Malaman Zaure Da Gudummawarsu A Harshen Hausa
Lahadi, 24 Faburairu, 2019
Malaman Zaure Da Gudummawarsu A Harshen Hausa

Takardar da a ka gabatar a taron kara wa juna sani na kasa da kasa a kan Nazarin Harshen Hausa Karo Na Farko A Karni Na 21 a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Na Jami’ar Bayero da ke Kano (10 – 12 ga Nuwamba, 2014). Tsakure Malaman zaure are the Hausa traditional Islamic scholars, who usually stay at the entrance hall (zaure) of their houses where they gather students and teach them. The profession of Malaman zaure is called Malantaka or Malanta. This Paper titled Malaman Zaure da Gudummawarsu a Harshen Hausa is dibided into two parts. The first part consist an introduction and brief edplanation about Hausaland, Hausawa and their architectural system. The paper also discussed on the brief history of Islamic education system and the effort of some Islamic scholars in educating Hausa people which led to what produced Malaman zaure. The second part of the paper discusses the teaching methods of Malaman zaure and classification of their students, as well as their contributions to Hausa with respect to consonant and bowel modification, translation and word formation. Finally, there is conclusion and references.

1.0 Gabatarwa Kowace al’umma ta duniya tana da nata hanyoyin da take bi, domin ilmantar da ‘ya ‘yanta. Hanyar koyarwa ta tsarin ilimi na bai daya, aba ce da ta sami karbuwa sosai daga al’ummomi daban-daban na duniya. Muhimman abubuwan da ake bukata a irin wannan tsari sun hada da: Samar da azuzuwan karatu da manhaja da amitattun littafan karatu da kuma tankade da rairaya dangane da abin da aka koyar da dalibai. Har wa yau, shi kansa ilimin addinin Musulunci ya zo da nashi tsarin koyarwa na musamman, wanda ya sha bamban da tsarin koyarwa na ilimi na bai daya. Alal misali; sun bambanta ta fuskoki da dama kamar haka: Manufa: Manufar tsarin koyarwa ta ilimi na bai daya ta ta’allaka ne ga samar da dubarun warware matsalolin rayuwar yau da kullum. A yayin da manufar tsarin koyarwa ta ilimin addinin Musulunci ta ta’allaka da warware dukan matsalolin rayuwa tare da neman sakamako daga wurin Ubangiji, kasancewar a Musulunce ana yin karatu ne da umurnin Allah. Kamar yadda ya zo a Alkur’ani mai girma “Yi karatu da sunan Ubangijinka” (96:1). Wannan shi ya sa Malaman addinin Musulunci suka ce kowane irin karatu ana yinsa ne da sunaan Ubangiji. Matallafa: A tsarin koyarwa na ilimi na bai daya, ana amfani da azuzuwa ne a matsayin muhallin da ake koyarwa a cikinsa. Haka kuma, a tsarin koyarwar, malami kan zo ne gaban dalibai ya tsaya a cikin aji ya koyar da su, ta hanyar amfani da allo da alli da magogi da littafi da rubuce-rubuce da zane-zane da hotuna da sauransu. A lokaci guda su kuma dalibai suna zaune a kan kujeri da tebura suna fuskantar malami domin koyo, ta hanyar amfani da littafan karatu da na rubutu da na zane-zane da alkalami da fensiri da sauran kayan karatu. Amma a tsarin koyarwa irin na ilimin addinin Musulunci, akan yi amfani ne da kowane irin bagire ya samu domin koyarwa. Alal misali; akan yi karatu a masallaci ko a zauren gida ko a karkashin bishiya ko a aji irin na