Matsalar Tsaro: Shugaba Buhari Duniya Tana Kallonka
Laraba, Fabrairu 12, 2020
Matsalar Tsaro: Shugaba Buhari Duniya Tana Kallonka

 Bari in fara da tuna baya, wanda masu iya magana ke cewa shi ne roko. Maganar harkar tsaro na daya daga cikin abubuwan da suke a bayyanai a wannan kasar, saboda haka yanzu kowa yasan halin da ake ciki game da wannan matsala. Shugaban kasa da sauran ‘yan siyasa, suna da tabbacin rashin kawo karshen wannan matsala barazana ne ga dorewar mulkinsu, amma kullin magana da ake yi shi ne, muna iyakar kokarinmu wajan ganin an samar da tsaro. Abu na biyu shine, jama’a na ganin wannan kokarin da hukumomin suke cewa suna yi?, saboda dai yanzu abin ya bude kowa na gani, babu wani mutun a Najeriya da yake musun cewa akwai zaman lafiya musamman yankin arewa. Saboda haka, abun ba a boye yake ba, sai dai abin tambaya shi ne, kokarin da gwamnatoci suke ce suna yi, kamar ya dan boyewa jama’a saboda yadda abubuwa kullun sai komawa baya suke kuma wai ace ana samun tsaro ko kuma an samu tsaro, akwai rainin hankali a wannan harka. Sannan mutanen boye masu shan jinin ‘yan Najeriya kullun abinda suke fada shi ne, an gaji wannan matsala ne daga tsohuwar gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan saboda haka ba su suka kawo ta ba. Idan ma din haka ne, wannan ba dalili bane da za a rika fakewa da shi idan har an kasa yin abinda ya kamata, saboda haka ya zama wajibi su canza tunani da wasu dibaru tunda an gano basa san sauka daga kan mulki. Wannan hali da muke cikin tun ana bada uzuri akan shugaban kasa Muhammadu Buhari har ta kai ana ba shi shawara game da wannan hali da ke sanadiyar raba jama’a da rayukansu da dukokiyoyinsu kullun ba tare da ganin wani canji ba. Mutane a yankin arewa masu gabas sun yi kuka har sun gaji akan neman agaji daga bangaran shugaban kasa akan matsalar tsaro, yanzu wasu da yawa daga cikin tuni suka fidda rai da samun dawwamanman zaman lafiya a wannan yanki na su. Sai dai kuma wani abu da za a iya kwatantawa da rashin sanin kimar dan adam su ne kalaman shugaban Buhari wanda ya ce yana mamakin da har yanzu ba a gama da masu tada kayar baya ba a yankin arewa masu Gabas wato yankin Maiduguri da sauran wurare. Abinda mafiyawan ‘yan Najeriya suke cewa shi ne wai shin ina shugaban kasa yake zaune ne, shin a wannan Najeriya yake ko a wata daban, domin kullun rana ta Allah jarida sa sauran kafafen yada labarai sai sun dauko wadannan labarai, saboda haka duniya tana sane da abinda ke faruwa ba wai ‘yan kasa ba wadanda abin ya shafa kai tsaye. Saboda haka ‘yan kasa sun fara tunanin cewa yanzu dai sun fara gano wadanda suke mulkin wannan kasa ba wai wanda suka zaba ba kuma suka sani ba, saboda haka akwai takaici matuka da har irin wannan magana tana fitowa daga bakin wanda yasan wannan matsala tun kafin hawansa mulki Bayan haka wadanda aka dorawa alhakin tafiyar da sha’anin tsaro bayan wai ace sun kasa ba, har ta kai ga cewa wadannan mutane ba abinda yarda bane, ba irin mutanen da ya kamata ace an baiwa amanar ‘yan Najeriya ba ne, kusan mutun miliyan 200 a hannunsu haba jama’a!. Kullin ana jin irin makudan kudadan da ake dankara masu da sunan samar da tsaro a kasa musamman yankin arewa, amma labarin dai daya ne, an kashe mutane kaza, an sace mutane kaza, an yi fashi da makami a gari kaza. Shin wai don Allah ina wadannan