Karin Maganar Hausa: Nazarin Salo
Laraba, 20 Faburairu, 2019
Karin Maganar Hausa: Nazarin Salo

Cairo University

Faculty of African Postgraduate Studies

Department of African Languages

 

 

Karin Maganar Hausa: Nazarin Salo

الأ مثال الهوساوية: دراسة أسلوبیة

 

By

Mustapha Abubakar Sadik

B.A (Ed.); M.A; PGDM; M.B.A; CCAA

A Thesis in the Department Of African Languages

Faculty of African Postgraduate Studies

Cairo University

Submitted to the School of Postgraduate Studies

In Partial Fulfillment of the Rekuirements

For the Award of the degree of

DOCTOR of PHILOSOPHY (PhD) IN HAUSA LITERATURE

Of The UNIVERSITY Of CAIRO

 

 

UNDER TH SUPERVISION OF:

Prof. (Dr.) Muhammad Ali Noufal       Prof. (Dr.) Sabry Mohammed Hassan

Dean, Department of African Languages,

Faculty of African Postgraduate Studies, Faculty of African Postgraduate Studies,

Cairo University, Egypt. Cairo University, Egypt.

December 2018

 

BABI NA DAYA

GABATARWA

Wannan bincike ya shafi bayanin karin maganar Hausa, ta fuskar salon amfani daita. Haka kuma binciken yana karkashin adabin Hausa, saboda haka bari mu dankalli ma’anarsa.

Manna (1981:254) ya bayyana kalmar “adabi,” da cewa kalmar suna ce da ke da haruffa uku kamar haka- adb mai ma’anar ‘ladabi’ ko ‘abubuwan da suka kunshi ilimin zantukan hikimar dan’adam.” Idan kuma aka fadada ma’anarta zuwa kamar haka- adiib. Tana nufin ‘masani’ ko ‘mai ilimin zantukan hikimar dan’adam.’ Alfakhuriy (1971:7) ya bayyana ma’anar “adabi” tun asalinta tana nufin, 0talaawiinul kaul wato ‘jujjuya magana’ ko ‘sarrafa harshe’. Ya ce da haka ne kalmar ta sami yaduwar ma’ana zuwa, ‘kawata zance’ da kuma ‘tarin labaran da aka rubuta da salailai masu armashi. Dangambo (2008) ya ce adabi shi ne, “zantukan da suka kunshi fusaha ko suke bayyana nau’o’in azanci a fanonin rayuwa iri daban-daban domin koya wani darasi ga al’umma, watau cikin furuci ko a rubuce. Adabi nau’o’in azanci ne ko fusahohin sarrafa harshe na al’umma. Hoton rayuwar al’umma ne wanda yake nuna fusahohinsu da kwarewarsu da cigaban da suka samu wajen iya sarrafa harshensu da ma rayuwarsu gaba daya.” Wannan ma’anar ma an kalli adabi ta fuskar rayuwar al’umma wajen furta maganganun hikimar dan’adam a gargajiyance, wanda karin magana tana ciki. Ya bayyana adabin Hausa shi ne, “ilimin nau’o’in azanci da fusaha na sarrafa harshe da ya kunshi kirkirarrun fusahohin magana cikin tsarin wakoki da labarai da tatsuniyoyi da tarihihi da hikimomin iya sarrafa harshe irin su karin magana da kacici-kacici da barkwanci da karangiya da dai sauransu.”

Junaid da ‘Yar’aduwa (2007:66) sun kalli adabi a matsayin “wata hanya ce ta musamman wadda mutum yake bi don sadar da abubuwan da suka shafi rayuwarsa da ta ‘yan'uwansa. Abubuwa da yakan sadar din kuwa mafi yawansu abubuwa ne da suka dadada masa rai, watau na annashuwa, ko suka munana masa zuciya don nuna bakin cikinsa da kin abin; watau a takaice dai adabi yana nufin rayuwar dan’adam dukkanninta.”

Yahaya da Dangambo (1986:99) sun ba da ma’anar adabi da cewa wani “madubi ne na rayuwar al’umma da ta kunshi al’adunsu da dabi’unsu da harshensu da nishadinsu da abincinsu da tufafinsu da makwancinsu da tunaninsu da ra’ayoyinsu da huldodinsu da dai sauran abubuwan da suka shafi dabarun zaman duniya don cigaba da rayuwa. Kamar yadda kowace al’umma a duniya ke da hanyoyin adana tarihi da sauran bayanai da suka shafe ta, haka su ma Hausawa ke da nasu irin hanyoyin na gargajiya don adana nasu tarihin.

Allah Ya halicci dan’adam sannan ya sanya masa harshe don ya yi amfani da shi wajen isar da sako a tsakanin 'yan'uwansa ko jama'arsa a kan wani abu da ke damunsa ko yake ba shi mamaki ko kuma sha'awa a rayuwarsa da sauransu. Wannan ne ya sa yake amfani da harshe don bayyana tunaninsa ko ra'ayinsa, ko mu'amula da sauran al'umma kamar wajen murna ko jaje ko kuma neman taimako, tare da nuna wani yanayi da ya shiga a halin rayuwar yau da kullum. Duk da haka, a cikin irin wadannan zantuttuka ne yake furtawa ko rubuta wasu batutuwa na fasaha da azanci da kuma zalaka ko hikima da ban sha'awa; da kuma koyar da wani darasi na halin rayuwa. Harshen Hausa ma ba a bar shi a baya ba wajen tsarinsa da muhimmancinsa da kuma yin amfani da shi don abubuwan da aka zayyana a sama. Wadannan abubuwa su ne suka tattaru suka samar da adabin al'umma da ke kunshe da irin halin rayuwarta. Saboda haka, kowace al'umma tana da irin adabinta da take aiwatarwa tare da yadda take takama da shi, don shi ne madubinta. Haka kuma, ta kasance tana yada shi, don shi ne madubin rayuwarta. Duk da haka, tana kuma bunkasa shi kamar yadda ya dace ya kuma kamata, don shi ne tafarkin cigabanta a gargajiyance da kuma a zamanance.

Thompson, (1946), ya bayyana adabin baka da cewa zantuka ne na gargajiya da suka hada da tatuniyoyi, da labaran da suke a baka, wadanda ake yadawa tsakanin al'uma tun kaka da kakanni. Kirk-Green (1966), cewa ya yi adabin baka na Hausa tamkar rumbu ne da za a iya samun damman bayanai da zu taimaka wajen fahimtar al'adu da dabi'un al'umar Hausawa. Ya kuma kara da cewa, adabin baka na Hausa na zama a matsayin hanyar ilmantarwa, da wayar da kai da kuma canza dabi'un al'uma.

Hiskett (1969), ya bayyana adabin baka na Hausa dacewa, cike yake da dukkan nau'o'in hikima da za a iya sa mu a kowane harshe na duniya, kamar irin harsunan India a Sikandibeniya da Amurka da Ireland da sauransu. Haka kuma ya kara da cewa akwai wasu nau'o'in adabin Hausa da za a iya gano asalinsu, kamar guntattakin labaran hikima na Larabawa (kissa da hikya) da suka yi tasiri ga adabin Hausa.

