Jamhuriyyar Angola
Asabar, Maris 16, 2019
Jamhuriyyar Angola

Kasar jamhuriyyar Angola kasa ce da yankin kuduncin nahiyar Afrika.

Luwanda ne babban birninta, kuma shi ne gari mafi girma a cikin kasar, harshen kasar a gwamnatance shi ne harshen Portugal. Kudin kasar shi ne Kwanza (AOA).

Adadin mutanen kasar ya kai kimanin mutum miliyan 26, Su ne bikin ranar Angola ne a duk ranar 11 ga watan Nuwamba.

Kasar Angola tana iyaka da kasar Namibia ta bangaren kudu da kuma kasar Zambia ta bangaren gabas, da kuma kasar Kongo Dimokradiyya ta bangaren arewa maso gabas, da kuma kasar Kongo ta bangaren Arewa da Kogin Atlanta ta bangaren yamma.

Kasar Angola tana da girma sosai wanda ya kai 1.246.700 Kilomita murab'i tana gurin noma da jeji da kuma kogi kamar yadda kasar take da arziki da yawa kamar su gwal da man fetur da karfe da uraniyum da sauransu.

Kasar tana da zaman lafiya da kwanciyar hankali na siyasa, kuma tana da tattalin arziki mai karfi.

Hukumar kasar Angola ta jajerice a wadannan shekaru wajen samar da sabon tsarin bunkasa arziki da haraji wanda zai kara wa kasar cigaba, da jawo masu zuba hannun jari.

Kasar Angola ita ce kasa ta bakwai wajen fadi a nahiyar Afrika, it ace kuma kasar da tafi kowace kasa a Afrika fitar da danyen mai, tana mallakar kashi 12% na arziki ruwan a nahiyar Afrika, kamar yadda take a matsayin kasa ta biyar kasashen duniya a fagen samar da Gwal..

A lokacin da tattalin arzikinta ya yi kasa, sanadiyyar faduwar man fetur shekara ta 2014, ya zama tilas kasar ta sanya tsari domin a rage matsalolin da suke faruwa a kasar ta hanyar samun wuraren bunkasa arziki daban-daban da kuma ware kudaden yau da gobe daga kudin man fetur.

A shekara ta 2015 kasar ta kawo sabon tsari na bunkasa arziki domin kara tattalin  arzikin kasar.

Dokar bukasa arziki sabuwa 10-18 a kasuwanni daban daban kamar yadda yake  a haka:

  • Ilimin da kuma koyawa mutane sana'a da bincike.
  • Noma da sana'anta abubuwa.
  • Hidimtawa mutane da ba su kula ta lafiya.
  • Saka kaya da tufafi da takalmi.
  • Kabar bakunsa.
  • Gini da sadarwa.
  • Samar da damammaki.