zamani ko ma a rumfar kasuwa da dai sauransu. Haka kuma, malami kan zauna ne a kan tabarma ko wundi ko buzu da makamantansu, a yayin da dalibai za su zauna su yi da’ira, su kewaye malami suna daukar darasi daya bayan daya, ta hanyar jan baki malamin na fassarawa. Idan kuwa masu koyon karatun Alkur’ani ne, zai ringa ja musu tilawa su kuma suna bibiyawa. Manhaja: Manhajar karatu irin ta tsarin koyarwa na ilimi na bai daya, akan shirya ta ne a matakan karatu daban-daban. Inda a kowane matakin karatu akan tsara masa tasa manhajar da za a bi domin a koyar. Haka kuma a yayin da dalibi ya kammala karatun, za a ba shi takardar shedar kammalawa. Amma a tsarin koyarwa na ilimin addinin Musulunci, manhajar karatu kan kunshi fagage daban-daban ne na ilimi, ba tare da iyakance wasu matakai ba na bayar da takardar sheda. A takaice dai, wannan takardar za ta yi tsokaci ne a kan tsarin koyarwa irin na ilimin addinin Musulunci a gargajiyance, tsakanin al’ummar Hausawa. Bayan haka kuma, za ta nazarci irin rawar da Malaman Zaure ke takawa wajen bunkasa Hausa a yayin koyarwarsu ta yau da kullum. 2.0 Takaitaccen Tarihin Hausawa Da Kasar Hausa Hausawa al’umma ne da ke yanki Afirka ta Yamma, galibinsu suna zaune a Arewacin Nijeriya zuwa Kudancin Kasar Nijar. Dadaddiyar sana’arsu ita ce noma da farauta da yawon kasuwanci (fatauci). Har wa yau, akwai Hausawa mazauna kasashe kamar su: Ghana da Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Benin da Burkina Faso daTogo da Sudan, da kuma wasu manyan birane da yawa da ke Arewa maso Yammacin Afirika da kuma Afirka ta tsakkiya. Haka kuma, mafi yawan Hausawa Musulmai ne. ‘Yan kalilan daga cikin Hausawa ne ke bin wasu addinai da ba na Musulunci ba. (org/wiki/hausapeople) Tun shekaru aru-aru Hausawa suka yi suna wajen fatauci zuwa kasashen waje. Sukan ketare hamadar sahara zuwa kasashen Morocco da Aljeria da Tunisia da kuma Libiya suna safarar fatu da kiraga zuwa wadannan kasashe, kuma suna sayo tufafi da makamai. Haka kuma sukan yi kudu ko yamma zuwa Kurmi, wato kasasr Yarbawa ko zuwa Gwanja da Dogomba da Ashanti a kasar Ghana. Babban abin safararsu a wannan shiyya shi ne goro da gishiri. Su kuma sukan kai kanwa. (Zarruk 2007). A yau, Hausawa sun shiga sako-sako na wannan duniyar domin hulda ta kasuwanci iri-iri da kuma cudanya da al’ummomi daban-daban. Harshen Hausa na daya daga cikin gungun harsuna ‘yan gidan Chadi (Chadic). Haka kuma, kiyasi ya nuna cewa, akwai mutane kusan miliyan tamanin zuwa miliyan dari (80,000,000 – 100,000,000) da suke magana da Hausa a matsayin harshen farko a gunsu. Har wa yau, hasashen ya nuna akwai wasu miliyan dari da ba ‘yan asalin harshen ba, amma suke amfani da shi yadda ya kamata a mu’amaloli daban-daban. (Yusuf 2011) Kasar Hausa tana shimfide ne a tsakanin rairayin Hamada na sahara daga Arewa, da kuma dazuzzukan da suka doshi tekun atilantika daga Kudu. Kasar Hausa tana shimfide ne a tsakanin kudu maso gabashin Nijar da arewacin Arewar Nijeriya. Daga gabas ta yi iyaka da kasar Barno. Ta yi iyaka da kasar Benin ta gabar kogin Kwara da kasar Zabarma ta daular Songhai daga yamma. Daga arewa kuwa, ta yi iyaka da kasar Adar da kasar Azbin, a yayin da ta yi