Hadakan Tsakanin Kungiyar Tarayyar Turai da Kasashen Afrika Akan Matsalar Gudun Hijira: Matsalolin Tare da Maslahohi Masu Karo da Juna
Laraba, 2 Janairu, 2019
Hadakan Tsakanin Kungiyar Tarayyar Turai da Kasashen Afrika Akan Matsalar Gudun Hijira: Matsalolin Tare da Maslahohi Masu Karo da Juna

Tun shekara ta 2015, daidai lokacin da matsalar kwararar 'yar gudun hijira daga Nahiyar Afrika zuwa Nahiyar Turai yake kara kagama ne, ake ta tattaunawa tsakanin kasashen Turai da kasashen Afrika game da ci- rani da yake da muhimmanci, da nufin kawo karshen wannan kwarara da ‘yan gudun hijira suke yi zuwa wannan nahiya ta Turai. Da kuma kokarin kara adadin masu komawa zuwa kasashensu na asali daga cikin ‘yan gudun hijiran da ba bisa ka’ida da suke yi. A cikin wannan yanayi ne, kungiyar Tarayyar Turai ta kirkiri wani sabon tsari taimakekeniya tare da kasashen masu tasowa, bayan ta gudanar yarjejeniya tare da kasar Turkiyya game da wannan al’amari a watan Maris ga shekarar 2016. Wannan tsari na musamman yana da dangantaka ne da kasashen Afrika; saboda wadannan kasashe su ne wadanda suke fitar da 'yar ci-rani zuwa Yakin Turai. Abin da ya kara samar da wani sabon fage a cikin siyasar harkokin kasashen waje na kungiyar tarayyar Turai game da ‘yan gudun hijira, wanda har yanzu sakamakon da aka samu a ciki bai taka-kara ya karya ba, duk kuwa da cewa wannan batu shi ne ya mamaye mafi yawan siyasar harkokin kasashen wajen ta kungiyar take bi, kai har ma da siyasar da mambobinta suke bi, ma’ana za a iya tabbatar da cewa matsalar ‘yan gudun hijira ce kan gaba a ayyukan siyasar da kungiyar tarayyar Turai take bi..

Saboda cin ma wadannan manufofi ne kungiyar tarayyar Turai ta rungumi samar da wani asusu “Asusun ayyukan raya kasa na gaggawa”, wannan siyasar hadaka game da matsalar ‘yan gudun hijira ya samar da shi, aka kuma amince da shi a taron kolin “Valette” a watan Nuwamba, 2015 a kasar Girka, abin da yake karfafa taimakekeniya a bangarori uku: manufofin gudun hijira na siyasa da na tsaro da na ayyukan raya kasa. Sai dai duk da haka, sakamakon wannan asusu na gaggawa bai haifar da wani abu na a zo a gani ba, hasali ma wannan taimakekeniya ce da turawan ne kawai suke mallakar wuka da nama a cikin, a daidai lokacin da su kasashen na Afrika ba su da katabus wajen sanya manufofinsa da zartar da shi..

Taimakekeniyar kasashen Turai a fagen ‘yan gudun hijira ya fara bayyana ne a lokacin da samar da 'yancin zirga-zirga da shige- da fice a yakin Turai gaba daya. Wannan taimakekeniya tsakanin kasashen da suke fitar da 'yan ci-rani a matsayin manufar shirin na biyar wanda Majilisar Turai  yi na’am da shi a shaekarar 1999, don kara karfafa siyasa na ciki da na waje ga Tarayyar Turai.

Marubuci:

“Matthieu Tardis”: Marubuci ne da ya sami (diplom) babban digiri a nazarin Turai. Ya yi aiki a cikin wata kungiya ta kasar Faransa, wadda take taimaka wa 'yar gudun hijira. Kuma ya taimaka sosai wajen karfafa kwarewa wajen ta’amuli da matsalar 'yar gudun hijira a kasar Faransa da Turai da Tunusiya ta hanyar nazari da ayyukan Turai da na kasa da kasa.