Harhsen Hausa, harshe ne wanda AllahYa wadata shi da kalmomi wadanda za a iya sarrafa su a yi magana cikin azanci kuma a isar da kowane irin sako ake son gabatarwa kai tsaye, ko a sakaye, ko kuma a kaikaice, gwargwadon bukatar mai magana. Saboda haka harshen yana kunshe da hanyoyin magana cikin azanci da yawa.

Hausawa tun fil azal na adana labaru na wadansu abubuwan da suka wakana a da, a cikin sigar wakoki da tatsuniyoyi, da karin magana da sauran zantukan hikima. Karin maganar Hausa na taka rawa wajen adana tarihi da sauran muhimman

bayanai na Hausawa don gudun bacewa. Bacewar wadannan bayanai tamkar share tarihin al’umma ne daga doron kasa. Haka kuma, tana bayyana nasarorin da magabata daga cikin al’umma suke samu, da ruwaito yadda magabatan suka yi rayuwarsu don na baya su yi koyi da su. Hakanan karin magana na taimakawa wajen bayyana tsarin zaman al’umma da zayyana tasawirarta da rarrabe sassanta musamman bangaren siyasa da tattalin arziki da zaman tare da sauransu.

Sanin abubuwan da suka wanzu ko suka wakana a baya, suke taimakawa a fahimci abin da ke faruwa a yanzu, kuma su agaza wajen yin has ashen abubuwan da za su faru a gaba. Ba Hausawa kadai ke amfani da karin magana ba, a iya cewa ba wata al’ummar da ba ta da irin nata zantukan hikima.Wannan ne ya sa wasu ke ganin karin magana a matsayin gado da ya hade dukkan mutanen duniya a waje guda, ba tare da la’akari da bambancin kabila, ko jinsi, ko bangare da aka fito ba. Don haka, karin Magana wani babban rukuni ne a adabin bakan Hausa.

1.1 Hausa

kalma ce da masana da yawa suka yi bayani a kanta. Wasu suna da ra'ayin cewa asalainta ya samu ne daga zuwan Bayajida Daura. Sun ce a lokacin da ya zo, ya zo ne a kan doki wanda a lokacin mutanen Daura ba su taba ganin irin wannan dabba ba, saboda haka sai suka alakantata da 'Sa' wanda shi sukke da shi. To sai suka alkantashi da hawan sa, watau ya hau sa wanda daga baya aka hada kalmomin guda biyu suka ba da hausa. Wasu sun yarda da wannan zance, wasu kuma da yawa ba su yardaba.

Danmasanin Kano (1991) kuwa, cewa ya yi asalin kalmar daga Habasha ne. Watau kalmar ce aka rika juyawa ta koma habsha daga baya aka kara juyata ta koma hausa. Bayanai dai kan wannan al'amari na kalmar Hausa abu ne mai fadi, mai girma, wanda masana tarihi suke ta magana a kansa.

Hausawa mutane ne da suke zaune a kasar Hausa, kuma suke magana da harshen Hausa. Wasu na amfani da tarihin asalin mutum wajen gano ko Bahaushe ne, wasu kuma da al’adun zamantakewar Bahaushe suke amfani. Wasu kuma na amfani da harshe tare da addini. Bin al’adun Hausawa kai tsaye wajen saka tufafi da bin

addinin Musulunci da yin Hausa babu gargada kan sa a dauka cewa, mutum Bahaushe ne. Haka kuma, asalin mutum kan saka shi cikin kabilar Hausawa. Rashin tabbas ya haifar da ijitihadin masana daban-daban a kan asalin Kalmar Hausa da Hausawa. Da aka tambayi sarkin Ningi Alhaji Haruna cewa ya yi ‘yar tsohuwa Ayyana ce ta fara furta kalmar”hausa”a lokacin da take bayanin bakonta da ya kashe macijiya a rijiyar kusugu.Shi kuwa Niben (1971), cewa yake asalin kalmar ‘Hausa’daga Buzaye take. Wai ya ce haka nan Buzaye ke kiran mutanen da suke zaune a Arewacin kogin Kwara. Malam Aminu Kano kuwa cewa yake asalin kalmar daga ‘Habasha’ne ta koma ‘Habsha’daga bisani kuma ta koma ‘Hausa’.

Kenan ra’ayinsu ya zo daidai da na Alh. Yusuf Maitama Sule kamar yadda aka yi bayani a sama. Amma shi masanin harshe Skinner (1968-p25), cewa ya yi Kalmar Hausa daga mutanen Songhai ne domin su suke kiran mazauna kauyukan gabas da su ‘Aussa’, daga nan kalmar ta koma ‘Hausa’.

Ita kuwa kalmar ‘Hausawa’, akwai ra’ayoyi daban-daban na masana da suke kokarin bayyana asalinta.

Ibrahim (1982 p.2-4), ya bayyana asalin Hausawa mutane ne barbarar yanyawa da aka samar tsakanin mutanen da suka rika yiwo kaura daga tsakiyar kasar Asiya,zuwa yamma a sakamakon wani tunzuri da ya auku a can,da kuma bakar fata mazauna kasar Sudan na asali.

Shi kuwa masanin harsuna Greenberg (a Amina A, 2000 p8-9), kokari ya yi na lalubo asalin Hausawa ta hanyar kwatanta harshe da harshe don nemo alaka tsakanin harsuna mazauna gefen kogin Chadi shekaru da dama kafin haihuwar Annabi Isah Alaihis-salam. An ce bayan da tafkin ya rika kafewa ne mutane suka rika kaura suka bazu ko’ina. A bisa kiyasinsa Hausa ta fada a karkashin gungun harsunan Chadi wanda shi kuma ya samo asali daga harshen Afro-Asiatic. Da wannan ne Greenberg yake ganin asalin Hausawa daga Chadi ne, domin harshensu yana da alaka da sauran harsunan Chadic din, kamar dai yadda bayani ya gabata. Shi kuwa masanin tarihi Smith (1997), na ganin shirinkita ce kawai za a yi idan aka ce wai ga yadda al’ummar Hausawa ta kafu a mazauninta na yau. Shi a ra’ayinsa Hausawa ne al’ummar asali mazauna kasar Hausa tun ma kafin zuwan Bayajida a garin Daura. Amma Adamu (1995), cewa yake Hausawa kalmar da mutanen kasar ke kiran kansu da ita ne.Hausa kalma ce ta harshen da Hausawa ke magana da shi. Ma’ana a ra’ayin Adamu, Bahaushe shi ne wanda yake magana da harshen Hausa a matsayin harshen uwa;sannan a same shi yana zaune a kasar Hausa kaka da kakanni;kuma a same shi ya tasirantu da dabi’u da al’adun zamantakewa da suka dace da addinin Musulunci.

