Shugaban Hukumar NEMA Ya Nemi A Kara Daukar Matakan Kare Ambaliyar Ruwa A Nijeriya
Litinin, 21 Satumba, 2020
Shugaban Hukumar NEMA Ya Nemi A Kara Daukar Matakan Kare Ambaliyar Ruwa A Nijeriya

A ranar laraba ne shugaban hukumar NEMA, ABM Muhammadu Mohammed, ya bukaci gwamnatocin jihohi 36 da yankin birnin tarayyar kasar nan Abuja su samar da shiri na musamman don tunkarar barnar da ambaliyar ruwa ka iya haifarwa musamman ganin damuna na kara kai wa matakin kololuwa a halin yanzu.

ABM Mohammed ya yi wannan kiran ne a yayin ziyarasa ga Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu a garin Birnin Kebbi.

Ya ce kananan hukumomi 102 a jihohi 28 na kasar nan tare da yankin babbar birnin tarayyar kasar na Abuja sun fada cikin rukunin da ka iya fuskantar matsananciyar ambaliyar ruwa a wannan damunan.

“Sauran kuma kananan hukumomi 397 barazanan da suke fuskanta ba shi da tsananin gaske.”

Shugaban wanda Darakta a ma’aikatar, James Akujobi, ya wakilta, ya ce, yawan aukuwar ambaliyar ruwa na barazana ga harkokin noma a kasar nan.

“Mun zo jihar Kebbi ne don mu fadakar da gwamnati da al’umma akan yiwuwar ambaliyar ruwa a damina 2020, kuma 

 jihar na daga cikin jihohin da ake gaggarumin ayyukan noma, amma wannan ambaliyar yana yi wa wannan harkar na noma barazana.

A jawabinsa, Gwamna Bagudu, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Babale Umar-Yauri, ya bukaci gwmanatin tarayya ta samar da issashen tallafi ga manonma don fuskantar noman rani, don ta haka ne za a rage karancin abinci da ka iya faruwa a kasar nan.

Ya kuma jaddada shirin gwamnati na tallafa wa manoman da ambaliyar ta shafa.

a yau