iyaka da kabilun Gwari da na kudancin Zariya daga kudu (Abdullahi 2008 da Malumfashi da Nahuce 2014 da Zarruk 2007). A gargajiyance tsarin yanayin gidaje a kasar Hausa yana da gwanin ban shaawa. Mutanen da suke zaune a kauyukan kasar Hausa sukan tsara mazauninsu ne ta hanyar yin wasu kewayayyun dakuna (bukkoki) ta amfani da kara da kuma shibci (karan dawa ko na gero da hakin shinkafa ko na lalaki). Haka kuma, sukan yi amfani da su don zagaye gidajen nasu (danga ko darni) ta hanyar yi musu kusurwa hudu .Idan magidanci na da mata fiye da daya, zai yi wa kowaccensu tata bukka, sannan ya koma kofar gidan ya yi zauren shigowa gidan. Idan har yana da bukata kuma, sai ya koma wani bangare ya yi wa kansa turaka (baraya) . A cikin birane kuwa, mutane kan yi amfani da kasa ne su gina dakuna masu kusurwa hudu tare da yi musu rufin kasa. Haka kuma sukan zagaye gidajen nasu ne da katangu na ginin kasa, daidai gwargwadon yadda magidanci ke bukatar tsawon gininsa, haka zai yi abinsa. Har wa yau, sukan gina zauren gida a kofar gidan, inda nan ne maigida kan zauna da abokan huldarsa a lokutan safe da rana, su kuma yaran gida idan dare ya yi nan ne wurin baccinsu. A biranen su ma ana gina wa kowace mata nata daki, shi kansa maigida yana gina turakarsa (Madauci 1968) Shi zauren gida akan gina shi ne da kofofi biyu. Kofa ta farko ita ce ta shiga zauren ta biyu kuwa, ita ce ta shiga cikin gida. Kowane zaure ana gina shi ne gwargwadon matsayin maigida. Alal misali, idan magidanci mai arziki ne ko mai mulki, to dole ne ya gina zauren gida mayalwanci domin saukar da baki da taruwar jama’a, kamar yadda yake a al’adance. Tarihi ya nuna cewa, kafin al’ummar Hausawa su karbi addinin Musulunci sun kasance suna bauta wa iskoki da manyan duwatsu da kuma gumaka. Babbar ibadarsu ita ce tsafi da bori. (Yahaya 2002) Ya bayyana cewa, addinin Musulunci ya shigo kasar Hausa ne a wajajen karni na goma zuwa na goma sha shida (10–16 k) wasu manyan masana ne daga kasashe daban-daban na Afirika suka zo kasar Hausa domin wa’azi da ilmantarwa da kuma yada addinin Musulunci. Alal misali a shekarar 1452–1463 wasu Fulani (Torankawa da Sullubawa) karkashin jagorancin Malam Musa Jakollo suka zo kasar Hausa daga Futa–Toro da ke kasar Malle. A shekara ta 1463–1499 wasu Malaman, wadanda ake kira Wangarawa karkashin jagoranci Malam Abdurrahman Zagaiti suka zo daga Senegal don yada addini a kaskr Hausa. Har wa yau, wani gungu na malamai daga Tilimsan ta kasar Moroko (Morocco) sun shigo kasar Hausa karkashin jagorancin Malam Abdulkarim Al-Magili, a shekara ta 1494. Dukan wadannan Malaman sun yi aiki tukuru, domin yada addinin Musulunci da kafa tauhidi da koyar da karatun furu’a (Fikihu) a kasar Hausa. Wannan jan aiki nasu shi ya kai ga haifar da dimbin jama’ar Hausawa suka rungumi addinin Musulunci. Bugu da kari, wadannan masana sun gina cibiyoyin Musulunci da masallatai da makarantu da dama. Ban da wannan ma, sun rubuta latafai daban-daban, cikinsu har da tsarin yadda ya kamata a tafi da mulki. Alal misali, Malam Almaghili ya rubuta kundin tsarin tafi da mulki ga sarkin Kano Muhammadu Rumfa wanda ya kira da Larabci Taj al-Din Fi Ma Yajibu Alal al-Muluk wato, Jagora