Kasar Hausa na cikin shiyyar Sudan ta tsakiya. Tana nan shimfide a shiyyar arewacin Tarayyar Nijeriya da kuma bangaren kudancin jamhuriyar Nijar.Ta yi iyaka da kasashen Borno daga gabas, daga yamma kuma ta yi iyaka da Jamhuriyar Benin, daga arewa kuwa ta yi iyaka da Agadas cikin jamhuriyar Nijar. Kasar Hausa ta kunshi kasashen Daura da Katsina da Gobir da Zazzau da Rano da Biram da Gobir duk a cikin Tarayyar Nijeriya. Daga jamhuriyar Nijar kuma, kasar Hausa ta malala har kasashen Maradi da Tasawa da Kwanni.

 

1.2 Dalilin Bincike

An dade ana gudanar da bincike kan adabin Hausa kama tun daga 'yan kasa har zuwa baki wadanda kuma suka ba da haske a kan irin ayyukan hikima da azanci masu nuna irin halin rayuwar yau da kullum da ke gudana a cikin al'ummar Hausawa, musamman a kan fannonin adabin Hausa daban-daban. Amma akwai karanci rubuce-rubuce kwrai a kan nazarin salon Karin maganar Hausa. Saboda haka, dalilan wannan bincike sun hada da:

- Yin bincike a kan harshe wanda ya shafi adabi, watau salon karin magana. Kamar yadda Archibald Hill1 ya ce, 'wani bangaren adabi ya shafi harshe, saboda haka za a iya bincike a kansa kamar yadda ake bincike dukkan wani abu da ya shafi harshe'. Ya kara bayani da cewa karin magana wani bangare ne na adabi wanda ya shafi salon amfani da harshe.

Asabe (2002) na da ra'ayin cewa karin maganar Hausa ya danganci yanayi, hali da kuma dalilin da ya sa aka yi karin maganar. Ana iya yin amfani da karin Magana guda daya a kan yanayi biyu mabambanta. Misali idan muka dubi wannan Karin maganar: / ʔa ri-ka sa:-ra: ʔa-na: du:-bab ba:-kin ga:-ta-ri/ 'When you are digging, be sure of where your ade is digging' (36), ana iya aiwatar da ita ga wani mai almubazzaranci da kudin Gwamnati. Haka kuma ana iya fadarta ga wanda ya kyale 'ya'yansa suna yin abinda suka ga dama.

Haka kuma a iya amfani da karin magana biyu a kan yanayi ko abu guda daya. Misali, / ʔa yi wad-da za: ʔa yi, be:-ra: ya: zu-bad da ga:-rin kyan-wa /'Do whateber you can do' (51) da kuma / ʔa yi wad-da za: ʔa yi, ra:-mam-me: ya: za:-gi ma:-ye / 'Do whateber you can do; a skinny person abuses a human killer' (52), ana iya amfani da su a kan yanayi guda kuma duk su shiga. Haka ma yake a wadannan karin maganar guda biyu: / ʔa-na: ce:-we: ru-wa: ya: ci ma-ka-di:, ka-na: ce:-wa:

gan-ga: ta: ji-ke / 'They are saying that the musician has fallen into the water, but you are saying his drum is wet' (127) da / ʔa-na: ra-ba: ka da ki:-won ʔa-wa:-ki:, ka-na: kyal-la ta: hai-hu / 'They are keeping you away from feeding the goats; you are saying white goat has delibered' (132). Yana da muhimmanci a yi nazarin ireiren wadannan furuci, saboda abubuwa ne da ke farawa cikin al'umma yau da kullum. Edgar3 ya yi bayanin cewa karin magana na taka rawa wajen saukaka zance. Tana ba mutum damar bayyana ra'ayinsa a cikin kalmomi 'yan kadan, wanda hakan na cikin dalilan da suka sa ya zama wajibi a yi nazarin karin magana.

- Gano salalen da a ke iya amfani da karin maganar Hausa.

- Fitowa da azanci da fasahar Hausawa cikin harshensu.

- Domin adana karin maganar Hausa.

- Bunkasa adabin Hausa da kuma adana shi.

-A fayyace duk wasu hanyoyin da Hausawa ke bi domin tsara da gabatar da Karin maganarsu.

-A ilimantar da Hausawa da wadanda ba Hausawa ba duk wasu hanyoyin da Hausawa ke bi su gina karin maganarsu  tantance wa jama'a salo, sigogi da yanaye-yanayen karin maganar Hausa.

-A fayyace wa jama'a ma'anoni da sakonnin da ke kunshe a cikin karin magana.

- Haka kuma an aiwatar da wannan bincike domin cika sharadin samun shaidar digiri na uku Ph.D) a fannin adabin Hausa a Cibiyar Nazari da Bincike ta Africa, Jami'ar Alkahira (Institute of African Research and Studies, Cairo University).

 

1.3 Ma'ana da Asalin Karin Magana

 

Karin magana dai tana daya daga cikin maganganun azanci na Hausa. To

don haka tana cikin adabin baka. Wushishi (1998:102), ta fassara karin magana da cewa "wata tsararriyar magana ce wadda take a gajarce, wadda take bayar da ma'ana gamsasshiya mai fadi da yalwa musamman idan aka tsaya aka yi bayani daki-daki.

A ganin Dangambo, (1984:38) kuwa, "Karin magana dabara ce ta dunkule magana mai yawa a cikin zance ko 'yan kalmomi kadan cikin hikima". A ra'ayin Umar, (1980), "karin magana wani irin shiryayyen zance ne da Hausawa kan yi, ta dabara da hikima, su yi magana cikin magana a takaice.

Sau da yawa, karin magana a Hausa, dunkulalliyar jimlace 'yar kil, mai

sassa biyu da ta kunshi zunzurutun ma'ana a lokacin da aka yi bayani".

 

Shi kuwa Yunusa (1989), cewa ya yi, “Karin magana zance ne dogo a

dunkule wuri daya”. Ita kuwa Koko (2011), cewa ta yi, “Ana iya kiran Karin magana da wani salo na baje kolin tunani da Bahaushe kan yi ta hanyar hikima cikin ‘yan kalmomi kadan.

Shi kuwa Umar (1987), ya kira karin magana da cewa ‘wata dunkulalliyar jumla ce ‘yar kil mai sassa biyu da ta kunshi zunzurutun ma’ana idan aka yi bayani’. Ita kuwa Koko (1989) cewa ta yi Karin magana, magana ce gajeriya amma bayani mai tsawo.Furniss (1996:70), cewaya yi karin magana na nufin ‘boyayyen zance’.

Zaruk da Alhassan (1982) sun bayyana ma'anar karin magana da cewa, nazari ne na rayuwa a dunkule, cikin gajerun maganganu da misalai irin na hikima. Yahaya da Dangambo (1986) a wani kaulin, sun fassara karin magana a matsayin daya daga cikin nau'o'in zantukan hikima na Hausa, kum sun bayyana cewa kowa na amfani da ita, maza da mata, yara da manya cikin zantukan yau da kullum.

