Labaran Ranar 3/2/2022
Alhamis, 3 Faburairu, 2022
Labaran Ranar 3/2/2022
Labaran Ranar 3/2/2022

AMINIYA:

 • ’Yan Ci-Rani 12 Sun Daskare A Dusar Kankara A Kokarinsu Na Shiga Turai.
 • ’Yan Bindiga Sun Kashe Dagaci Da Wasu Mutum 5 A Katsina.
 • Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Yunkurin Juyin Mulki A Guinea-Bissau.

RFI:

 • Shugaban Rasha da Firaministan Birtaniya sun tattauna rikicin Ukraine ta waya.
 • OPEC ta amince da shirin kara farashin man fetur.
 • Ana Biciken Musabbabin Yunkurin Juyin Mulkin Guinea da Mutuwar Mutane 11.
 • Gwamnatin Rasha Da Jamus Na Neman Sa Zare Saboda Rufe Tashar Sadarwa.

Leadership Hausa:

 • Ta’addancin ‘Yan Bindiga: Sarkin Musulmi Ya Nemi Aiwatar Da Ingantattun Manufofin Tsaro.
 • Majalisa Ta Yi Kiran Gaggauta Ceto Mutum 38 Da Aka Sace A Katsina.
 • Dukkanin Tawagogi 91 Sun Kammala Rajista Gabanin Bude Gasar Olympic Ta Birnin Beijing.
 • Majalisar Wakilai Ta Nemi A Yi Bincike Kan Kisan Hanifa.
 • Sojojin Sama Sun Tarwatsa Mabuyar ‘Yan Bindiga A Jihar Katsina.

PREMIUM TIMES HAUSA:

 • YUNƘURIN JUYIN MULKI: Shugaban Guinea-Bissau ya ce fanɗararrun maharan ba su yi nasara ba, kuma an damƙe su.
 • Majalisa ta umarci Hukumar Kwastan ta biya diyyar Naira miliyan 360 ga iyalan mutum 18 da ta bindige.
 • Majalisar Tarayya ta fara shirin halasta wa matuƙa mota ‘yan sama da shekaru 21 yin amfani da ‘Bluetooth’.
 • Gwamnatin 2023 za ta gaji ingantacciyar dimokraɗiyya da ƙarfafan hukumomin tsaro – Buhari

DW:

 • Guinea Bisau: Juyin mulkin soja ya gagara.
 • Ministar tsaron Faransa na ziyarar a Nijar.
 • Makomar kafafen yada labarai a Najeriya.
 • Hodar Iblis ta yi ajalin mutane 20 a Ajantina.

VOA

 • Wa'adin Korar 'Yan Rwandar Da Nijer Ta Ba Mafaka Na Gab Da Shudewa.
 • An Maida Shari’ar Wadanda Suka Kashe Hanifa Gaban Babbar Kotun Jihar Kano.
 • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Maida Martani Kan Dakatar Da Shirin Idon Mikiya Na Vision FM.
 • Senegal Ta Kai Zagayen Wasan Karshe A Gasar AFCON.
 • Shugaba Buhari Ya Yi Alkawarin Mutunta Yarjejeniyar Da Aka Kulla Da ASUU.
 • Wata Kungiya Ta Baiwa Makarantu Horo Kan Dabarun Kare Kai A Lokacin Harin 'Yan bindiga.

Legit:

 • Yanzu-Yanzu: An tsaurara tsaro a sakateriyar APC yayin da ake rantsar da shugabannin jihohi.
 • Tubabbun 'yan Boko Haram na taimakawa wurin yaki da ta'addanci, Zulum.