Gina Sabuwar Dimukradiyya a Afrika Daga Hasashen Solon Saboda Yaduwar Arziki
Litinin, 31 Disamba, 2018
Gina Sabuwar Dimukradiyya a Afrika   Daga Hasashen Solon  Saboda Yaduwar Arziki

Shafin wannan littafi 200 (dari biyu) ne, mawallafa ya yi magana akan matsalolin da yakin Afrika ke fuskanta. Abu mafi muhimmanci a ciki shi ne tambayar da ya yi na cewa: shin da gaske shugaban Turawa suna aiki domin yi wa tsarin Afrika hidima wajen gina dimokuradiyya a yakin Afrika..?

Mawallafin ya karkata zuwa ga cewa "lallai Afrika ba ta bukatar tsarin dimokradiyyar da zai rarraba tsakanin ‘yan kasa, gina sabuwar dimokradiyya yana nufin sake yi mata fasali akan ginshinkan da “Solon” -wanda shi ya kirkiro Dimokradiyya- ya dora ta a kai, wato hakan yana nufin kafin a gina nagartacciyar Dimokradiyya akwai bukatar bin abin sannu a hankali, ba wai a fara a rana daya, a kare kuma a wannan ranar ba, kaman dai yanda aka gine ta a garin “Asina” da tsohon tarihin da muka sani. Haka ma marubucin ya nuna irin yanda Dimokradiyyar Girka mai tarihi za ta yi daidai da abubuwan da suke faruwa a Afrika, ganin cewa sashen al’adu da na zamantakewa kusan abu daya ne.

A gefe daya kuma Marubucin ya kuma bayyana matsalolin da tsohon shugaban Amurika Obama da tsohon shugaban Faransa Huland suka fuskanta, da ma zanga zangar da aka yin a nuna kin jinin da shugaban Amurika na yanzu, wato Trumb ya fuskanta bayan zabensa, da wadannan mutane wadanda suke kira cewa "Trumb ba shugabanmu ba"; shin duka wadannan abubuwa za su farlanta yin tambayar: shin manyan kasashen turai a shirye suke su taimaka wajen gina Dimokradiyya ta Allah da Annabi a yankin  Afrika?

Marubucin shi ne: “Prosper Alagbe”, asalinsa dan kasar  Benin ne, yana da ayyuka masu yawa. Kokarinsa a koda yaushe shi ne fito da manyan matsalolin da Afrrika take fuskanta, da kuma nemo hanyoyin warware su. A shekara ta 2009 ya kafa cibiyar nazarin bincike wanda yana da alaka da batutuwa masu muhimmanci.