Furniss (1996), ya bayyana cewa karin magana na daya daga cikin zantukan hikima wadda take kunshe da boyayyar ma'ana, wadda sai mai sauraro ya nemi fassararta. Yakubu (2007) kuwa ya ce karin magana wata gajeriyar jumla ce ta hikima, wadda ta kunshi ma'ana mai yawa idan za a a yi bayaninta. Knappert (1997) kuwa, ya bayyana karin magana da cewa yanki ne na tunanin al'uma da aka dunkule cikin kyakkyawan zance. Manufar karin magana ita ce domin ta koya wa mutane hikima cikin kayataccen bayani. Ya kara da cewa karin magana dadaddiyar taska ce da ta dade tana taskace tunanin al'uma, wadanda wasu mutane masu hikima suka kirkira domin bayyana halin da al'umar take ciki. Birnuwa (2005), ya bayyana karin magana a matsayin gajeruwar jumla da ke sakaya ma'ana, wadda idan aka warware ta sai ta bayar da ma'ana mai tsawo, wadda mafi yawan kalmomin da ke cikinta ba su kunsa ba, sai dai suna da dangantaka da ita. Amma Isma'il da 'Yar'aduwa (2007), sun bayyana ma'anar karin magana da cewa wata 'yar jumla ce gajeriya da mai magana zai fada ta hikima, kuma ta kunshi ma'ana mai yawa idan an tashi yin sharhinta. Karin magana dai idan za a dauki kalmominta a fitar da ma'anarsu filla-filla a hakikar gaskiya ko kadan ba za su ba da ma'anar da mai magana ke nufi ba, ko kuma ma'anar da ita karin maganar ta kunsa ba.

Hassan (2009), ya bayyana ma'anar karin magana da cewa, wata 'yar magana ce cikin guntuwar jumla da take kunshe da zunzurutun ma'ana in aka yi mata sharhi. Irin wadannan maganganu dauke suke da hikima da falsafa ta rayuwa a dunkule.

Ina ganin kuma a iya cewa karin magana ma'ana ce ta wani zance mai fadi ake dunkulewa waje guda ta hanyar amfani da azanci, a inda ‘Kari’ ke nufin lankwasa ko karya abu, yayin da magana ita ce zance. Don haka karin magana shi ne karya magana domin a gajarta bayaninta wanda ke tattare da hikima mai yawa idan aka cigaba da fadada ma’ana. Kuma wani kundi ne da ya taskace tunanin al'uma wanda za a iya nazarin tunanin al'uma wanda za a iya amfani da shi a fagen nazari ta fuskoki da dama, kamar nazarin tunanin al'uma, fasaha da kuma al'adunsu. Azima (2011) ta yi karin bayani a kan ma'anar karin magana da Zarruk da Wasu

(1986) suka bayar cewa 'karin magana gajeren zance ne wanda yake kunshe da hikima'. Sai ta bayyana cewa idan aka yi la'akari da wannan bayani na su, Karin magana ta kunshi habaici, saboda shima gajeren zance ne wanda ke kunshe da hikima. Bayan haka ta kawo ma'anar habaici da muhallan yinsa da jigoginsa da salon da ke cikinsa da kuma yinsa. Ta bayyana cewa ana habaici a karin magana,

don haka ma ta kawo ra'ayoyin masana dangane da karin magana tare da tabbatar da cewa habaici na iya zama karin magana saboda ana amfani da karin magana ne wajen yinsa.

Yahya da wasu (1992), ya yi bayanin cewa masana sun aminta da cewa Karin magana na da tsari na musamman, wato na gutsure zance da ake wadda alama ce ta azanci. Kuma ya kara da cewa masana da dama na da ra'ayin cewa karin magana

yankin magana ce da ke kunshe da balagar harshe, kuma take isar da wani sako.

Amin (2000), ya tattauna ra'ayoyin masana dangane da fahimtarsu game da Karin magana musamman abin da ya shafi ma'ana da tsarin karin magana. Marubucin ya yi na'am da kokarin masana irin su Shimkim da Pedros (1953) da Rymond (1954) da Tshimpaka (1977) da Powe (1981) da Dundes (1994) da sauransu, wadanda suka tabbatar da cewa nazarin karin magana da kwankwance ta yana bukatar kula da zurfin tunani. Shi kuwa sai yakara da cewa kwankwance karin Magana na bukatar sanin al'adun al'umar da ke da karin maganar. Ya kara da cewa sanin ma'anar karin magana kadai ba zai wadatar ba wajen sharhin karin magana, mai

nazari na bukatar sanin al'adun al'uma. Mrubucin ya kafa hujja da aikin Powe (1981), wanda ya yi sharhin karin magana ta la'akari da ma'anarta, ya nuna kasawar Powe (1981) na rashin la'akari da al'adun Hausawa wajen sharhin Karin magana, domina cewarsa za a iya samun karin magana ta dauki ma'anoni da dama. Karin magana kusan ya mamaye kowane fanni na rayuwar Bahaushe. Yana da

wuyar gaske a ce ga sha’anin rayuwar da ba a samun karin magana, kuma wannan shi ya bada damar kamar yadda harshe da al’ada kan sauya su bi zamani, to kwatankwacin haka karin magana ke sauyawa.

Karin maganganu sun fito daga cikin rayuwar al'uma, shi ya sa suka kunshi yawancin abubuwan da suka shafi bangarorin rayuwar al'umma.

Yana da wuya a ce ga mutumin da ya kago karin magana, a lokaci kaza, ko a wuri kaza, ko kuma saboda dalili kaza. Amma a iya cewa naso ne na al'adu da dabi'un Hausawa ya samar da karin magana. Sauye-sauyen zamani da shudewar al'umma ke sa juyawar karin magana ta hanyar mantawa da wasu ko kirkiro wasu sababbi.

Ke nan karin magana ya samo asali ne tun lokacin da dan Adam ya kirkiri fasahar mayar da zance mai tsawo ya zuwa gajere. Babu wani takamaiman lokaci da aka kebe cewa nan aka fara, sai dai babbar hikimar da ke tattare da wannan shi ne Karin magana ya ratsa kowane fanni na rayuwar Bahaushe. Ana iya fahimtar rayuwa ta karin magana, kuma kamar yadda harshe ba ya gajiya da karbar sababbin abubuwa,

Salo

Akwai ra'ayoyi da dama dangane da salon karin magana, Godiya (2014) na ganin salo bangare ne na ilimin nazarin harshe. Amma wasu na ganin cewa nazarin salo bai kai a ce za a kwatanta darajarsa da ta ilimin nazarin harshe ba, sai dai a ce shi nazarin salo yana karkashin ilimin harshe ne. Abraham (1962) ya bayyana salo da cewa ana iya kallonsa ta hanyoyin daban-daban. Akwai salo da yake nufin kirkiro hanyar yin wani abu ko yanayin wani abu. Akwai kuma mai ma'anar dabara ko fasaha ko wayo ko hazikanci, ko gwaninta.

