Labaran Yau 16- 1-2019
Laraba, 16 Janairu, 2019
Labaran Yau 16- 1-2019

DW
         Theresa May za ta fuskanci kuri'ar rashin amanna.

Aminiya
         Sabon shugaban ‘yan sanda ka yi shirin magance magudin zabe -PDP.
         Petr Cech zai yi ritaya daga kwallon kafa.
         Shugaba Buhari ya nada sabon Sufeto Janar na ’yan sanda

voa
         Jami'in Hukumar Alhazai Ya Mayar Da Rarar Kudin Da Aka Ba Shi.
         An Rusa Daruruwan Gine-Gine A Birnin AccraCi gaba: Shugaban kasa Buhari ya kaddamar da Rejistar sabon tsarin fasfo na yanar gizo.

rfi muryar duniya
        Shugaban Gabon ya koma gida.
        Nijar da Italiya sun sha alwashin fadada yaki da kwararar baki Turai.

 

Beljiyam: Gidan adana kayan tarihin Afirka

Daga cikin rubuce-rubuce na neman gafara da gidan kayan tarihin ya yi, har da sunayensu da aka rubuta kan bango da kuma sunayen 'yan Beljiyam fiye da 1500 da suka mutu lokacin mulkin mallakar. Koekie Claessens ta ce matakin da gidan tarihin ya dauka na duba wancan lokacin, abu ne mai sosa rai. Sai dai akwai abubuwa da dama game da gidan tarihin wanda kafin a yi masa gyara wasu ke kiransa "gidan tarihin mulkin mallaka na karshe a duniya" musamman saboda rashin kaucewa daga ainihin manufar Sarki Leoprad na biyu dangane da galabar da ya samu a Kwango. An dai kiyasta ya halaka mutane kimanin miliyan 10. Daraktan gidan tarihin Guido Gryseel ya yi bayanin yadda 'yan Beljiyamke jan kafa wajen amsa cewa mulkin da Sarki Leopold ya yi a Kwango, ya kassara kasar domin arzurta kasarsa wato Beljiyam. Gryseel ya ce ra'ayinsu a yanzu shi ne mulkin mallaka a matsayin tsari na shugabanci babban kuskure ne. Ya ce za a samu ra'ayi mabambanta daga maziyarta.

Source: www.dw.com