KASAR ERITREA
Litinin, Maris 04, 2019
KASAR ERITREA

Wuri

Kasar Eritrea tana Nahiyar Afrika ta wajen mashigar kudu ta Bahrul Ahmar, kuma a kusa da mashigar Mundub, wadda take da matukar muhimmanci ta inda take a tsakanin kasar Ethiopia da Jiboti da kasar Sudan. Daga gabas Bahrul Ahmar yana iyaka da ita, ta arewa kuma kasar Sudan da iyakar da ta kai kimanin kilomita 912. Ta kudu kuma tana da iyaka kasar Jiboti ta inda iyakar ta kasar Jiboti ta kai kimanin kilo mita 109. Daga yamma kuma tana iyaka da kasar Ethiopia wadda ita ce iyakokin da take kusa da ta kai kimanin kilo mita 1021, tana tafiya ta wani yanki tare da kogin State Tekezy daga cikin kogunan da suke taimakawa Kogin Nilu, wanda tsayinshi ya kai kilo mita 120. Iyakar kasar ta kasar Ethiopia ta kai kimanin kilo mita 1626, iyakarta kuma ta kasa ta kai kimanin kilo mita 2234.

Adadin Mutane

Adadin mutanen kasar Eritrea  ya kai kimanin miliyan 6.

Rabe raben kasar

Kasar Eritrea an kasa ta zuwa Zobatat da Debubawi da Debub (south) da Anseba da Gash da K'eyih Bahri da Semenawi da Ma'akel da Barka da Keyih Bahri.

Yanayin Kasa

Yanayin kasar Eritrea yana bambanta daidai da babban birnin kasar wato Asmara ta inda yanayin kasar yake da daidaituwa a yawancin lokutan shekara, duk da cewa akwai sanyi kadan a wasu lokutan amma a wuraren da suke kwari kamarsu Masu'i – Asabi- Kiran. To yanayin yana da tsanin zafi mai tattare da sanyi, a lokacin zafi duk da cewa yanayin ya karkata zuwa sanyi, yana kai kawo tsakanin mita 1800 da 2400 a saman kogi.

Kundin Tsarin Milki

Yanzu, akwai gyare-gyaren sabon kundin tsarin milki na kasa, inda  wannan gyare- gyare  ya fara a shekara ta 2014.

Tsarin mulki

Jamhuriyya ce da take karkashin shugabancin kasa.