Cutar Hanta: A Kalla Mutane Miliyan Daya Ke Mutuwa Duk Shekara A Duniya- Bincike
Lahadi, Janairu 05, 2020
Cutar Hanta: A Kalla Mutane Miliyan Daya Ke Mutuwa Duk Shekara A Duniya- Bincike

Bincike ya nuna cewa akwai abubuwan dake janyowa dan adam cutar hanta wadda a aturance ake kiranta da Hepatitis da hanyoyin da za abi don a magance ta da yadda za’a baiwa jiki garkuwa. Bugu da kari, cewon ya kasu iri-iri da hanyoyin dake janyowa a kamu data dda da alamominta. Ire-iren cutar biyar sune, Hepatitis A, Hepatitis B, Hepatitis C, Hepatitis D, Hepatitis E,inda kuma daga cikin wannan ire-iren, akwai masu bacewa da kansu bayan sun dan adam, inda kuma wasunsu sai anyi magani. Har ila yau, wasunsu basa Tsananta, inda kuma wasunsu suna tsanantawa amma bincike ya nuna cewa, cutar Hepatitis A, Hepatitis B, da Kuma Hepatitis C sune suka fi wanzuwa tsakanin bil adama. Kamar yadda binciken ya sanar, cutttukan hanta suna da yawa bawai cutar bace kadai ke lakata hantar wanda ya kamau da cutar ba akwai sauran cututtuka da dama dake lalata hanta ko yi mata wani lahani wadanda au ana gadon su ne daga gun iyaye kuma ya danganta ne daidai da gwargwadon ahekarau dan adama Cutar, tana janyo mutuwar zuciyar wanda a kamu da ita da lalacewar kodar sa da rufe masa hanyar dake daukar jini daga hanta zuwa zuciyar wanda ya kamu da kuma lalacewar huhu ga masu yin tu’amalli da shan taba sigari da sauran su.

Yadda ake daukar jini daga hanta zuwa zuciya Kamar yanda bincike ya nuna a Shekarar 2015 akalla yan adama miliyan 114 ne ke dauke da cutar “Hepatitis A” a fadin duniyauk , inda kuma kalla bil adama su miliyan 343 ne ke dauke da “Hepatitis B”. Har ila yau, a kalla mutane miliyan 142 ke dauke da “Hepatitis C” a fadin duniya, inda kuma a kalla bil adama su miliyan daya ke rasuwa a duk shekara a fadin duniya. Bugu da kari, bincike ya nuna cewa, a kasar Amurka akalla mutane 250,000 ne ke kamuwa da wannan cuta a duk shekara, yayinda akalla mutane 75 ke rasuwa a duk shekara sanadiyar Hepatitis.

Almomin Cutar Hanta:

Hepatitis A:- ciwon ciki, Zafin Jiki, Amai, Tashin Zuciya, Kasala, Bakin Fitsari, Idanuwa da Fata su koma rawaya-rawaya da sauransu, inda ita irin wannan nau’in na cutar, bata tsananta in an kamu da uta.

Hepatitis B:– Zafin Jiki, Kasala, Idanuwa zasu yi yalo da fta da Idanuwa, Gudawa da Kuma wasu alamomin masu kama da Cutar murar tsintsaye kuma wannan nau’in na cutar, wani lokacin bata alama haka, tana iya tsananta da kashi 10 cikin dari na mutanen da suka kamu da ita.

Ita kuwa, Hepatitis C:- Iri daya ce da Hepatitis B, amm wannan tana iya tsananta da kashi 75 zuwa kashi 80 cikin dari na wanda ya kamau da ita. Tsawin kwanaki daga lokacin shigarta jikin wanda ya kamau har zuwa bayyananar lamominta:

Hepatitis A:- Daga sati biyu zuwa Smaati Bakwai ita kuwa cutar Hepatitis B, daga sati shida zuwa sati ashirin da uku,inda kuma cutar Hepatitis C daga sati biyu zuwa sati biyu ko zuwa sati ashirin da biyar.

Abubuwan dake haddasa cutar hanta:

Hepatitis A:- abinda ke Hmhaddasata shine wani Kmkwayar Cmcuta da Imido baya iya gani, unda ita kuma cutar Hepatitis B, Hepatitis B Birus (HBB) haka ita kuma cutar Hepatitis C:- Hepatitis C Birus (HCB). Har ila yau, yawan tu’ammali da barasa da gubar dake fita dake fita da matsalar garkuwar jiki da yin amfani da kwayoyin magani bisa Bisa ka’ida ba ana kuma yin gado da sauransu. Hanyoyin kamuwa da cutar: Hepatitis A:- Gurbatuwar abinci ko ruwan sha da ya gurbata da sauransu.

Cutar Hepatitis B:- idan aka sanyawa mutum jinin mai dauke da ita da yin amfani da allura ko Reza dake dauke da kwayar cutar daga Uwa zuwa Danta da lokacin yin jima’I a tsakanin mace da namiji dake dauke da cutar da sauransu.

Hepatitis C:- Sanyawa mutum jinin mai dauke da ita da yin amfani da allura Ko Reza mai dauke da kwayar cutar da musayar abubuwan tsafta wanda mutum daya ya kamata ya yi amfabi dashi da sauransu.

YADDA AKE GANO CUTAR A JIKIN DAN ADAM

Ana Iya Gano Cutar Hepatitis (ciwon Hanta) Ne A Jikin Mutum Bayan Alamunta Sun Fara Bayyana, Daga Nan Sai Ayi Gwajin Jini Biyo Bayan Zukar Jinin Mutum.

Yadda ake magance ta:

Zuwa asibiti mafi kusa don saduwa da ma’aikacin lafiya idan mutum ya fara jin alamun ta da aka zayyyana a sama.

Hadurran dake tattare da wanda ya kamu da ita: Babban hatsarin shi ne, Hantar wanda ya kamu da cutar ta hanata, zata iya lalacewa ta yanda dole sai dai ayinmasa dashen wata idan kuma da tsautsayi ya gitta, zai iya mutuwa.

Yadda ake kare jiki daga kanuwa da cutar:

Ana iya kare ta hanyar yin allurar rigakafi, inda kuma akwai magknin da ake cewa Hepatitis Baccine wata allurar ta. Ana kuma yiwa mutum ne da zarar an haifeshi, inda kuma a sati na shida dana goma dana goma sha hudu da haihuwar Jariri, inda za a yi allurar a dunkule. Ana kuma son a dinga kula da gyran muhalli,.musamman don kaucewa daga kamuwa da cutar ta hanta.

Source: Leadership A Yau