Jumhuriyyar Uganda
Litinin, Maris 18, 2019
Jumhuriyyar Uganda

Kasar Uganda tana gabashin nahiyar Afrika, ana yi wa kasar kirari da “Zinariyar Afrika”, ta yi iyaka ta bangaren gabas da kasar Kenya, ta bangaren arewa kuma ta yi iyaka da kasar Sudan, ta bangaren yamma ta yi iyaka da Kongo Dimokradiyya, ta bangaren Kudu kuwa ta yi iyaka da kasashen Rwanda da Tanzania, sashe mai yawa na tafkin Biktoriya yana yankin kudancin kasar, inda ta yi tarayya da kasashen Kenya da Tanzania, kasa ce da ba ta a gabar teku.

Fadinta : kilomita murabba’i dubu dari biyu da talatin da shida, da digo arba’in (236.40).

Babban  birni: Kambala.

Harshen da take amfani da shi:

Suna amfani da harshen Turanci da harshen Swahili kamar yadda suke da harsuna daban-daban wadanda ake amfani da su.

Adadin Mutane:

Adadin mutanen kasar sun kai miliyan talatin da biyar (35,000,000).

Yadda ake raba kasar:

Kasar Uganda tana da jihohi dari da goma sha biyu (112)

Manya Manyan Garuruwa:

Antibi – Janja -  Mbali – Galo- Fort Portal.

Tsarin Hukunci: shugabanci, Jamhuriyya

Kasar Uganda ta sami sunanta ne daga masarautar Buganda, wadda ta kunshi yankuna daban daban daga kudancin kasar ciki har da babban birnin kasar Uganda, kasar ta samu 'yanci kanta a ranar 9 ga watan Octoba, shekara ta 1962.

Yanayin Siyasa:

Kasar Uganda ta samu kwanciyar hankali na siyasa tun lokacin da jam’iyyar gwagwarmayar kasar, karkashi jagorancin shugaban kasa Yuri Musfini ta amshi ragamar mulki a shekara ta 1986.

Kasar Uganda tana cikin kasashen gabashin nahiyar Afrika da suke samun taimakon sojo daga kasar Amurka, bugu da kari da rawar da  kasar Uganda take takawa a kasar Somalia da Sudan ta Kudu wajen samar da zaman lafiya da yaki da ta'addanci.

Tattalin Arziki:

Kasar Uganda tana daga cikin kasashe masu karfin tattalin arziki a shekara ta 2017 tattalin arziki ya bunkasa kimanin 47% kamar yadda shugaban kasar ya yi gyare gyare a kasar tun lokacin da ya dare kan karagar mulki.

Bankin duniya ya nuna cewa tattalin arziki na Uganda ya karu sakamakon ruwan sama da karuwan masu zuba jari, da kuma man fetur. Kudin da ake kawowakasar ya kai Dola milyan 3.5 kamar yadda yawan bude ido a kasar yake kawo kudi sosai.