Bayero (2001) ya yi bayanin cewa, salo na nufin duk wata dabara ko hanya wadda aka bi domin isar da sako. Dabara ce ko hanya mai yin kwalliya ga abu domin abin ya kwarzanta ko ya bayyana. 'Yar'aduwa (2007) kuwa, ya fassara salo da hanyoyin da marubuci ya bi wajen isar da sako ta yin amfani da harshe. Ayuba (2014) na ganin salo wani kyalekyakle ne da marubuta kan yi don fito da ma'anar abin da suke son bayyanawa jama'a. Salo wata dabara ce da ake yi wa harshe ado da ita,

kuma hanya ce ta sarrafa harshe, a jujjuya shi ta yadda za a iya takaita manufa ko a sakaya ma'ana ko a kaifafa tunani. Dabara ce ga abu domin abin ya kwarzanta ko ya bayyana. Gargaliya Wannan harshe ne da ake amfani da shi wanda ya saba ka'idar harshen asali.

Kowane yare yana da tasa irin gargaliyar, haka kuma a tsakanin mutane masu gargaliya iri daya ana samu wasu bambance-bambance wajen furuci. Furucin gargaliya ba a karbarsa a rubuce, saboda ya karya ka'idar rubutu. Karin maganar da na yi amfani da su wajen wannan bincike sun karya ka'idar rubutun Hausa, saboda na rubutasu daidai yadda nike furucina na yauda kullum. Malamai da dalibai manazarta da yawa sun gudanar da bincike da rubuce-rubuce da dama a kan Hausawa da al’adunsu. An gudanar da bincike daban-daban a kan adabi da harshe da kuma al’adun Hausawa tare da nuna muhimmancinsu ga rayuwar al’umma da bazuwar su da kuma tasirinsu ta fuskar cudanyarsu da bakin al’adu ciki da wajen kasar Hausa. A wannan babi an dubi kundayen bincike daga digiri na uku da na biyu har ma da na farko. Haka kuma an yi nazarin littattafai da mukalu tare da mujallu daban-daban da suke da nasaba dakarin Magana Masana sun yi rubuce-rubuce a lokutta daban-daban da kuma wurare daban-daban a kan abin da ya shafi azancin magana. A nan,an duba ayyukan da wasu marubuta suka yi wadanda suke da alaka da karin maganar Hausa. Bala (1982) ya yi aiki mai taken “Karin magana”. Ya karkasa aikin nasa zuwa babi biyar. A babi na farko an yi tsokaci a kan ma’anar adabi da kuma karin magana, sai

babi na biyu wanda aka fayyace jigogin karin magana da suka hada da shagube ga mutane da dabbobi da ciwo da magani da abubuwan da suka yi kama da hakan. A babi na uku kuwa, tasirin karin magana neaka bayani a kaii,a babi na hudu kuwa aka zo da salon sarrafa harshe a cikin karin magana. Daga karshe, wato a babi na biyar ya kawo wadanda suka fi amfani da karin magana kamar mata da maroka da karuwai da malamai da sauran su.

Koko (1989), ta yi rubutu ne mai taken “Karin magana a hannun mata a garin Sokoto”, an karkasa aikin zuwa babi hudu. Na farko tarihi ne da bayanin kewayen Sokoto. Na biyu kuwa aka fadi ma’anar karin magana da rabe-rabenta. Sai a babi na uku inda aka zo da jerin wasu karin maganganu tare da bayaninsu, a babi na hudu kuwa, aka zo da jerin wadansu karin maganganu zalla fiye da guda dari. Bugaje (2014) ta gabatar da kundin bincikenta domin neman digiri na uku mai take‘Karin Magana Mahanga Tunani: Nazarin Lokaci A Hausa’. Ta yi nazari a kan

dangantakar da ke tsakanin karin magana da falsafa ko tunanin Hausawa game da lokaci. Ta tattaro karin magana musamman wadanda suka shafi lokaci, sa’annan ta yi bayanin ma’anoninsu tare da tunanin da ke kunshe a cikinsu. A karshe ta raba su ya zuwa ajin lokuttan Hausa. Ta kawo misalan karin maganganu, ta kuma yi bayaninsu, sannan ta nuna muhallin da ake amfani da su da kuma alakar Karin maganganun da lokaci.

Yahya, (1979) ya bayyana tasirin adabin baka ga rayuwar Hausawa tun daga kuruciya har zuwa girma. Ya bayyana cewa adabin baka ya kunshi fasaha ta zahiri ta al'uma. Ya kuma yi tsokaci kan nauo'in adabin baka da suka hada da tatsuniya, da karin magana, wadda kanta nake bincike, da wasa kwakwalwa, da hikayar mafari da tarihihi da sauransu, a inda ya kawo ra'ayoyin masana kan abin da ya shafi matsayinsu a adabin baka.

Bada, (1995) a bincikensa na digiri na uku mai suna,‘Literary Studies of Themes Functions and Poetic Debices of Hausa Karin Magana’. Ya kawo jigogin Karin magana da suka hada da yabo da godiya da girmamawa da ilimantarwa da addini da son gaskiya da sauransu. Ya kuma yi kokarin kawo tasirin karin magana a rayuwar Hausawa wadanda suka hada da nishadi da addini da raya harshe da adon harshe da dai sauransu. Sannan ya rufe aikin nasa da hikimomi da salailai da suka jibanci karin magana. Garba (1982) a kundin digiri na biyu a Jami'ar Bayero Kano mai taken 'A linguistic analysis of Hausa karin magana' ya yi tsokaci a kan karin maganganun Hausa da ake samu a harshen Hausa. Ya bayyana ma'anar karin magana da rabe-rabenta tare da misalai.

Garba (1998) a nazarin da ta yi na digiri na biyu a Sashen Nazarin Harsunan

Nijeriya da Afirika, Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, mai suna “Nazarin Jinsi A Adabi: Tsokaci Kan Matsayin Mace A Rubutattun Wasannin Kwaikwayo na Hausa,” ta kawo munanan halayen mata a inda ta kawo misalan wasu daga cikin

karin maganganun Hausa da ke nuna wasu munanan halaye irin su kishi da gulma da zuwa wajen bokaye.

Bilal (2005) a cikin aikinsa na digiri na biyu mai taken, 'Kwatanta Karin Maganar Larabcin Libya Da Na Hausa," a babi na daya, ya yi kokarin fito da ma'anar kalmar Hausa da bayanin yanayin kasar Hausa da asalin Hausawa da harshensu, da

kuma dangantakar Hausawa da Larabawan Libiya. Haka kuma, a babi na hudu ya bayyana ma'anar karin magana da kawo rabe-rabenta da bunkasarta da kuma dangantakarta da Larabawa da Turawa. Binciken ya bayyana muhimmancin Karin magana da hikimar da ke cikin ta a lafazance ko a cikin waka. A babi na shida, ya kwatanta karin maganar Hausa da ta Larabci ta la'akari da kamanninsu da

bambance-bambancensu. Bayan haka, a cikin aikinsa da ya kwatanta Karin maganar Hausawa da ta Larabawan Libiya, ya gane cewa karin magana wani bangare ne na adabin baka na Hausa da ke kunshe da al'adu da dabi'u da falsafar rayuwar kowace al'umma a duniya- musamman Hausawa da Larabawa.

Asabe (2003) ta gabatar da kundin digiri na uku a Sashen Koyar da Harsunan Turai, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, mai suna “Women in Hausa Folklore.” Kodayake wannan aikin nata ba a kan karin magana ta yi shi ba, amma ta kawo wani babi na musamman kan karin magana da ke bayani kan mata, iyaye mata, da matan aure da kishi da dai sauransu.