a kan Nauyi da ya Hau kan Shugabanni a Addini. Haka kuma, shi ya gina Masallacin unguwar Sharifai a Kano. Wannan gwagwarmaya ta yada ilimin addinin Musulunci da wdannan masana suka aiwatar ita ce musabbabin samuwar dimbin malamai da dalibai da suka shahara a kasar Hausa. Alal misali, ita ce ta haifar da samuwar manyan Malamai kamar su Wali Dan-masani da Wali Dan-marina a Katsina da Malaman Kusfa wdanda aka sani a Zariya da Malaman ‘Yandoto a Bauchi da Tsafe (Jihar Zamfara), har da ma, mayan Shahararrun Malaman nan da suka zauna a Kano da Zariya da Sakkwato, wato Malam Muhammadu na Birnin Gwari da Malam Shi’itu Dan Abdurra’uf. Malam Muhammadu Al-Katsinawi. Sakamakon samuwar wadannan dalibai da Malamai a kasar Hausa, sai gwagwarmayar da wadancan masana ke yi ta yada ilimi da harkokin addinin Musulunci ta koma a hannun Malamai ‘yan gida. Saboda haka, kowane Malami sai ya zabi ya zauna a zauren kofar gidansa domin ya koyar da dalibansa. Wannan kuwa, shi ya janyo a kira su da Malaman Zaure ko Malaman Soro a wasu wurare. Idan aka ce Malaman Zaure ana nufin: Malaman addinin Musulunci da ke koyarwa a gargajiyance a kasar Hausa, wadanda ke zaunawa a zaurukan kofofin gidajensu suna karantar da dalibansu. Shi kuma irin wannan aiki nasu ana kiransa Malanta ko Malantaka. Malanta: sana’a ce wadda malamai da masana ke yi don su koya wa almajirai abin da suka fahimta na ilimi da sani. (Alhassan 1988) Malantaka na nufin: aikin yada ilimi (Kamusun Hausa 2006) Ana kallon Malantaka a matsayin wani aiki na koyarwa (Newman 1997) A shekara ta 1804 an sami wani agarumin sauyi da ya kawo wasu canje-canje masu ma’ana a ilimi da harkokin addinin Musulunci a kasar Hausa. Wannan sauyi kuwa shi ne Jihadin Musulunci da ya auku karkashin jagoranci Mujaddadi Shehu Danfodiyo (Allah ya kara masa yarda). Daya daga cikin manyan manufofin wannan Jihadin akwai yada ilimin addinin Musulunci tare da sake sabunta shi da kuma yin gyare-gyare a wasu bangarori nasa. Kafin Jihadin Muajaddadi Danfodiyo, an sami gurbata da son rai sun durmuya a cikin harkokin ilimin Musulunci, kamar yadda shi kansa Shehu Danfodiyo ya fada a litafinsa Nurul Al-babi. Haka su ma kansu makarantun zaure din sun karanta ga al’umma. Saboda haka, Shehu Usmanu da almajiransa suka dukufa ga rubuce-rubuce da ilmantarwa da fadakarwa ga jama’a. Bugu da kari suka kara kaimi wajen bubbuda makaratun zaure a koina a fadin kasar Hausa. Wannan shi ya kawo gagarumin sauyi da kuma yawaitar Malaman Zaure da Makarantun Zaure (Makaarantu Allo) bila-adadin a daular Usumaniyya. 3.0 Gudunmmawa A Hausa Abu ne mai sauki a iya fahintar irin gudummawar da Malaman Zaure ke bayarwa ga harshen Hausa. Musamman idan aka tsaya aka nazarci irin dubarun da suke bi wajen ilmantar da jama’a. Mafi yawa a tsarin koyarwa irin na Malaman Zaure akan kasa sha’anin Malanta ne zuwa mataki uku kamar haka: 1. Matakin na koyar da masu koyon Kidan Baki da karatun Alkur’ani (elementary stage) 2. Mataki na koyar da masu koyon karatun sani/karatun ilimi (secondary stage) 3. Mataki na koyar da wadanda suka kai Malamai (adbanced stage) 3.1 Mataki Na Koyar Da Masu Koyon Kidan Baki Da Karatun Alkur’ani A wannan matakin, galibi kananan