Jumhuriyyar Libiya
Lahadi, Janairu 20, 2019
Jumhuriyyar Libiya

Babban Birni:

Tarablus shi ne mafi girman garin da ya fi shahara a kasar.

Dalilin kiranta da Libiya:

An sanya wa kasar sunan Libiya ne saboda kabilar Libo da take zaune a wannan yankin shekara da shekaru da suka wuce.

Wuri:

Kasar Libiya tana Arewacin nahiyar Afrika, bahrul Mutawassid yana iyaka da ita ta bangaren Arewa, daga gabas kuma kasashen kasar Misra da Sudan ne suka yi mata iyaka har zuwa kudancin gabas, sannan kasar Chadi da Nijar a kudu, zuwa yamma akwai kasar Algeriya da Tunisiya.

Girman Kasar

Kilomita murabba’i miliyan daya da dubu dari bakwai da saba’in (1.77)

Kasar Libiya ita ce kasa ta hudu wajen fadi a Nahiyar Afrika, kuma ita ce kasa ta 17 wadda ta fi kowacce fadi a duniya.

Rabe- raben Kasar:

Jihohin kasar Libiya sun kai 22.

Yanayin Kasar:

Kasar Libiya tana tsakanin layika guda biyu na “equator” daraja 19 da daraja 34 a Arewa da layika guda biyu na tsaye 59  26.

Addini:

Babban addini a kasar shi ne Addinin musulunci, mazahabin Ahlus-sunna kuma shi ne ya fi kowanne yaduwa.

Tutar Kasar Libiya:

Tutar kasar Libiya kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin samun 'yanci na shekara ta 1951 ta tattara launuka guda uku, wadanda su ne ja, da baki, da kore, a tsakiyar wadannan launuka akwai jinjirin wata da farar tauraruwa ana kiran wannan tuta da sunan tutar samun 'yancin kai, a ranar 21 ga watan Agustus shekara ta 2011 an daga wannan tuta, a kungiyoyin duniya da suke babban birnin Tarablus bayan samun 'yanci.

Harshen Asali:

Larabci – sannan akwai yaduwar Turanci da harshen Italiya a wanda ya yadu a tsakanin tsofaffi.

Yawan mutane

Kamar yadda ya zo a kafar "world meter" kasar Libiya ita ce kasa ta goma sha uku a yawan mutane, wanda suka kai kimanin miliyan shida da dubu dari biyar (6.5). kuma suna karuwa a duk shakara wanda hakan ya kai 1.51%.

Shekarun Mutanen Kasar

Kashi 27.7 daga cikin dari na mutanen kasar suna kasa da shekaru 15, kashi 68.4 % kuma cikin dari suna tsakanin shekara 15-64, kashi 3.9% cikin dari kuma suna sama da shekara 65.

Kundin Tsarin Milki

Sojojin kasar an kasa su gida hudu sojojin sama da na kasa da na ruwa.

Tattalin Arzikin kasar Libiya

Tattalin Arzikin kasar Libiya ya dogara akan fitar da man fetur da gas. Saboda haka ne yake tasirantuwa da yadda ake samar da fetur da gas a kasar.

Gas da Man fetur

Man fetur da Gas da kasar Libiya take fitarwa shi ne kashi 94 cikin dari daga kudin shiga a kasar, Libiya tana alfahari domin tana fitar da man fetur kimanin duro biliyan 41, kuma ita   ce ta fi kowacce kasa man fetur a Nahiya ta Afrika daga cikin wuraren da ake fitar da man fetur a kasar akwai “Haudh Sirt” da “Gadamis” da “Marzak” da yankunan da suke kogi a Arewa maso yammacin kasar, kuma har yanzu ana cigaba da bincike don gano wuraren da man fetur yake a kasar.

Tsofaffin sana'o'i a kasar

Garin Gadamis ya shahara da sana’anta fatu, saboda haka ne ma aka rada ma garin suna (Garin fatu).

Sana'o'in da suka dogara akan abubuwan sana'anta karfe.

Kafofin Yada labarai na Kasar Libiya

A wannan lokaci kafofin yada labarai na kasar Libiya sun kasance a karkashin hukuma, a ranar 29 ga watan Janairu shekara ta 2006 babban da Kazzafi mai suna Saiful Islam ya bayyana cewa hukumar kasar Libiya za ta bai wa gidajen telebijin da rediyo dama ta kansu. Bayan zanga zangar da aka yi a ranar 17 ga watan Fabrairu, an samu sababbin gidan jaridu da gidajen telebijin da rediyo masu zaman kansu, sai dai mafi yawancin wadannan tashoshi suna yada abubuwan da suke faruwa daga wajen kasar Libiya.