Asabe da Bala (2012) sun nazarci karin maganar Hausa masu dauke da sakon ban dariya. Da farko sun fara da bitar ma'anar karin magana inda suka kawo ra'ayoyin masana daban-daban dangane da ma'anar karin magana, daga ciki har da ma'anar da Wolfgang (2004) ya bayar, wadda ita ce ma'anar da marubutan suka yi na'am da ita, wadda ya ce karin magana gajeren zance ne na al'uma wanda ya kunshi hikima da gaskiya da tausayi da tunanin al'uma a cikin tsari na musamman wanda aka gada kaka da kakanni. Haka kuma marubutan sun kawo karin magana masu ban dariya da sa nishadi tare da bayaninsu. Haka kuma, sun bayyana hikimar da ke cikin ire-iren wadannan karin maganar.

Masana irin su Shipley (1955), da Mieda (1993), da Knappert (1997), da sauransu sun bayyana cewa karin magana na zuwa da kwalliya wadda nau'i ce ta salon sarrafa harshe, kuma tana daya daga cikin abubuwan da ke fayyace fasahar harshe.

Haka kuma akan yi amfani da kwalliya a cikin karin magana domin bayyana kamanci na abubuwa biyu ko fiye, ko kuma domin sakaya ma'ana.

Shi kuwa Ringim (1973), ya yi tsokaci ne kan ‘muhallin karin magana a cikin al’umma’. Ya karkasa aikin nasa a cikin babi guda hudu. A babi na farko ya kawo ma’anar karin magana, babi na biyu labarun da ke dauke da su, babi na uku bayani ne na yadda karin magana ta shafi al’adun Hausawa, a yayin da a babi na karshe aka zo da karin maganganu da aka gina labaru da su.

Nahuce (2008) a kundinsa na neman digirin na biyu mai take‘Karin Maganar Hausa A Rubuce’. Ya yi cikakken bayani dangane da samuwar karin maganar Hausa da rabe-rabenta da tasirinta ga rayuwa Hausawa da wuraren da ake yin su.

Daga karshe ya kawo ratayen karin maganganu da dama da suka shafi rayuwar Hausawa, ta amfani da tsarin abcd.

Calbin (1982) a kundin digirinsa na biyu da ya gabatar mai sunan‘A Linguistic Analysis of Hausa karin magana’. Ya gudanar da bincike a kan karin maganganun Hausa, inda ya yi bayanin ma’anonin da suke dauke da su.

Balarabe (2012), a kundin digirinta na biyu da ta gabatar mai taken 'Karin Magana a Cikin Littattafan Adabin Kasuwar Kano na Mata'. Ta kasa aikin nata zuwa babi biyar. A babi na daya shimfida ce da tsokaci a kan ayyukan da suka gabata. A babi na biyu kuwa, sai ta yi bayanin adabin kasuwar Kano dangane da m'anarsa, samuwarsa, bunkasarsa da kuma jigoginsa. Amma a babi na uku, tarihin Bilkisu Ahmad Funtuwa ta bayar, dangane da littattafan da ta wallafa da kuma lambar girma da ta samu. Daga karshen babin kuma ta kawo tarihin Hafsatu Cindo Sodangi. A babi na hudu kuwa at yi tsokaci ne a kan karin maganar da ke cikin littattafan adabin kasuwar Kano na mata dangane da ire-iren karin maganar. A karshen aikin nata, watau a babi na biyar ta bayyana darussan da ke cikin Karin maganganun da ta fitar tare da kammalawa da kuma bayanin sakamakon bincike.

Alkali (1989) a kundin da ya gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Beyero Kano, na digiri na biyu, mai suna “Cudanyar Adabi: Tasirin Adabin Baka A Kan Rubutattun Wakokin Hausa”. Ya yi aikinsa a kan yadda adabin baka kan yi tasiri a kan rubutattu wakokin Hausa dangane da habaici da kirari da kuma karin

magana. Mode, (1998) a kudin bincikensa na neman digiri na biyu mai take‘The Use of

Proberbs in Modern Hausa Literature’, ya dubi karin maganganu ne na cikin rubutattun adabin Hausa, kuma ya nazarci yadda aka yi amfani da su a cikin wadansu kagaggun littattafan Hausa.

Shi kuwa Umar (1986) ya gabatar da aikinsa mai sunan “Guntattakin Zantukan Hikima”, a cikin babi biyar. Da farko ya fara da ma’ana, sai a babi na biyu ya zo da wadanda suka fi yin su, kamar malaman addini da gidajen watsa labarai da ‘yan kasuwa. A babi na uku kuwa, an zo da jigogin karin magana da suka hada da na zaman duniya da mu’amala da ilmi da sauran makamantansu. Shi kuwa babi na hudu, an bayyana tarihin samuwa da yaduwarsu ne.A babi na biyar kuwa aka kawo

muhimmancin karin magana ga al’umma baki daya.

Mode, (2005) a kundinsa na neman digiri na uku a Sashen Koyar da Harsunan Turai, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato mai suna “Stylistic Study of Hausa town’s kirari (Epithets)” a ciki ya yi nazari a kan kirarin da ake yi wa garuruwan Hausa, amma a cikin babi na biyu na aikinsa ya dubi yadda ake sarrafa Karin maganganu wajen yabon mutane, watau a yi masu kirari ta danganta su da wasu karin maganganun. Aikin nasa ya takaita ne kawai a kan kirari da Karin maganganun da ake amfani da su wajen kirari.

Bachaka kuwa (2005) a digirinta na farko mai suna “Karin Magana cikin Wakokin Sarauta: Nazari kan Wakokin Sani Aliyu Dandawo”. A cikin kundin ta yi kokarin fito da tarin karin maganganun da mawakin ke amfani da su a cikin wakokinsa na sarauta.

Balle, (2011) a kundin digirinsa na biyu da ya gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo mai suna, “Hikimomin zantukan Sarkin Musulmi Abubakar III (1938-1988). Ya karkata akalar bincikensa ne a kan kebabbun zantukan hikima na marigayi Sarkin Musulmi Abubakar na III. A karshe ya kawo zantukan hikima na Sarkin Musulmi guda talatin da biyar wadanda suke dauke da hikimomi na musamman wadanda tuni wasu suka rikide suka zama karin maganar Hausa Auwal (2008), a cikin aikinsa na digiri na farko mai taken 'Kaswanci a Ma'aunin Karin Magana', ya kawo ma'anar karin magana da rabe-rabenta, karin magana jiya da yau, da kuma muhimmancinta ga al'uma. Ya kuma yi bayanin karin magana mai alka da kudi da masu kudi; mai alka da kasuwa da 'yan kasuwa. Daga karshe sai ya kawo wadanda suka shafi kasuwa da 'yan kasuwa; ciniki da saye da syarwa; riba da kuma faduwa.

