Jumhuriyyar Dimukradiyya ta al’ummar Algeria
Asabar, Maris 09, 2019
Jumhuriyyar Dimukradiyya ta al’ummar Algeria

Kasa ce ta farko a fadin kasa a nahiyar Afrika, ita ce kuma ta goma sha daya a duniya.. Sunan babban birninta “Algeria”, tana gabar baharul mutawassit ne ta bangaren Arewa.

Wuri

Kasar Algeria tana tsakiyar Arewa maso yammacin nahiyar Afrika tsakanin layuka biyu na tsaye 12 ta bangaren gabas, tsayi  9 kuma a bangaren yamma, da kuma tsakanin layikan kwance 19 ta bangaren Arewa, da 37, iyakokinta na kasa kuwa ya kai kimanin kili-mita murabba’i 7543, ta ruwa kuma a gabar baharul mutawassit ya kai kimanin 1200, tana kuma ta iyakoki kimanin kili mita murabba’i 6343 tare da kasashen da take makwabtaka da su, wadanda suka hada da: Tunisia da Libya da Nijar da Mali da Muritaniya da Morocco.

Girman Kasar Algeria

Girman kasar Algeria ya kai kimanin kilo mita murabba’i 2.381741.

Yanayin Kasar

Yanayin kasar yana kasancewa tsaka-tsaki lura da bahrul mutawassit a bangaren Arewa ta inda darajar zafi take kai kawo tsakanin daraja 12 cikin dari, da sanyi da kuma da darajar sanyi lokacin zafi, haka kuma da darajar sanyi 100% kamar yadda yanayin yake kasancewa mai sahara a kudu ta inda darajar zafi take yin kasa ta kuma ke hawa da rana tare da bazara. Darajar zafi tana kai kawo tsakanin 10 da sanyi da kuma iska wadda take jawo wannan tudun.

Ranar kasar:

19 ga watan Nuwamba, 1954.

Ranar Samun 'Yanci

5 ga watan Yuli, 1962.

Kudin Kasar

Dinare wanda yake daidai da Sintim 100, dala daya kuma ta yi daidai da dinare 118.

Adadin Mutane

Adadin Mutane Kasar Algeria a watan Janairu 2016 ya kai miliyan 40.4.

Harshen Kasar

Harshen Larabci shi ne yare na biyu tare da wasu harsuna daban kamar Amazigiyya da Dawarkiyya sai dai cewa wadannan yaruka ba su yadu sosai ba.

Addini

Addinin Musulunci shi ne addinin kasar wanda Musulmai a kasar sun kai kashi 99% akwai wasu mutane da suke da addinin Kiristanci wanda ba su wuce  0.5% kamar yadda akwai Yahudawa a kasar.

Tattalin arziki

Kasar Algeria tana da arzikin man fetur sai dai ba shi da yawa idan aka gwada da iskar gas da take da shi, inda take fitar da kimanin ganga biliyan 12, a karnin da ya gabata ne kuma kasar ta zamo fitacciya wajen tace man fetur, da sana’anta kayan abinci, da ma’adinai da sauransu.