Namibia
Laraba, Mayu 08, 2019
Namibia

Inda Kasar take:

Jumhuriyyar Namibia tana nan a kudu masu yamma na nahiyar Afrika, kasar Angola da Zambia su ne suke iyaka da ita ta bangaren Arewa, daga gabas kuma kasar Botswana ita ce take iyaka da ita, daga gabas kuma da kudu kasar Afrika ta kudu ita  ce take iyaka da ita. Tsawon iyakar kasar ya kai kilomita 3936. Tsawon bakin ruwanta kuma ya kai kilomita 1500.

Girmanta:

Girman fadin kasar Namibia ya kai 824299 kilomita. Daga Arewa da kudu tana da tsawon tafiyar kilomita 1498, daga gabas kuma da yamma tana da tsawon tafiyar kilomita 880. Kasar Namibia tana nan  a tsakanin ruwa guda biyu da sahara guda biyu, ta inda iyakokinta na Arewa da kasar Angola suka fara daga bakin kogin na bangaren yamma na kogin Orange wanda yake musalta  iyakoki na siyasa tsakanin kasar da kasar Afrika ta kudu ta bangaren yamma, kuma tana farawa da saharar Namibia a bisa tsayin bakin kogin Atlas har zuwa tsakiyar saharar Kalahary wadda take a yamma.

Harshen Kasar:

Harshen Turanci shi ne harshen da ake amfani da shi a kasar. Harshen Afrikanz shi ne wanda yawancin mutanen kasar suke magana da shi kamar yanda akwai yaduwar harshen Jamus wato Jamusanci a kasar, tare da harsuna daban daban guda 10 na cikin gida daga cikinsu akwai Oshipambo da Nama da Kafonjo da Kabirife.

Tutar Kasar:

Tutar kasa tana dauke da kaloli guda hudu su ne: shudi, da fari, da ja, da kore, akwai rana a kan launin shudi wadda take nuni da rayuwa da damar yin aiki hasken ranar kuma yana nuni zuwa kabikin da suka yadu a kasar.

Tsarin Mulki: Jumhuriyya

Tattalin Arziki:

Noma: Adadin wadanda suke noma a kasar ya kai kashi 31 cikin dari na yawan mutanen kasa. Noma yana taimakawa da 4 % na abin da ake samarwa a kasar a na noma gyada da a kasar. Sanadiyyar rani da ake fama da shi a kasar da rashin saukar ruwan sama kasar tana kawo kashi 50 cikin dari na Abin da take bukata daga kasashe ketare. A kasar akwai tashar gidan talibijin guda biyu da jaridu 13 hada da gidajen radiyo guda 25.

Siyasar Kasar  waje:

Kamar yadda yake a nassi na 90 na kundin tsarin mulkin kasar, manufar siyasar waje ta kasar ita ce kasar ta tabbatar cewa ta kafa siyasa wadda ba ta nuna karkata zuwa wani bangare tare da taimakawa, huldodin kasashen waje da samar da tsaro da zaman lafiya tare da girmama      dorkar kowacce kasa a karkashin yarjejeniya da aka yi ta gida ta waje.