yara wadanda suka fara zuwa makaranta ne ake koya wa yadda za su iya furta sautukan Alkur’ani Maigirma, (bakake da wasulla) da kuma yadda ake gwama su a furta lafuzzansa. Mafi yawa, ana koyar da wannan ne a surorin Alkur’ani goma na karshe (daga Suratun Nas zuwa Suratun al Fili) Dubarun koyarwar da Malaman Zaure ke amfini da su wajen koyar da sautukan Alkur’ani Maigirma, ta yadda Bahaushe zai iya furta su ba tare da wahala ba, ita ce kwaskwarima (modification). Inda suke furta sautukan (bakake da wasulla) a Hausance. Misali, sautin Ba’un na Larabci (ب) sukan kira shi Ba-guje. Sautin Ha’un (ح) Ha-karami. Sautin Ka’fun kuwa, (ک) Kaulasan. Irin wannan koyar da sautukan Alku’ani da Hausa, shi ake kira Kidan Baki. Ga misali wasu sautukan a cikin wannan Jadawali domin karin haske: BAKAKEN LARABCI TAKWARORINSU A HAUSA YADDA AKE KIRANSU A LARABCI KWASKWARIMA A HAUSA TAKWARORINSU A INGILISHI ﺑ ﺐ [b] Ba’un Ba Baguje B ﺖ ﺓ [t] Ta’un Taguje Takuri T ﺣ ﺡ [h] Ha’un Ha-karami Ha-karami komas baya H ﺝ[j] Jimun Jin-karami Jin-karamin komas baya J ﺴ ﺲَ [s] Sinun Sin Sin’ara S ﻅ ﻂ [zw] [d] Zwa’un Da’un Zwadi Damasannu Z D ﻏ ﻐ [g] Gainun Angaibakin-yofi Angailikkafa G کﻕ [k] [k] Kafun Kafun Kaulasan Kaf-wau K K Har way au, a wannan matakin ne ake koyar da dalibai sautukan wasulla wanda ake kira Kidan Wasulla. Shi ma kwaskwarima ce ake yi wa sautukan, inda ake Hausance su domin saukaka wa dalibai iya furta su da tantance su a cikin sauki. Misali, sautin fatha na Larabci ( َ ) akan kira shi wasali sama. Sautin kisira ( ِ ) wasali kasa. Sauttin dwamma ( ُ ) ana kiransa rufu’a. sautin jazma kuwa, ( ْ ) shi ake kira da dauri. A wasu lokuta a harshen Larabci akan ninka sautukan fatha da kisira da dwamma (duplication) (ً ٍ ٌ ) wanda ake kira tanween a Larabce, amma sai a Hausance shi a kira shi faduwar wasulla sama, idan fatha ce ko faduwar wasulla kasa, idan kisira ce ko kuma faduwar rufu’o’i sama, idan ta kasance dwamma. Ga misali a cikin jadwali: WASULLAN LARABCI TKWARORINSU A HAUSA YADDA AKE KIRANSU KWASKWARIMA A HAUSA َA Fatha Wasali sama ِ IKisira Wasali kasa ُ U Dwamma Rufu’a ْ Jazma Dauri ً An Tanween al-fatha Faduwar wasulla sama ٍ InTanween al-kisira Faduwar wasulla kasa ٌ Un Tanween al-dwamma Faduwar rufu’o’I sama Daga tsarin wadannan sautukan ne (bakake da wasulla) da aka yi wa kwaskwarima aka samar da rubutun Ajami. Wanda yana daya daga cikin muhimmiyar gudummawar da Malaman Zaure suka bayar ga samuwa da habakar rubutu a harshen Hausa. Rubutun Ajami shi ne inda marubuci kan yi amfani da sautukan Larabci ya rubuta bayani da harshe Hausa. Saboda haka, a wannan mataki dalibai za su iya gwama sautuka su tada kalmomi, wanda a karshe kuma har ta kai suna iya karanta Alkur’ani Maigirma. 