Jumhuriyyar Ghana
Asabar, Fabrairu 09, 2019
Jumhuriyyar Ghana

Jumhuriyyar kasar Ghana jumhuriyya ce da take nahiyar Afrika, haka kuma tana gabar Arewaci ne na kogin Guinea wanda yake a yammacin Afrika, wannan kasa ta sami 'yancin kanta daga kasar Birtaniya a shekara ta 1957. A da can ana kiranta da "Bakin Kogin Gwal". Sunanta na yanzu an sanya shi ne a bisa shahararren tarihin wannan kasa da kuma masarautar ta Ghana, duk da cewa ba ta cikin iyakar wadannan kasashe.

 

"Inda kasar take"

Kasar Ghana tana yammacin Afrika, ta hade da kogin Guinea, ta bangaren gabas kuma ta yi iyaka da kasar Togo, ta yamma kuma tana da iyaka da kasar Kwaddebuwa, ta Arewa tana da iyaka da kasar Burkina faso.

 

Yanayin Kasa

Shimfidaddiyar kasa ita ce ta fi yawa a kasar Ghana, ta inda ake samun shimfidaddiyar kasa a kudu da Arewa, inda muka duba tsakiya kuma, za mu ga akwai duwatsu na kasa wadanda tsayinsu ya kai mita dari shida. A gabas sananannu kogunan da suke kasar su ne farin kogin fulta da bakin kogin Fulta da Awati, akwai katangar Fulta wadda aka gina da ita. Wannan katanga tana daya cikin manyan aiyukan cigaba da aka yi a kasar ta Ghana.

 

Yanayin Shekara

Yanayin shekara a kasar ta Ghana ya hada da daidattaccen yanayi da yanayi mai caccanjawa.

 

Babban birnin kasar Ghana

Birnin Akra shi ne babban birnin kasar Ghana, kuma wannan babban birni ana sanya shi a daya daga cikin manyan birane a kasar, bugu da kari, wannan babban birni shi ne babbar cibiyar tattalin arziki da aikace aikace a kasar.

Haka kuma da siyasa da ke kasar ta Ghana wannan babban birni yana bakin kogin Arewa na kogin kasar Guinea, haka kuma wannan birni ya tattara hanyoyin sadarwa daban-daban, daga cikinsu akwai hanyar jirgin kasa, da kuma babban filin tashar jirgin sama. Wannan babban birni ya shahara da sana'antu, daga cikinsu akwai sana'anta tayal da zinari da katako, a cikin wannan babban birni akwai Jami'ar Ghana  wadda take Lijon. A cikin wannan makala za mu bijuro da abubuwa masu mahimmanci game da babban birni na kasar Ghana.

 

Kudin Kasar Ghana

Kudin Kasar Ghana tana da alamar GHC.

Yare

Harshen Turanci shi ne harshen da kasar take amfani da shi, duk da haka akwai yaruka daban kamar su Hausa da tare da Bejin.

Yawan Mutanen Kasar

Adadin mutanen kasa Ghana sun kai mutum milyan ashirin da tara da dubu dari shida da casa’in da hudu da dari biyu da ashirin da hudu (29.694.224) a shekara ta 2018, kamar yadda rahoton kasashen hadaka ya nuna.

Tutar kasar:

Tutar kasa Ghana tana da kaloli guda uku, wannan tuta tana da layika wadanda aka zana su a kwance, wadannan kaloli su ne ja da ruwan dorawa da kore hada da tauraru biyar masu bakin launi a cikin wani layi wanda yake da kalar ruwan dorawa.

Tsarin Mulki

Kasar Ghana tana da yanayin tsarin mulkin jumhuriyya da kuma majilisar dattijai wadda dukka wannan mulki a kasar yake hannunta. Haka kuma akwai majilisar kololuwa wadda take hannun dattijai na kasar ta Ghana da kuma karamar majilisa da take haunnun wakilai na kasar ta Ghana takensu shi ne Hadin Kai da Adalci

 Ranar Bikin Samun 'Yanci

Jumhuriyyar Kasar Ghana tana bikin samun 'yanci a duk ranar 6 ga wata Maris na kowacce shekara.

Siyasarta ta waje

Siyasar kasar Ghana ta waje ta kunshi kiran Nahiyar ta Afrika don hadin kai a fagen siyasa da zamantakewa da tattalin arziki za mu iya cewa sunan kungiyar kasashen Afrika da aka rada a shekara ta 2001 ya zo ne da ya tutubi ayyukan nahiyar ta Afrika wanda a wannan lokacin shugaba kasar ta Ghana na farko kuma ma'abocin duk wani tunani da ke kasar ta Ghana shi ne ya shugabanci wannan kungiya wato sunansa Kwami Nkaroma an yi hakan ne don a tabbatar da taimakon kasar ta Ghana ga irin wadannan ayyuka sa'annan da gyara kundin tsarin mulki na kasar ta Ghana a lokacin shugabancin Nkoroma don samar da tushen ja da baya ga wani yanki na mulkin kasar domin samun hadin kai tsakanin kasar Ghana da Guinea da Mali.

Tattalin Arzikin kasar Ghana

Yawancin mutane kasar Ghana suna yin noma. Kuma sun dauke ta a matsayin sana'a, Koko yana daya daga cikin manyan abubuwa da ake samarwa a kasar. Haka kuma akwai dabino da abarba da shinkafa da dankali da doya, haka kuma mutanen kasar Ghana suna kiwon shanu a guraren da suke da ciyayi, bugu da kari tattalin arzikin kasar ya dogara a kan kayan daki da shi da gini akwai sana'o'i da yawa kamarsu sana'anta alminyum da saka.

Daga cikin manya manyan abubuwa da tattalin arzikin kasar Ghana ya dogara akansu akwai sana'anta gwal saboda haka ne ma kasar Ghana da aka kiranta bakin kogin gwal, hakan ya sanya kasar Ghana abar kwadayi masu kudi na kasashen waje; domin suna zuwa kasar Ghana da su yi kasuwar kasar Ghana ita ce kasa ta goma a duniya wajen sanar da gwal.

 

Manazarta

Ministry Of Foreign Affairs and Regional Integration 

"Ghana", nationsonline

"Climate", ghanaweb,