Jumhuriyyar Tarayyar Ethiopia ta Dimokradiyya
Asabar, Maris 23, 2019
Jumhuriyyar Tarayyar Ethiopia ta Dimokradiyya

Kasar ta Ethiopia tana daya daga cikin tsofaffin kasashen a nahiyar ta Afrika, wadda ba a yi mata mulkin mallaka ba, sai na tsawon shekaru shida kacal daga 1935 - 1941 a zamanin Mosolini. Wannan kasa tana da tarihi na al’adu da ma masarauta mai dadadden tarihi tun karnin miladiyya na biyu, wato masarautar “Aksum”.

Mafi shaharar abin da ya faru a zamanin Hailasalasi shi ne: sanarwar da majalisan dinkin duniya ta yi a shekara ta 1952 cewa Eritria da Etiopia kasa ce daya ta tarayya, sa’ilin da shi kuma Hailasalasi a shekarar 1962 ya sanar da cewa yankin Ethiopia kasa ce mai zaman kanta.

A wannan shekara 1963 an yi babban taro na farko na kungiyar hadin kan Afrika, ya kuma cigaba har zuwa 1974, lokacin da sojojin suka kifar da gwamnatinsa, Manjesto kuma ya kwafe makwafinsa wajen shugabantar kasar.

Wuri

Kasar tana nan a Arewa maso dabas na nahiyar Afrika, yankin da aka fi sani da kahon Afrika, kasar Eritia ce ta yi iyaka da ita ta bangaren Arewa, ta bangaren Arewa maso gabas kuma tana da iyaka ne da kasar Jibuti, sa’ilin da kasar Kenya take a kudu maso yamma, daga gabas da kudu maso gabas kuma tana da iyaka da kasar Somalia, ta Yamma, da yamma maso kudu tana iyaka da kasar Sudan.

Girman Kasar: ya kai kilomita murabba’i (1.133.382), wato kimanin mil (437.794), kasar Ethiopia ta kunshi kan dutsen Ethiopia, da kuma wani budadden fili, da dutesn Somalia, da kuma dutsen Ugadin, dutsen Ethiopia shi ne kusan rabin fadin kasar.

Ranar Bikin Kasar:

Ranar 28 ga Mayu, 1990 ne Mungosto Maryaam ya bar kasar.

Adadin Mutanen Kasar:

Alkalumman mutane a kasar Ethiopia ya kai mutum miliyan dari da bakwai da digo biyar (107.5) a shekara ta 2017, da haka ita ce kasa ta biyu da ta fi kowace  girma a Afrika ta bangaren yawan mutane, bayan kasar Najeriya.

Harsuna kasar sun hada da: harshen Amharic, da harshen Tigereniyya, da harshen Oromo, ga kuma Turanci da sauran harsuna kamar Larabci da Somalia an ci.

Addini:

Akwai Kirstoci Arsozuks 43.9%, Burutstant 18.8%, Musulmai 33.9% da sauran addinai.

Kudin Kasar:

 Kudinsu shi ne Bar wanda ya yi daida da Dola 27 a 2018.

Jam’iyyun Siyasa:

Jam’iyyar Jabha ta kasa EPRDF.

Jam’iyyar Amhara.

Jam’iyyar Oromo.

 Tattalin Arziki:

Kere - kere shi ne ya fi yawa a kasar, ya kuma kai 22.8% na tattalin arzikin kasar suna sana’anta abinci da kayan maye da kayan da takalma da siminti.