3.2 Mataki Na Koyar Da Masu Koyon Karatun Sani/Karatun Ilimi A wannan mataki na Malanta, daliban da suka kammala karatu a mataki na farko ne ake koya wa karatun sani. A nan akan soma da koyar da dalibai ilimin Tauhidi da Furu’a da kuma harshen Larabci (wato, nahawu da tasaifi da adabi). Babu shakka a wannan mataki dalibai na iya karanta Alkur’ani maigirma kuma suna iya karanta lafuzzan Larabci. Saboda haka, za su iya jan baki malami na fassara musu. Galibi lattafan ake fara koyar da dalibai a nan su ne: Usulul al-Din na Sheikh Usmanu Danfodiyo Nurul Al-Babi na Sheikh Usmanu Danfodiyo Al-Kawaa’ed na Malaman ‘Yandoto Bayan kammala wadannan sai a biyo wa dalibai da wasu littafai na ilimi daya bayan daya ana koyar dasu, har su kai munzalin da za su kasance kananan Malamai, wadanda a al’adance ana tura su koyar da matan aure. Haka kuma suna iya zama Malaman kananan yara ‘yan ajin matakin farko. Ga ‘yan wasu kadan daga cikin jerin ltatafan da ake koya wa daliban wadanda suka shafi Furu’a: Al-Mukhtasar al-Akhadari, na Abdul-Rahman al-Akhdary Al-Kurdaby, na Malam Yahaya al-Kurdaby Mukaddimatul Ibn ar-Rushidin, na Al-Sheik Abdurrahman Arrafi’ey Bayanul Bidi’ah na Sheikh Usmanu Danfodiyo At-Takaribu Al-Darury na Shehu Usmanu Danfodiyo Kitabul al-Iziyyah, na Abul Alhasan Aliyu al-Malikiyyu Matanur al-Risalah, na Abu Zaid, al-Kirawany. Fatahul al-Jawad, na Sheik Yahuza Zaria Dau’ul al-Musalli, na Sheik Abdullahi Gwandu Al-Mukhtasar al-Khalily, na Muhammad al-khalil Wasu littafan da ake koya wa dalibai a wannan matakin sun hada da na: Nahwun Larabci da Tasarifi da Balagah da Mandiki da Arudi da Adabi da Ilimin Hadisi da kuma Ilimin sanin Alkur’ani maigirma. Ga misalign kadan daga cikin littafn: Matanul al-Ajarumiyyah, na Abi Abdullahi Muhammad bin Muhammad. Ta’alim al-Muta’allim Tarikal al-Ta,allum, na Burhan al-Din al-Zarnuji Sharhul Ibn al-Akeel, na Ibn Akeel Alfiyatul al-Sayuty, na Imam Abdul-Rahman al-Sayuty Mukamatul al-Hariry, na Muh’d al-Kasim ibn Ali ibn Muh’d ibn Uthman al-Hariri Kitab ash-Shu’ura, na Umru’ul-Kais Kitab al-Deliyyah na Ibn Naseer. Ashsharhul al-Kitabu az-Zuhd, na Imam Umar ibn Abubakar ibn Usman Al-kubawy Hisnul ar-Rasinu, na Sheik Abdullahi Gwandu. Al-Khulasatul al-Usuli, na Sheik Abdullahi Gwandu Al-Tarikhul al-khulafah, na Imam Abdul-Rahman Al-Sayuty Kitab al-Ashafa, na Al-kadi al-Iyad Bulugul al-Marami, na Ibn Al-Hijir al-Askalaany Riyadu as-Salihin, na Imam Yahaya Annawawy Ihya’ul as-Sunnah, na Sheik Usmanu Danfodiyo Daliban da suka yi zurfin karatun a wannan mataki ana kallonsu a matsayi kananan Malamai ko manyan almajirai, sai dai ba su da cancantar yin Fatwah sai zuwa lokacin da suka kai matakin karatu na gaba, inda za su kasance da ilimin da za a iya kiransu Malamai. 3.3 Mataki Na Koyar Da Wadanda Suka Kai Malamai A wannan mataki na Malanta dole malami ya kasance babbabn malami kuma shahararre, domin daliban da ke wannan matakin su kansu malamai ne da ke neman kwarewa. Har wa yau, suna da gogayya da fahimta mai zurfi a kan ilimin Furu’a da Tauhidi da sauran wasu fannoni, saboda haka suna iya yin kyakkyawan tunani da kuma daukar matsayi a cikin harkokin ilimi da addini Musulunci. Bugu da kari, irin wadannan dalibai kownnensu na iya kafa nasa babban zauren ba da karatu. Haka kuma ana tsamanin su kasance mutane masu halayen kirki da tsoron Allah da gudun duniya da kamun-kai da tsantseni ga kowane al’amari da fadar gaskiya ba tare da wani shakku ba. Har way au, daliban da ke wannan mataki na karatu suna iya yin fatawah da kuma tafsirin Alkur’ani mai tsarki, matukar dai sun gulbanta a wasu muhimman bangarori na ilimi da suka hada da: