Buhari Zai Gabatar Wa Majalisa Kasafin 2021
Alhamis, Oktoba 01, 2020
Buhari Zai Gabatar Wa Majalisa Kasafin 2021

A mako mai zuwa ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai gabatar wa da majalisar hadin gwiwa ta majalisun kasa da kasafin kudin shekarar 2021.

Shugaban majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ne ya bayyana hakan a cikin jawabinsa na bude zaman majalisar ta Dattawa a bayan komowar majalisar daga hutun da ta tafi a Abuja.

Lawan ya ce majalisar ta Dattawa za ta bai wa Ma’aikatun gwamnati da sauran hukumomin gwamnati wa’adin wata guda domin su zo majalisar su kare kasafin kudin na su.

“Don haka muna shawartar dukkanin hukumomin gwamnati da su tabbatar da sun bijiro da kawukansu domin kare kasafin kudin na su, su kuma zo ne da dukkanin takardun bayanan da za a nema daga gare su domin kare kasafin kudin na su.

Lawan ya ce akwai bukatar a rika sake yin nazarin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima a kai, akai, domin inganta yanayin tafiyar da gwamnati da kuma tabbatar da tsaftar tsarin da ake tafiya a kansa.

Ya ce aikinn da ake yin a sake duba dokar zabe a tsarin mulkin kasar nan za a hanzarta shi a majalisar ta Dattawa.

Ya kara da cewa: ‘ Tuni ma har kwamitin sake nazarin tsarin mulkin na majalisar ta Dattawa ya gayyaci shawarwari daga ‘yan kasa da sauran kungiyoyi.

“Za mu tabbatar da mun yi dukkanin gyare-gyaren da za su inganta harkar gudanar da zabe a bisa tafarkin gaskiya da adalci a zabukan kasar nan.

“Yanayin tsaro a kasar nan bas hi ne abin da muke fatan sa ba. muna son samar da yanayin tsaro ne a kasar nan da zai tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

Ya dage a kan cewa a daidai lokacin da kasar nan ke fama da matsalolin tsaro kala-kala, majalisun kasa za su cigaba da lalubo matakan da za a inganta harkar tsaro din.

“Sam babu wani mahimmin aikin gwamnati za ta yi wanda yake sama da samar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasarta,” cewar Lawan.

Ya kuma yaba wa kwamitocin majalisar ta Dattawa a bisa ayyukan da suka aiwatar a lokacin da majalisar take a cikin hutun ta.

Ya kebance kwamitin kasha-kashen kudi kudi da tsare-tsare a kan kasafin kudin tsakiyar shekara na shekarar 2020-2022 da Ambato da kuma yaba wa a kan aikin nasu, ya na mai cewa, “Wannan kwamitin ya gana da sama da hukumomi 300 a kan batun a kan kudaden da gwamnati ta fitar da kuma maido wa da gwamnatin rarar wasu kudaden.

“Mun fuskanci matsalar gibin sama da dalar Amurka biliyan 14 na kudaden da muka tsammaci Tarawa gwamnati, sannan kuma ga matsalar da muka samu a bisa yawan dogaronmu a kan danyan man fetur.

“Bai zama wuce gona da iri ba in mun yi Magana a kan karfafa sauran sassan tattalin arziki masu mahimmanci kamar sashen noma, albarkatun kasa da karafa gami da kere-kere, duk domin samar da karin hanyoyin tattalin arzikinmu.

“Mu na da bukatar yin aiki tare da dukkanin masu ruwa da tsaki domin tabbatar da tattalin arzikinmu bai sake shiga cikin wata komadar ba, mu daidaita tattalin arzikin, mu samar da karin ayyukan yi ta hanyar tattalin arzikin.

a yau