance wannan matsala ta wutar lantarki. Haka kuma, muna kokarin yin amfani da damammakinmu, domin samar da harken wutar lantarki wanda hakan wani gagarumin cigaba ne kwarai da gaske a tare da mu.” Ya kara da cewa, shirin samar da hasken wutar lantarki wanda Gwamnatin Jihar Kano ke kan aikin yin sa a halin yanzu, wanda kuma ke kan matakin karshe na kammaluwa, ko shakka babu zai amfani masu Kananan Sana’o’i kasancewar za a cigaba da amfani da su wajen Noman Rani. Saboda haka, ba za mu sallama su baki-daya ga harkar samar da wutar lantarki kadai ba. “Wannan tasa na ke cewa, Kamfanin samar da hasken wutar lantarki na kasa (TCN), ya fara samar gagarumin cigaba domin ciyar da Jihar Kano gaba. Har wa yau, Kamfanoninmu za su dawo kan aiki kamar yadda suke a baya. Da aka gwada amfani da hasken lantarki mai amfani da hasken rana, mun fahimci wasu matsaloli a cikinta,” in ji shi. Gwamna Ganduje ya yi alkawarin cewa, zai kafa Kwamiti mai karfin gaske wanda zai kunshi hanyoyin samar da hanyoyin aiwatar da tsarin, domin karkare gagarumin aikin. “Za kuma mu hada hannu da sauran Aminanmu irin su Gwamnonin Jigawa da Katsina, domin ganin samun nasarar aikin.” Manajan Daraktan Kamfanin TCN, U.G Mohammed, wanda ya jagoranci kakkarfar tawagar zuwa Fadar Gwamnatin Jihar Kano, ya tabbatar da cewa da wannan sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna ta ‘MoU’ tare da aiwatar da ita, matsalar wutar lantarki za ta ragu kwarai da gaske idan ma ba a magance ta baki-daya ba. Ya cigaba da cewa, “idan muka magance matsalar samar da wutar, matsalar rarraba ta mai sauki ce, ina tabbatar maku da cewa raba hasken wutar lantaki ya fi komai sauki a wannan tsari.” Mohammed ya kara da cewa, tashar wutar lantarki ta Kumbotso, Dan Agundi da kuma Dakata, su na cikin wadanda za a kara wa karfi zuwa kaso 100%, ya tabbatar da cewa, “idan aikin sabuwar tashar ta kammala, Jihar Kano za ta kasance tashar da ta fi kowacce samar da ingantaccen hasken wutar lantarki a fadin kasar nan baki- daya. Hakan kuma, zai kara inganta harkar Masana’antu da sauran harkokin kasuwanci.” Takardar yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Jihohin Kano, Jigawa da Katsina da Kamfanin samar hasken wutar na kasa ta tsara samar da hasken wutar lantarki mai karfin 132KV da kuma wasu kananan tashoshin a Kazaure da Babura, wadanda za su samar da wuta mai karfin 60KVAd2 da kuma wuta mai karfin 132/33 da za a samar a Mashi, Tumin da kuma layin Katsina-Daura da ke kan aikin tashar Mashi. Kamar yarda yarjejeniyar ta nuna, kowacce jiha da su ka kunshi Kano, Katsina da Jigawa, za su tabbatar da hakkin mallakar samar da abubuwan da a ke bukata da biyan diyyar filayen da za a samar da tashoshin tsakanin Daura, Kazaure, Dambatta da kuma Babura. Haka zalika, kunshin yarjejeniyar ya nuna cewa, samar da filaye masu tsawon 300×33, domin gina tashoshi a Kazaure, Babura da Mashi, sannan kuma a samar da muhimman takardu daga Hukumar TCN. Wani muhimmin kudiri da ke kunshe cikin kunshin yarjejeniyar ta ‘MoU’ an tsara samar da tallafi wajen gudanar da kyakkyawar alaka da al’ummar da ke wuraren da za a aiwatar da wannan aiki har tsawon lokacin kamala aikin.

Source; a yau