Masarautar Marocco
Litinin, Fabrairu 11, 2019
Masarautar Marocco

Takaitaccen tarihi

Masatautar kasar Moroco tana nan a cikin jerin kasashen arewa maso yammacin nahiyar ta Afrika. Kasar Moroco tana hudowa da bahrul mutawassit, da kuma kogin Atlanta ta bangaren yamma, a bangaren Gabas ta yi iyaka da kasar Aljeriya, a bangaren kudu kuma kasar Muriyanya ita  ce take iyaka da ita, kasar Moroco ta samu 'yancin kanta daga kasar Faransa a shekara ta 1956, haka kuma kasar ta tsunduma cikin kungiyar Majalisar dinkin duniya a ranar 22 ga watan afrilu na wannan shekara ta 1956, ta kuma zama mamba a kungiyar kasashen Larabawa a shekara ta 1958. Musulmai sun bude kasar ta Moroco a shekara ta 683 miladiyya karkashin jagorancin Ugubatu dan Nafi'u.

 

Babban Birni

Manya manyan biranen sun hada da “Al- Ribad” wanda yake birni ne na siyasa, sannan “Dar al-baidaa” ko “Casablanca” wanda yake birni na tattalin arziki. “Fas” kuma nan ne birnin ilimi da duk wata wayewa, da kuma garin “Danja” da “Marakish” da “Akadir”.

Kudin Kasar

Shi ne dirhami, farashin dola, yana kai kawo tsakanin dirhami 9 da dirhami 9 da dugo 55.

Harshen Larabci shi ne harshen da kasar take amfani da shi, kundin tsarin mulki da aka yi a shekara ta 2011 ya kara harshen Amazig a matsayin harshen da za a dinga amfani da shi a kasar, wannan harshe na Amazig ya yadu da harsuna guda uku. A kasar Moroco ana bikin murnar samun 'yanci a duk ranar 30 ga watan Yuli na kowacce shekara.

Yanayin Shekara

Yanayin da ya fi yawa a kasar Moroco shi ne yanayi daidaitacce wanda yake tasiri da yanayin bahrul mutawassit, da yanayin kogin Atlanta a yamma da kuma Arewa maso yamma, idan aka duba ciki za a ga cewa yanayin kasar yana da sahara mai zafi da kuma tsananin sanyi a kudu.

Adadin Mutane

Daidai da kidayar mutane da aka yi a kasar a shekara ta 2014 mutanen kasar Moroco sun kai mutum miliyan 33 da dubu 848.

Tsarin siyasar kasar

Masarautar Moroco daidai da yanda ya zo a kundin tsarin mulki na kasar a shekara ta 2011 an canja tsarin mulkin kasar zuwa masarauta wanda sarki shi ne zai rinka mulkar kasar kuma ya nada fira minista daga jam’iyyar da ya fi kowa samun nasara a wajen zabe.

Jamiyyoyin Siyasa

A kasar Moroco akwai jamiyyu guda 32 wasu daga cikinsu tsofaffi ne tun lokacin da kasar ta samu 'yancin kanta, wasu daga cikinsu kuma sababbani sun zo tare da cigaban siyasa, ko kuma sakamakon wasu dalilai na zamantakewa, yawancin wadannan jam’iyyu ne na wadanda ba ruwansu da addini, dokar jamiyyun siyasar ta hana kafa jam’iyyu wadanda suke da alaka da addini, ko harshe, ko kabila, ana kirgar Morocco daya daga cikin kasashen da suka san jam’iyyu na siyasa tun a shekara ta 1934 lokacin da suka yi yaki da mulkin mallakar Faransa.

Majalisar dattijai ta kasar Moroco

Kasar Moroco ta san abin da ake kira da majalisar dattijai a shekara ta 1962 bayan an tattabar da kundin tsarin mulki a shekara ta 1962 kuma majalisar dattija ta kunsi majalisa guda biyu 1996 majalisar wakilai wadda ta kunshi memba 395 wadanda aka zabe su kai tsaye don su yi mulkin shekara biyar da kuma majalisar masu ba da shawara wadda ta kunshi memba 265 wanda aka zabe su daga wadanda aka zaba a dakuna sana'a tsawon shekara 1934 kuma ana sabontashi duk shekara uku.