Abdulkadir da Yusuf (2008) sun gabatar da aikinsu mai taken ‘Dangantakar Harshe da Al’ada:

Nazari a Kan Karin Magana da Zamananci’. Sun kasa aikin zuwa babi biyar. A babi na daya gabatarwa ce da kuma ayyukan da suka gabata; babi na biyu an yi bayanin ma’anar harshe da kuma al’ada, da kuma dangantakar da ke tsakaninsu.

Babi na uku kuwa dukkansa yayi bayani ne a kan Karin Magana, musamman dangane da yadda zamani ke shafar Karin Magana. Kamar lokacin jahiliya, zuwan musulunci da kuma bayan zuwan Turawa.

Jibrin (1992), a digirin sa na farko mai taken 'Karin maganar magana jari ce da manufofinsu' Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, ya kasa aikin zuwa babi biyar. A babi na farko ya gabatar da ayyukan da suka gabata a kan abin da ya yi bincike. Babi na biyu kuwa, ya kawo takaitaccen tarihin Abubakar Imam ne. Amma a babi na uku

ya tattauna ne a kan krin maganar magana jari ce ta farko tare da yin tsokaci a kan manufofinsu. A babi na hudu marubucin ya yi tsokaci ne a karin maganar Magana jari ce ta biyu tare da manufofinsu. A babi na karshe, watau babi na biyar, sai ya yi bayanin karin maganar magana jari ce ta uku, ita ma tare da manufofinsu.

 

karin magana. Daga karshe a babi na biyar ta yi tsokaci a kan ma'abota Karin magana kamar yadda ta kirasu.

 

Godiya (2014), a bincikenta da ta gabatar a kan 'Kwatankwacin Karin Magana a Hausa da Ruruma', ta kasa aikin zuwa babi biyar. A babi na farko shimfida ce da ta

shafi tsari da kuma gudanar da bincike. Babi na biyu kuwa waiwaye ta yi a kan ayyukan da suka gabata. Babi na uku kuma shi ne jigon binciken, saboda tsokaci ne a kan kamancin karin magana a Hausa da Ruruma, tafuskar jigo, tsari da kuma salo. Babi na hudu kuwa jawabi ne a kan bambancin karin magana a Hausa da

Ruruma a kan dai wancan jigo, tsari da kuma salo. Ta nade aikinta tare da kawo shawarwari a babi na karshe, watau babi na biyar ke nan.

Dange (2011), ta gabatar da kundin digirinta na farko mai taken 'Tasirin Kishi a Karin Maganar Hausawa'. Ta kasa aikin nata zuwa babi biyar, a inda babi na daya ya kunshi mukaddima da bitar ayyukan da suka gabata. A babi na biyu ta kawo ma'anar karin magana da asalinta da kuma rabe-rabenta. A babi na uku kuwa, marubuciyar ta yi tsokaci ne a kan kishi. Ta yi bayanin ma'anar kishi, asalinsa da kuma rabe-rabensa. Ta yi bayani a kan kishi a karin maganar Hausa a babinta na hudu, wanda daga bisani ta fayyace tasirin kishi a karin maganar Hausa. Ta kammala aikinta a babi na biyar. Shehu (2012) ya gabatar da kundin digirinsa na farko, mai taken “Gurbin Sana’a a Ma’aunin Karin Magana”. Ya dubi sana’a ne a kan yadda takefitowa a Karin magana. Sai dai binciken nasa ya takaita a kan sana’a ne.

Shafa'atu (2012) a kundin digirinta na farko mai taken, 'Mutum da gabobinsa a karin maganar Hausa: Sharhi da nazari', ta kasa aikin zuwa babi biyar. A babi da daya shimfida ce da bitar ayyukan da suka gabata. Ta kawo wasu masana da suka

yi bincike a kan karin magana. A babi na biyu kuwa, bayani ne a kan karinmaganar Hausa, a inda ta tabo ma'ana, dalili, muhimmanci da masu amfani da karin magana. Amma a babi na uku, marubuciyar ta yi bayanin karin magana da ta shafi Bahaushe, Bafullatani, Balarabe, Bature, Banufe, Buzaye da Badakkare. Haka kuma a babi na hudu sai ta kawo karin maganar da ta shafi sassan jiki kamar su fuska, kai, idanu, hanci, hannu, jiki, farce, kafafu, kunne, gemu, ciki da wuya.

Ta karkre aikinta tare da kammalawa da kuma kawo jerin manazarata a babi na biyar.

Ibrahim (2012), a kundin digirinsa na farko, sashen Harsunan Nijeriya UDUS, mai taken 'Dangantakar karin maganar Hausa da Ayoyin Alkur'ani da Hadsi masu jigom gaskiya, tauhidi da fadakarwa'. Ya kasa aikin nasa zuwa babi biyar. A babi na daya gabatarwa ce tare da bayanin ayyukan da suka gabata. Babi na biyu kuma ya kunshi bayanai a kan karin maganar Hausa wanda ya shafi ma'ana, muhimmanci da sauransu. A babi na uku kuwa ya yi bayani ne a kan karin Magana mai jigon gaskiya. A babi na hudu marubucin ya kawo bayanai da suka shafi dangantakar karin magana da wasu Ayoyin kur'ani. A karshe, watau a babi na biyar, sai ya kawo dangantakar karin magana da wasu Hadisai, sa'annan ya nade

aikin nasa tare da kawo manazarta. Waya (1990), a kundin digirinsa na farko mai taken 'Habaici, zambo da Karin magana: Matsayinsu da tasirinsu a cikin al'adar Hausawa' a Jami'ar Bayero, Kano, ya kasa aikin nasa zuwa babi biyar. A babi da daya shimfida ce da bayanin aikin nasa. Babi na biyu kuwa an yi bayanin habaici ne dangane da asali, dalili, illoli, ire-ire da kuma matsayi da tasirin habaici ga al'adar Hausawa. A babi na uku tsokaci ne a kan zambo dangane da asali, dalili, illoli, ire-ire da kuma matsayi da tasirin zambo. Amma a babi na hudu marubucin ya yi bayani ne a kan Karin magana wanda shi yake da alaka da aikina. Nan ma ya dubi asalin ne da dalili, illoli, ire-ire, matsayi da tasirin karin magana ga al'ummar Hausawa. An kamala aikin a babi na biyar inda aka yi bayanin aikin a takaice tare da kawo manazarta.

Akwai bugaggun littattafai misali,Koko (2011) ta wallafa littafi mai suna Hausa Cikin Hausa. Marubuciyar ta tsara littafin nata bisa tsarin babi-babi har zuwa babi hudu. Babi na daya yana dauke da ma’anar karin magana da rabe-rabenta da dangantakarta da harshe da matsayinta ga harshe da kuma amfaninta. Babi na biyu

kuwa, yana kunsh da bayanai a kan masu amfani da karin magana da dalilan da ke haddasa amfani da karin magana tare kuma da muhallin da ake amfani da ita. Babi na uku kuwa, tsokaci ne a kan wasu daga cikin karin maganaganu.

