Jumhuriyya Gambiya
Litinin, Janairu 14, 2019
Jumhuriyya Gambiya

Kasar Gambiya ita ce kasar da tafi kankanta a cikin kasashen Afrika wajen fadi, kuma tana daya daga kasashen da suke yammacin Afrika. Kalmar "Gambiya" sunan kogin da ya keta kasar ne. Tutar wannan kasa ta hada da layika guda uku a kwance. Wadannan layika suna dauke da launuka: ja da shudi da kuma kore. Wadannan layika guda uku, akwai layika farare guda biyu da suka raba su. Launin ja da yake sama yana nuni da rana da shimfidaddiyar sabana a tsakiyar wannan tuta akwai shudin launi wanda yake nuni da kogin Gambiya wanda shi ne kogin da ya raba kasar zuwa gida biyu. Launin ja kuma wanda yake kasar tutar yana nuni zuwa yankin da daji ya mamaye shi a kasar, fararen launika kuma da suke sama kuma suna nuni ne zuwa aminci, an fara amfani da wannan tuta 18 ga watan Fabrairu shekara ta 1965. A wannan rana ce kasar Gambiya ta zama kasa mai 'yanci bayan ta kubuta daga milkin masarautar Ingila.

Wurin da kasar Gambiya take da fadinta

Kasar Gambiya tana nan a kwarin hadadden kogi, girmanta ya kai kimanin kilomita 111300, a arewa da gabar akwai kasar Senegal wadda take iyaka da ita daga gabas kuma akwai kogin Atlas wanda shi ke iyaka da ita. Sannan kogin Gambiya yana keta wannan kasa don ya kwarara a kogin Atlas.

Babban Birni:

Babban birnin kasar Gambiya shi ne garin Banjol, kasar ta kasu zuwa gida biyar da babban birni guda daya. Wadannan gidaje biyar din su ne:

Kogin kasa (Mansakonko)

Kogin taka-tsaki/ tsakiya (Janjanoreh)

Kogin sama (Yasi)

Sashen yamma

Bakin kogin Arewa (Kirowan)

Bikin samun 'yancin kai:

Ana bikin samun 'yancin kai a kasar Gambiya a ranar 18 ga watan Fabrairu sanadiyyar samun 'yanci da ta yi daga mulkin mallakar kasar Ingila shekara ta 1965, duk da haka kasar ta dade karkashin mulkin kasar Ingila har zuwa shekara ta 1970. Kuma a wannan shekara a ka bayyana kasar Gambiya a matsayin jumhuriyya.

Yanayin Kasa:

Kasar Gambiya a shimfide take, wanda hakan ya faru ne sakamakon ambaliyar ruwa da ya tsallakata. Wanda tsayinsa ya kai kilomita 300, kuma fadinsa baya wuce kilomita 50.  Yana bulbulowa daga kasar Ginea.

Yanayin shekara kasa:

A dunkule za mu iya cewa yanayin shekara a kasar Gambiya jujjuyawa yake yi, domin kuwa kasar tana da zafi mai hade da sanyi da damuna daga watan Yuni zuwa Nuwamba. Akwai kuma sanyi mai hade da zafi daga watan Nuwamba zuwa watan Mayu.

Yawan mutanen kasar:

A shekara ta 2018 mutanen kasar Gambiya sun kai kimanin mutum sama da miliyan (2,092,731). Babbar kabila a kasar ita ce kabilar Mandinka, wadda adadin mutanen ta ya kai kaso 40 cikin dari.

Addini:

Musulmin kasar sun kai kaso 95 cikin dari.

Harshe:

A kasar Gambiya an dogara da harshen Larabci a matsayin harshen kasar, hakan ya zo bayan an kawar da harshen Turanci. Kuma bayan kasar ta fita daga kungiyar kasashen renon Ingila.

Kundin Tsarin Mulki:

A shekara ta 2017 shugabannin hukuma da zababbun mutane sun yi taro don sun sanya iyaka ga tsarin mulkin kasar, a watan Disamba na wannan shekara aka kafa kwamita don ya duba wannan kundin tsarin milki, an nemi shekarar kowa da yake kasar wanda a karshe. Wadannan shawarwari suka tabbatar da gudadanar da suke neman ra'ayin mutane don a kafa kundin tsarin milki a shekara ta 2019.

Tsarin Hukunci:

Shugabancin Jumhuriyya, shugaban kasar na yanzu shi ne Adama Baro wanda ya karbi mulki tun 19 ga wata Janairu shekara ta 2017.

Hanyoyin Samun Kudin Shiga:

Tattalin arzikin kasar ya dogara akan noma da kasuwanci. Tashar jirgin ruwa Bangol tana daya daga cikin manyan kafofi na samun kudin shiga a kasar. A wannan tashar jirgin ruwa ana sauye – sauye na kasuwanci kimanin kaso 90 cikin dari. Kuma wannan tashar tana daya cikin tashoshin jirgin ruwa wanda suke daukar nauyin canje-canjen kudi a yankin Mali da Ginea Konakri da Ginea Bisau.

Manyan manyan Sana'antu:

Kasar tana da manya manyan sana'antu, daga cikinsu akwai sana'anta kyandir din zuma da katako da man bishiyar dabino.

Manazarta

  • Sashen CIA
  • Sashen Wekipedia
  • Takardar bincike mai taken "takaitaccen Tarihin kasar Gambiya wanda aka canja daga 1997-2012.