Rahoton da Hukumar yada labarai ta fitar ya nuna cewa: an samu manyan nasarori ta fuskar siyasa da tattalin arziki a karkashin shugabancin Misra na kungiyar tarayyar Afirka.
Laraba, Fabrairu 12, 2020
Rahoton da Hukumar yada labarai ta fitar ya nuna cewa: an samu manyan nasarori ta fuskar siyasa da tattalin arziki a karkashin shugabancin Misra na kungiyar tarayyar Afirka.


A manyan taruka na duniya guda 10 da aka yi a Nahiyoyi 4 shugaba El-sisi ya yi magana akan hakkokin Afirka na zaman lafiya da ci gaba, Misra ta yi alkawari kuma ta cika, ta kuma nuna ta cancanta da yardar da sauran kasashen Afirka suka yi mata. A ranar tara ga watan Febrairu 2020 shugaba Abdul Fattah El-sisi ya cika shekara daya da amsar shugabancin kungiyar tarayyar Afirka a taron kolin Adis Ababa a cikin watan Febrairu na 2019.

Misra a karkashin shugabancin ta na kungiyar tarayyar Afirka ta dauki wannan nauyi a matsayin yarda da shugabannin Afirka suka nuna mata, haka ta dauki shugabancin a matsayin nauyi ne akanta da ya zama tilas ta sauke wannan nauyi na Afirka da al'ummar ta.

A tsawon wannan shekara shugabancin na Misra ya yi kai-komo a wurare da dama domin masalahar al'ummar Afirka, kuma domin karfafa taimakekeniya tsakanin Misra da kasashen Afirka, da kuma tsakanin al'ummar Afirka da junansu.

Daidai da rahoton da hukumar yada labarai ta fitar, shugaba Abdul Fattah El-sisi ya kai rangadi a Nahiyoyin duniya domin ba wa masalahohin Afirka kariya, da kuma daga muryarta na hakkin zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ci gaba.

Bayan manyan tarukan Afirka shugaba Abdul Fattah El-sisi ya halarci taron kolin zaman lafiya na Munich a Jamus domin zaman lafiyar Afirka, sai kuma ya halarci taron kolin Afirka da Turai wanda aka yi a Nasma, sai taron China da Afirka a Bakin, da kuma taron kolin Japan da Afirka (TICAD) wanda aka yi a Tokyo, da taron kolin kasashe bakwai a Birnin Faris, da taron kolin manyan kasashe ashirin masu karfin tattalin arziki a duniya wanda aka yi a Osaka na Japan, da kuma taron babban zauren majalisar dinkin duniya, sai kuma taron koli na taimakekeniya tsakanin kasashe ashirin masu karfin tattalin arziki a duniya da Afirka wanda aka yi a Jamus, sai taron kolin Afirka da Rasha wanda aka yi a Sochi, sai taron kolin zuba jari tsakanin Afirka da Burtaniya wanda aka yi a Janairu 2020 a Birnin London.

A cikin dukkanin wadannan tarurrukan na Duniya da wasunsu shugaba Abdul Fattah El-sisi ya yi jawabi akan batutuwan Afirka da kuma hakkokin ta da masalahohin ta.

A fadin Afirka kuma shugaba El-sisi ya halarci taron kasuwancin bai daya na Afirka wanda shi ne abu mafi girma domin taimakekeniyar tattalin arziki tsakanin kasashen Afirka. Mafi girman wadannan tarurrukan koli su ne:
-Taron kolin zaman lafiya na Munich. a 15 ga watan Febrairu 2019.
- taron kolin da aka yi a Bakin a 24 ga watan Afirilu 2019.
- taron kolin kasashe ashirin masu karfin tattalin arziki a duniya a Japan a 37/6/2019.
- taron koli karo na 45 na manyan kasashe bakwai G7 wanda garin Biarritz na kasar Faransa ya karbi bakuncinsa a 25 da 26 na watan Agusta 2019.
- taron koli karo na bakwai ( TICAD7 ) a 28 zuwa 30 ga watan Agusta 2019.
- taron koli na Rasha da Afirka a 23-24 ga watan Oktoba 2019.
- taron kolin Jamus da Afirka 19 ga watan Nuwamba 2019.