Bello (2007) ya wallafa littafi mai suna ‘Karin Magana Hausa’ Bayan gabatarwa sai marubucin ya kawo bayanai da suka kunshi ma’anonin Karin Magana. Bayan haka sai ya kawo amfanin Karin maganar Hausa. Mafi yawan abin da ya kanannade littafin, shi ne jerin Karin Magana ta fasalin amfani da abcd. An jero Karin maganganu da suka kai kimanin dubu daya da dari tara da sittin da daya.

Madaba’ar NNPC (1958) ta wallafa Littafia mai suna Karin Magana da ya zo da misalai na karin maganganun Hausa masu yawan gaske tare da hotuna domin a fahimce su sosai. Ba wasu bayanai da suks biyo baya, illa kawai an jera su ne zallarsu.

Rattery (1913), a littafinsa mai suna: Hausa Folklore, Customs and Proberbs ya ya tattara tatsuniyoyi da karin maganganunHausawa a waje daya, sa’annan yakawo tatsuniyoyi a cikin rubutun ajami a gefe daya, yayin da a daya gefen ya juya su

zuwa Hausar boko, tare da kawo fassararsu zuwa Ingilishi. Shi kuwa Greene (1966) a cikin littafinsa mai suna Hausa ba Dabo Ba Ne, ya tattara wasu karin maganganun Hausa ne, a inda ya dauke su yana ba su fassara a cikin Ingilishi. Wato ya dinga daukar karin maganar Hausa yana kawo bayani tareda fassara abin da take nufi.

Madauci da wasu (1968) a littafinsu mai suna, HausaCustom, sun yi kokarin nazartar matakan rayuwar Hausawa guda uku, wadanda suka danganci haihuwa da mutuwa da aure da addini. Haka kuma sun dubi wasu al’adu kamar wasannin dambe da kokawa da dai sauransu. Sun kuma yi magana a kan sana’o’in Hausawa na gargajiya da irin muhimmancin da yake tattare da kowace sana’a. Kodayake a cikin harshen Turanci aka rubuta littafin, amma ana zayyano karin maganganun

Hausa a zube a karshen littafin a matsayin rataye, amma dai ba su yi sharhinsu ba.

dubu biyu da suka shafi adabi da kuma rayuwar Hausawa. Ya kuma yi kokarin

zayyana su bisa tsarin abcd amma bai yi sharhinsu ba.

Umar, (1987) ya wallafa littafi mai suna Dangantakar Adabin Baka da Al’adun Hausawa. Marubucin ya yi kokarin fayyace fagen nazarin da wannan littafi yake bayani a kai inda ya bayyana sanadiyyar kafuwar al’umma da yadda al’adu suke samuwa. Haka kuma ya bayyana nau’o’in al’adun gargajiya da muhimmancinsu, sannan kuma ya kawo bayani game da adabin baka da muhimmancinsa ga rayuwar al’umma wanda karin Magana na ciki. Bugu da kari, ya yi kokarin fito da yanayin

wasu al’adun Hausawa na gargajiya wadanda suka hada da addini da mulki da tsarin zaman iyali da sauransu.

Har wa yau, ya yi kokarin bayyana adabin baka na Hausa da ya kunshi wasu rukunoni guda uku: wato zube da waka da wasan kwaikwayo. Sannan ya yi sharhi a kan kowane rukuni na adabin baka tare da misalai, domin fito da al’adun da suka kunsa.

BABI NA BIYU

NAZARIN SALON TSARIN SAUTIN KARIN MAGANAR HAUSA

Hyman (1975)25, ya yi bayanin cewa tsarin sauti ya shafi yadda mutane ke furuci da ilmin da yake tattare da shi, da kuma kashe-kashensa. Wani bangaren ilmin harshe ne da ya nazarci harsuna daban-daban na duniya.

Kowane yare yana da irin nasa tsarin sauti da ya shafi ire-iren furucinsu. Babu yadda za a yi ilmin wani harshe ya yi daidai da wani harshn, saboda yanayin harsunan ba daya ba ne, mabambanta suke da juna ta fannoni da yawa. Misali, duk

da yake mafi yawan sautukan Hausa an aro su ne daga Turanci, amma akwai sautukan Turanci da babu su a Hausa [p, k, b, da d] kamar yadda yake a Hausan ma akwai sautukan da ke da akwai wadanda babu su a Turanci [b, d, k, ky, kw, ky,

kw, gy, gw, fy, da sh]. Kodayake Hausa a furuci tana da [p] amma a rubuce ana rubuta harafin [f] ne.

A harkar salon tsarin sautin karin maganar Hausa, yana da muhimmaci kwarai a san yadda Baushen asalin yake furucinsa, saboda samun damar tantance amsa-amo Kodayake an fassara 'salo' a baya, amma Ullman (1971)26 ya bayyana cewa, salo ba bangare ba ne na harshe, shi ma yana zune ne da kafafunsa. Saboda haka, salo na da kashe-kashensa kamar yadda shi ma harshe yake da shi. Archibald Hill (1951)27, ya bayyana salo da cewa ba wai ya takaita a jimala ba ne kawai, ya watsu ga dukkan sauran bangarorin furuci. A dangane da haka, bari mu kalli wadannan karin magana wadanda za a iya tattaunasu a kan kowane irin salo:

/ Hل:-lى zل:-nèn dْ:-tsي / (389)

'Character is a line drawn on a rock'

/ Mâi hà-lى bل: yà bà-rîn hل-lىn-šى / (677)

'Character cannot be changed'

BABI NA UKU

YANAYIN ILMIN KWAYOYIN MA'ANA DA GININ JUMLA Yanayin salon kwayoyin ma'ana da ginin jumla, sun shafi karin magana kamar yadda muka ga tasirin salon tsarin sauti a cikinta. Bayanammu sun jingina ga hasashe guda biyu, na farkonsu ya shafi yanayin da aka samu harshe shi ke ba da hasken irin salon da ya kamata a bi wajen bincikensa. Na biyun kuma shi ne, karin magana na da wani tsari da yakan sha bamban da irin yanayin tsarin harshen da karin maganar ta fito daga gareshi.

BABI NA HUDU

TAKAITAWA da KAMMALAWA. Idan aka kula da abubuwan da aka bayyana a baya, ga sakamakon da aka samu a

kan karin maganar Hausa:

(1) Tana da tashin sauti da ya kunshi na aininihi/babba da kuma karami, kowane na iya zuwa na farko ko na biyu a cikin kalma. Yawan tashin sauti da ake samu a karin magana, ya danganci tsawon karin maganar.

(2) Mafi lokuta tana karewa da wasali;

(3) It has among its items a minimum of two forms with identical syllable structure;

(4) Tana da amsa-amo somin tabi;

(5) Tana da halaye na maimai na kwayar ma'ana ko na ginin jumla. yana zuwa da sigogi daban-daban, 'yantacce, sarkakke ko waninsu;

(6) Mafi yawa tana da daffan mutumna uku, kuma wadannan daffan suna taimakawa kumshiya;

(7) Tana da tsarin daidaito mai yankuna biyu iri daya. Daidai ya tabbata har cikin karin magana mai sahe daya wanda yake da wajen kashi ashirin da biyar  na kundin;