Sudan
Asabar, 29 Disamba, 2018
Sudan

Nahiyar

Jumhuriyyar kasar Sudan: Kasar Larabawa ce a Afrika, tufar da kasar take amfani da ita, a yanzu an kirkirre ta ne a 20 ga watan mayu 1970, tufar ta kunshi kaloli uku: ja da baki da kuma fari, akwai kuma koriyar kusurwa a gefen hagu.

Kasar Sudan tana Arewa maso kudancin Afrika, ta yi iyaka da kasar Ertria da Ethiopia ta gabar, ta Arewa kuma tana da iyaka da kasar Misra da Libiya, ta yamma kuma tana da iyaka da kasar Afrika ta tsakiya da kasar Chadi, ta kudu kuma tana da iyaka da kasar Sudan ta Kudu.

Sudan ita ce babbar kasa ta uku a Afrika a fi fadin kasa, ta tattara yanki ko filin kilo mita 1, 865, 813.

Babban birni:

Garin Khartum wanda ya kunshi birane uku:

  • Karto: Babban birnin siyasa.
  • Omdorman: Birnin tarayya.
  • Kartum: Birnin masana’antu.

Ranar samun ‘yanci

Ta samu ‘yancin kai a ranar  1  ga  watan Janairu. Mutanen Sudan suna murna da wannan rana; domin samun ‘yanci daga mulkin Inglishi da Misra.

Adadin mutanen kasar Sudan:

Kimanin 43, 120,843.

Addini:

Musulunci da Kiristanci da kuma addinan gargajiya.

Harsuna:

Larabci da sauran harsunan gida da wanda suka kai kimanin harsuna 300.

Kundin tsarin mulki:

Kundin tsarin mulkin shekara ta 2005.

Kasar:

Kasar Sudan tana karkashin jagorancin mulki guda uku:

Na farko: karfin tsarin mulkin wanda shugaban kasa yake jagorantarshi haka kuma shi ne yake jagorantar shugabancin majilisar dattijar.

Na biyu: karfin mulkin gwamnoni.

Na uku:  karfin tsarin mulki ciyamomi wanda suke jagorancin kananan hukumomi na jiha.

Karfin lauyoyi, kungiyar lauyoyi tana da ‘yancin kanta ba kuma ta karkashin kungiyar majalisar dattijai, haka kuma ita ce take daukar nauyin kanta, kuma ba karkashin Gwamnati take ba. Shugaban kungiyar lauyoyi kuma shugaban Kotun koli ta kasa.

Hanyoyin da take samun kudin shiga:

  • Noma na daukar kashi tamanin na ayyukan mutane.
  • Ma’adanai da danyen mai
  • Kiwo

Manyan masana’antu:

Kamfanin saka, kamfanin siminta, da kamfanin man abinci, kamfanin siga da kamfanin sabulu, da kamfanin ledodi da kamfanin kayan abinci da masana’antar ma’adanai.

Alakar ta da kasashen waje:

Alakar Sudan ta waje ta hada da kasashen Larabawa Musulmai. Bugu da kari tana da kyakkyawar alaka da kasashen Turai, kuma tana kokarin ta ga ta tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin da kasashen ketare, musamman kasar Uganda da kasar Chadi.

Kasar Sudan mamba ce a kungiyoyin kasashen gida da waje kamar su Majalisar Dinkin Duniya(UN). Kungiyar Kwadugo ta duniya (ILO) da kungiyar United Nation Educational da kungiyar kimiyya da Ala’du (UNESCO) da kuma kungiyar Tarayyar Afrika (AU).