kudade suke makalewa, me ake yi da su,? Babau wannan amsar sai dai ka ji an ce ‘yan jarida na kara ruruta wutar abu, bayan kuma wai bai kai haka ba. Sai dai su ma din masu wannan zargin, har yanzu babu karin haske game da irin kudadan da ake mika masu domin baiwa jami’an tsaron da ake turawa wajan wanzar da zaman lafiya a wuraran da ake fama da wannan matsala. Tun ‘yan Najeriya na kallon matsalar tsaro a matsayin wata annoba da Allah ya kawowa har sun fara sake tunani game da haka, yanzu ana iya cewa kallon ya koma sama, saboda akwai lauje cikin nadi game da wannan bakar harka. Yanzu kowa na ganin wannan harka ta tsaro ta koma wani sabon kasuwancin a tsakanin manyan jami’an tsaron Najeriya da wasu kuma wadanda suke boye a bayansu suna shan jini al’umma da suna ba su kariya a nan duniya. Duk lokacin da ‘yan kasa suka koka game da abubuwan da ke faruwa ba zaka taba jin wadannan mutane sun goyi bayan su ba, ba zaka taba jin sun yi magana a dauki wani mataki ba, ba zaka taba jin sun yi wa al’umma jaje ba, suna kallon ana kashe jama’a amma ko a kwalar rigarsu. Sannan sun hana kowa yin magana sai dai wanda ya sha ta dubu ko ya shirya yin hakuri da mukami ko rawani ko aikinsa ko kuma ya shirya zaman cikin matsala, su kadai suka rage masu tankawa akan wannan al’amari domin kuwa abin ya zama abinda zama, sai dai addu’a Da kasashen Yarabawa suka hango wannan matsala tafe akan su, idan an gama nakasa arewa baki daya, sun fara shirin ko ta kwana, inda suka kirkiro ‘yan bangansu domin su ba su kariya saboda dai wannan gwamnatin ta Najeriya tuni ta kasa yin haka kuma duniya tana kallo. Kirkira ‘yan “Operation Amotaken” alama ce ta cewa babu sauran tsaro a wannan gwamnati ta shugaba Muhammadu Buhari sauran kadai a ayyanata a matsayin ba kasa ba, saboda tsaro na daya daga cikin abubuwan da suke tabbatar da wanzuwar kasa, to Najeriya ta rasa hakan. Mutane masu kima da daraja irin su mai alfarma sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad na III tun suna alkunya game da wannan sha’ani domin kadda ace sun juyawa na su baya, a karshe dai sun fito sun yi magana sun ja daga suna jiran abinda zai biyo baya. Sarkin Musulmi Abubakar Na III ya bayyana cewa yanzu ba su da ikon yin magana akan sha’anin tsaron kasar nan duk da cewa shima tsohon jami’in tsaro ne, amma saboda wasu dalillai idan ya cigaba da magana, da ni da kai da ku mun san abinda zai biyo bayan maganar da zai rika yi. Sannan idan ya kame bakinsa ya yi shiru duniya na kallonsa yaki yin abinda ya kamata a matsayinsa na shugaba mai ta cewa, saboda haka idan har ya yi magana akan abinda ya hango ya sauke nauyin da ke kansa, abinda ya rage shine wadanda alhakin samar da tsaro ya hau kai ya rage ruwansu ko dai su yi, ko su bari kamar yadda ake gani yanzu. Bayan ga shi akwai dai dai kun mutane da suma suka sha ta dubu suka fara magana domin suna kallon za a karar da arewa a karkashin mulkin dan arewa wanda aka yi wa zaton yana san arewa amma ya yi watsi da ‘yan arewa a lokacin mulkinsa. Idan Allah mai kowa mai komi ya kai mu sati mai zuwa, za kawo maganganun wasu manyan mutane da suka hango bala’in da ke tafe wannan kasa saboda rashin samar da tsaro a karkashin kulawar Buhari, da kuma yadda yin magana ya zama wani baban bala’I a wajan mahukuntan kasar nan. Mu hadu a sati mai zuwa Insha’Allahu.

Source: a yau