Jamhuriyyar Kamaru
Asabar, Fabrairu 23, 2019
Jamhuriyyar Kamaru

Takaitaccen tarihi:

Kasar Kamaru ta mika wuya ga wasiyyoyin da kasashen Faransa da Birtaniyya suka yi mata, a dalilin haka ne yankin gabashin kasar ya samu 'yancin kansa a watan Janairu 1960. Sauran sassan kasar kuma suka sami 'yancin kai a watan Fabrairu, 1961, duka yankunan biyun kuma suka hade da juna a watan Octoba, 1961, bayan yin kuri’ar jin ra’ayin ‘yan kasa a watan Mayu, 1971, Kamaru ta zamo kasa daya al’umma daya karkashin jagorancin Amadu Ahijo, wanda ya hau kan karagar mulki tun 1960 a matsayin shugaban kasar na farko, ya kuma sauka daga kan mulki don kashin kansa a 1982, ya mika zuwa ga Paul Biya, wanda yake shugabantar kasar tun daga 6 ga watan Nuwamba, 1982 har zuwa yau..

Suna: Jumhuriyyar Kamaru.

Tsarin mulki: Shugabanci, jamhuriyya

Bikin samun 'yancin kai: Farkon watan Junairu a shekara ta 1960. Kasar Kamaru ta samu 'yancin kanta daga kasar Faransa.

Babban birni: Yawunde.

Manyan biranen: sun hada da Dwala, da Bafo San, da Victoria.

Wuri: Kasar Kamaru tana nan a tsinkiyar Afrika. Kasar Chadi tana iyaka da ita ta bangaren Arewa, daga yamma kuma kasar Naijeriya da Kogin Atlanta, kuma kasar Afrika ta tsakiya tana iyaka da ita daga gabas, kuma kasashen Kongo da Gabon da Equatorial Guinea suna iyaka da ita daga kudu.

Yanayin shekara:

Yanayin shekara a Kasar Kamaru yana zuwa da salo iri- iri, akwai lokacin da ake samun danshi, kaman yanda akwai inda ake yawan samun fari duka a kasar, ga kuma ta da yawan dazuzzuka da manyan duwatsu.

Girman Kasar: 

Kilomita murabba’i 475,442.

Yawan Mutane:

Adadin mutanen kasar Kamaru sun kai mutum milyan ashirin da biyar da dubu dari daya da goma sha daya da dari bakwai da goma sha takwas (25,111,718) a shekara ta 2018.

Harshe:

Farasanci da Turanci a matsayin harshen da za a dinga amfani da shi a kasar, duk da haka akwai yaruka daban daban na cikin gida.

Kudin kasa: Frank na Afrika.

Kundin tsarin mulki: an amince da kundin tsarin mulkin kasar Kamaru ne a ranar 20 ga watan Mayu, 1972, aka kuma fara aiki da shi a hukumance a ranar 2 ga watan Yuni, 1972, an kuma yi masa bita a watan Junairu, 1996, an kuma yi masa gyara a 2008.

Jam'iyyun siyasa:

Yunkuri mulkin demokradiyya na mutanen Kamrau (Jami'yyar Demokradiyya na Jama'ar Kamaru), Hadakar Jam'iyyun demokradiyya ta Kamaru, 'Yancin kare Jamhuriyar, Kungiyar Yunkurin neman 'yanci da ci gaban Kamaru, Kungiyar kasa don demokradiyya da ci gaban.

Yanayin Tattalin Arziki:

Noma ta kasasance ita ce sana'ar asali ga akasarin mazauna kasar 85% (tamanin da biyar cikin dari) daga cikin yawan ma'aikata.

Mafi Muhimmanci abubuwan noma:

Coffee, koko, auduga, roba, ayaba, hatsi, ganye da dabbobi.

Manyan masana'atu:

Man fetur, kuma sake farfada shi zuwa alumini’um da kayan abinci da saka.

Kungiyoyin duniya da na yanki da take ciki:

Kungiyar Tarayyar Afrika, da kungiyar tattalin arziki da kudi na yankin tsakiyar Afrika, da kungiyar kasashen rainon Faransa, da kungiyar gudanar da tafkin Chadi, da kungiyar gudanar da kogin Nijar.