Jumhuriyyar Musulunci ta Muritaniya
Laraba, Afrilu 03, 2019
Jumhuriyyar Musulunci ta Muritaniya

Kasar Muritaniya, kasa ce  ta Larabawa wadda ake kira da jumhuriyyar Musulunci ta Muritaniya, hakan ya faru tun lokacin da addini Musulunci ya shiga kasar a Karni na takwas da haihuwar Annabi Isa. Sai dai addinin bai gama yadauwa ba sai lokacin da aka kafa daular Murabuduna shekarar 1902, a lokacin da Faransawa suka shiga kasar don mulkin mallaka a farkon karni na ashirin. Ta sami 'yancin cin gashin kai a 1956, Nouakchott ne babban birnin kasar.

A shekara ta 1958 aka sanar da samun 'yanci na kasar aka kuma kafa sojoji aka zabi Mukhtar Wulud Dadah a matsayin Fira Minista.

A 28 ga watan Fabrairu 1960 aka sanar da 'yancin kasar, Mukhtar Wulud Dadah ya zama shugaban kasar Muritania na farko.

Inda take da girmanta:

Kasar tana nan a arewacin yammancin Afrika a bakin kogin Atlas, daga Arewa tana da iyaka da Marocco da Algeria, daga kudu kuma tana da iyaka da Senegal, daga gabas da kudu kuma tana da iyaka da kasar Mali, kuma kasar ita ce wadda ta hada tsakanin Arewacin da kuduncin Afrika kamar kasar take da sahara.

Yanayain tudu da kwararrur kasar

Kasar tana da kwarurruka da turbaya wadda take akan kasa mai fadi.

Yanayin shekara:

Kasar Muritaniya tana nan a bangaren Arewa na daidaitaccen layi saboda haka yana da wahala a yi ruwan sama a kasar, kamar yadda take da zafi da sahara mai fadi da girma.

Babban birni: Nouakchott

Adadin jihohin kasar: akwai jihohi goma sha uku.

Tutar Kasar: An tabbatar da tutar kasar a 22 ga watan Maris 1958 a lokacin da aka kafa sojojin kasar wanda tutar koriya ce a cikinta akwai jinjirin wata a tsakiya da taurawa a samansa da launin darawa. Koren launa yana nuni da kasa ruwan dorawa kuma yana nuni da sahara jinjirin wata kuma da tauraruwa suna nuni da addinin Musulunci.

Adadin Mutane Kasar:

Alkalumman kidanya da aka yi a kasar Murtania a 2017 sun nuna cewa adadin mutane a kasar ya kai kimanin mutum miliyan hudu da digo arba’in da biyu (4.42).

Kudin kasar: ogoba.

 Harshe :

harshen Larabci shi ake amfani da shi a kasar duk da cewa akwai harshen Faransanci da Turanci kadan.

Tsarin Mulki:

Jumhuriyya, shugaban kasar shi ne Muhammadu Wulud Abdul’Aziz.

Tattalin Arziki:

Kasar tana samun tattalin arzikinta daga su a kogi, da kuma karfe da gwal. Noma a kasar ba shi da yawa duba da yanayin da kasar take da shi na sahara game da abubuwan da ake nomawa kuwa akwai dabino da shinkafa da masara suna kuma kiwon dabbobi.

A wajen sana'o'i kuma kasar tana sana'arsa kifin gwangwani; domin Muritinya tana daga cikin kasashen da suke da kifaye a duniya. Kasar tana kawo kaya daga da abubuwa daga kasashe daban daban kasar ana sanya ta cikin kasashen da tattalin arzikinsa ba shi karfi.

Inda take samun kudin shigo:

Farautar kifaye, noma , mai fetur.

Tsarin Siyasa:

Tsarin jumhuriyya shi ne tsarin kasar a duk shekara biyar ana zabe a kasar, kuma bai halatta ga shugaban kasa ba ya mulki kasa ba sama da zagaye biyu a jere ba, 'yan majalisu a kasar su aka fi karfafawa a lokacin zabe, kuma ba zaman majalisu da ake yi ana yin shi ne kai tsaye ido na ganin ido, karara haka, kuma su ma 'yan kasa suna da hannu wajen kula da wakilai da aka zaba, suna kula da aikinsu, ko ba a yi don kare siyasa.

Kafafen sadarwa:

Kasa tana da gidan jaridu tun lokacin mulkin mallaka 1945, sanadiyyar haka ne aka sami marubuta da dama a kasar, hakan ya taimaka sosai ga gidan jaridu bayan a n sami 'yancin kai a 1960.

A shekara 1975 an samu sabuwar jarida sa'annan jaridar mata da wayewa ta bayyana a kasar 1991, dokoki na farko da suka bayyana a kasar sun zo ne a 1991, da farkon 2002 an kafa kafafen Internet don amfani da su wajen labarai.

Kamar yadda ake kafa ma'aikatar labarai a kasar a shekara ta 1995 mai suna ma'aikatar labarai ta Muritaniya a lokacin da jarida ta farko ta bayyana wadda aka buga da harshen Faransanci da Larabci.