Jumhuriyya Murishiyos
Litinin, Disamba 31, 2018
Jumhuriyya Murishiyos

Kasar  Murishiyos wasu tsuburarruka ne da suke tattare a kogin Hindu / kogin India wadanda suke nesa da kimanin kilomita 2000 daga bakin ruwan Arewa da gabas na nahiyar Afrika. Larabawa masu shiga kogi su ne farkon wadanda suka gano kasar Murishiyos kuma suka kirata da (duniyar Larabawa) sannan bayan haka mutanen Portugal suka zo bayansu a karnina goma sha shida, wannan tsibiri ya dade babu mutane har sai da mutanen Holand suka kirkiri karyar cewa nasu ne a shekara ta 1598, sannan suka kirashi da suna Murishiyos saboda imani da suka yi da Sarki Moris, sarkin garin nasu.

An tabbatar da tsibirin Murishiyos a sha biyu 12 ga watan Maris, wanda tutar kasar ta tattara launuka guda hudu su ne: ja, da shudi, da ruwan dorawa. Wadannan launuka an jera su ne a kwance.

  • Ja yana nuni da jinin da aka zubar domin samun 'yancin kai.
  • Shudi kuma yana nuni da kogin Hindu wanda ya kewaye wannan tsibirin.
  • Kore kuma yana nuni da arziki shuka da ke wannan tsibiri gurin da take da kuma Girmanta.

Kasar Murishiyos ta kasance wani yanki ne na tsibirarrukan maskarin. Wannan kasa tana nan a kogin Hindu. Kuma tana gaba da gaba da bakin ruwan nahiyar Afrika wanda yake a gabas, haka kuma tana nesa da gabas din kasar Madagaska a kogi Hindu da kilomita 800. Girman kasar tsibirim Murishiyos ya kai kilomita 2030 akan kasa da kuma kilomita goma a cikin ruwa; wato dai girman wannan kasa a dukule ya kai kilomita 2040.

Babban birni:

Babban birnin Murishiyos shi ne tashar jirgin ruwan (Port Luis) wanda shi ne birnin  tashar jirgin ruwa ta farko da aka kafa a garin.

Jumhuriyya Murishiyos ta kasu zuwa yankuna guda tara. Bakin kogi, Falak, babbar tashar jirgin ruwa moka, Bomblimos, Bilen welemez, Port Luis, Kogin Rifarmat, Savana. Da kuma yankuna a guda uku wadanda suke mabiya ne kamar haka:

(Tsibirarrukan Rodrigez) wadannan tsibirarruka sun sami 'yanci daga kasar Murishiyos a shekara ta 2002, har yanzu kasar tana neman ta kara mulkar wadannan tsibirarruka.

  • Sant Brandon – tsibirarrukan Ajaleja.

Bikin samun 'yancin kai

Tun lokacin da kasar Murishiyos ta sami 'yancin kanta daga hadaddiyar masarauta. Shekara ta 1968 har zuwa 1992 wannan kasa ta kasance karkashin tsarin mulkin na masarauta wanda Elizabet take jagorancinsa. A shekara ta 1992 kasar Murishiyos ta zama Jamhuriyya.

Yanayin kasar

Kasar Murishiyos kasa ce ta duwatsu masu aman wuta a kogin Hindu tsarin wannan kasa daidaitacce ne sawa'un a babban tsibiri, ko kananan tsibirarruka da suke gefenta ta inda tsayin / tudun kasa a garin kuma a bakin dutse ya kai sama da mita 800.

Yanayin shekara

Kasar tana da yanayi na shekara daidaitacce sanadiyyar kasancewarta matattara ta tsibirai. Ruwa kuma yana sauka a garin wanda hakan ya taimaka wajen samun dazuka a wasu yankuna a garin.  Al'amarin da ya haifar da tafiye-tafiye don yawon bude ido a kasar Murishiyos.

Adadin mutanen kasar

Mutane 1,364,283 kamar yadda yake shekara ta 2018.

Addini:

Addin Hindus yana da kaso hamsin 50 cikin dari. Kiristanci kuma yana da kashi 30 cikin dari na mutanen kasar. Addinin Musulunci kuma yana da kashi 17 cikin dari.

Harshen kasa

Turanci da Farasanci ba tare da samun fifiko ba.

Tsarin mulki

Dimokradiyya

Hanyoyin samun kudin shiga

A lokacin mulkin mallakar kasa Ingila tattalu arzikin kasar Murishiyos ya dogara ne, a bisa samar da sukari da sayar da shi ga kasashen Turai, bayan kasar ta sami 'yanci hukuma ta bambanta hanyoyin samun kudin shiga ta hanyar gina kamfanoni da hidimtawa ta (Logistits) da kuma samun ci gaba a bangaren yawon bude ido.

 A sabuwar shekara dubu kuma tattalin arzikin kasar Murishiyos ya samu cigaba sosai. Kuma an sami hanyoyin samun kudin shiga daban daban a kasar kamar su kere kere da yawon bude ido da kasuwanci da hidimce hidimice.

Siyasa kasar ta waje

Kasar Murishiyos memba ce a kungiyoyi daban daban na gida da na waje, hakan ya faru ne sanadiyyar kyan kasa da yanayi da Allah ya yi wa garin, daga cikin wadannan kungiyoyin akwai- kungiyar kasashen Afrika Comesa – Comlenth, kungiyar kamar da kabilanci.Kungiyar asasun duniya.