Jumhuriyyar Burundi
Laraba, Afrilu 10, 2019
Jumhuriyyar Burundi

Suna: Jumhuriyyar Burundi

Tsarin hukunci: Jumhuriyya.

Samun 'yancin kai: 1 ga Yuli, a hannun kasar Beljika.

Babban Birni: Bujumbodo.

Manya - manyan Birane: Dusimbra- Njuri – Kyinza- muaro.

Inda take: Kasar Burundi tana nan a bakin kogin gabas na karamin kogin Tanganefa, ta bangaren Arewa kuma ta yi iyaka da Dimokradiyyar Kongo, ta bangaren gabas da kudu kuma kasar tana da iya da kasar Tanzaniya.

Yanayin Shekara: Yanayin kasar Burundi yana da daidaito na sanyi, sai dai cewa tudun da take da shi ya sa an sami daidaito a zafin kasar.

Mafi tsananin bangarorinta yana da zafi daga yamma; saboda akwai ramuka da kuma ruwan sama wanda ba shi da yawa idan aka hada da inda yake da  tudu na kasar ta Burundi: kamar yadda ta shahara da dadidaitaccen yanayi ta inda darajar zafi ta kai 28 kamar yadda ruwan sama yake fadowa da sauka a kasar tsawon wata bakwai.

Girmanta: 27.830 kilomita murabba’i

Adadin Mutane: alkaluma sun nuna cewa kasar tana da yawan mutane kimanin (12.328.587) a kididdigar shekarar 2018.

Kabilu: Hutu, Tutsi

Harshe: Faransanci shi ne harshen da ake amfani da shi a kasar hada da sauran harsunan cikin gida kamar su harshen Banto da Sawahili.

Kudi: Frank.

Tuta: An tabbatar da tutar kasar Burundi 28 ga watan Maris 1967. Koriyar kala tana nuna Buri fara kuma tana nuni da tsafta, ja kuma yana nuni da jajircewa da dagewa domin samun 'yanci. A tsakiyar tuta akwai wani zagaye wanda yake dauke da taurari guda uku wanda suke nuni zuwa manya manyan kabilun kasar gudu uku wanda su ne Hutu du Tutsi da Tuwa, kamar yadda suke nuna tambarin hadin-kai na kasar tare da aiki da cigaba.

Takaitaccen tarihi:

Kasar ta sami 'yancin kanta 1 ga Yuli 1962, Mko biro shi ne wanda ya karbi shugabancin kasar kamar yadda shi ne shugaban kasa na farko a kasar sa'annan bayansa aka sami shugabannni daban daban. Shugaban kasar na yanzu shi ne Birnikoziza wanda ya karbi mulki 26 ga Agustus 2005

Tsarin Dokoki:

An dauko tsarin kasar daga dokokin kasa Belgium da kasar Jamus kasa ba ta karbi mulkin dole ba na kotun laifuka ta duniya.

Kundin tsarin mulki an kafa shi a 28 Fabrairu shekara ta 2005 bayan an nemi shawarar 'yan kasar.

Manya manyan Jamiyyun Siyasa:

Jamiyyar Dimokradiyya ta Burundi majilisar kasa don kare Dimokradiyya – Hadin kai don samun cigaba.

Masu zartarwa: shugaban kasa da shugaban hukuma da majalisar ministoci.