Ilimin Tauhidi da na Furu’a (a kowane sashe) da na sanin hanyoyin tsamo dokokin shari’a (Usulul Fikih) da Nahwun Larabci da Ilimin Ginin Kalmar Larabci da Balagah da Mandiki da Arudi da Adabin Larabci da Tarihin Musulunci. Haka kuma, dole ne a nan dalibi ya kasance kwararre a ilimomin sanin Hadisi. Tun daga sanin ingancin matanin Hadisi da salsalarsa har ya zuwa ga sanin abin da ake kira ruwaya da kuma sanin masu ruwaitowar. Bugu da kari kuma, daliban wannan mataki tilas ne su kasance suna da ilimin sanin fannonin Alkur’ani mai tsarki. Kama daga ilimi kira’a da tafsiri har ya zuwa ga ilimin sanin sabkar ayoyi da surorin Alkur’ani da dalilan sabkarsu da wadanda hukuncinsu ke shafe hukuncin wasu da saurasu. Wadannan su ne matkan malanta da dalibta da dubaru da ake bi wajen aiwatar da su, a tsari koyarwa na Malaman Zaure a wasu gurare na kasar Hausa. 4.0 Gudummawa Wajen Bunkasa Rumbun Kalmomi Hausa Malaman Zaure suna taka muhimmiyar rawa wajan fadada rumbn kalmomi Hausa. Irin hubbasar da suke yi wajen fassara da kokarin da su ke yi wuri bayyana wata kunshiya ko tunani ga dalibai, daga harshen Larabci da adabin Musulunci zuwa harshen Hausa, yana haifar da karuwar kalmomin Hausa. Saboda haka, sukan bunkasa rumbun kalmomin Hausa da sababbin kalmomi. Har wa yau, yadda suke taka tsantsan da zabar kalmomi na mutunci a lokacin koyarwarsu da ma sauran mu’amalolinsu na yau da kullum, don kaucewa amfani da haramtattun kalmomi yakan tilasta musu kera sababbin kalmomi da kuma Hausantar da kalmomin Larabci. Misali: 4.1 Fassara Daya daga cikin dubarun koyarwar Malaman Zaure akwai fassara. Inda suke kokari fito da ma’anar abin da aka rubuta game da addinin Musulunci a cikin harshen Larabci zuwa Hausa, domin samar da makusanciyar fahimta ga dalibai. Ta fuskar kokarin su kawo makusanciyar ma’ana ga dalibai, yakan sa su yi zabin kalmomi da kuma tsarar da wasu kalmomin. Misali: LARABCI ZABI/TSIRAR DA KALMA MA’ANA Wafaatun Ràsúwáá / cíkaàwáá Mutuwa Gaa’idun Tùróósóó Tutu/Kashi FarjunMáátúccìì Gindi Riihun ĺskàà Tusa 4.2 Samar Da Kalmomi A wasu lokuta kokarinsu na fito da cikakkiyar ma’ana abin da suka fassaro daga Larabci, kan janyo su yi aron kalma kai tsaye kuma su Hausantar da ita. Saboda haka, sukan samar da sababbin kalmomi a Hausa duk da cewa akwai takwarorinsu a harshen. Misali: LARABCI HAUSANTATTAR KALMAR TAKWARARTA A HAUSA Dahaaratun Dàhááràà Tsárkíí Duburatun Dúbùráá Tákááshí Fasaahatun Fàsááhàà Ázáncíí Ruuhun RúúhììRâi / Kùrwáá Sulhun Súlhù Sásàntáàwáá 4.3 Kyamar Amfani Da Haramtattun Kalmomi Irin matsayi da kima da mutunci da Malaman Zaure suke da su a cikin al’ummar Hausawa su suka haifar da gaba dayan mu’amalolinsu da harkokinsu na yau da kullum suka kasance cikin tsari da mutunci. Wannan sai ya janyo har kalmomin da suke yin magana da su, dole ne su yi zabi, domin gujewa amfani da haramtattun kalmomin da za su sa a ga munin zancensu. Msali: HARAMTATTAR KALMA MADADINTA Túútù Bááyángídáá/Tùróósóó Háwáá/cî Dùhúúlìì/jìmáá’ìì Gìndíí/Gúútsùù Àl’áuràà/FárjììTsúwàyyáá Márèènáá/Lúnsàyáyníí 5.0 Kammalawa Daga wadannan bayanai da misalai da aka ambata a sama, za a iya cewa Malaman Zaure suna daga cikin manyan masu ba da muhimmiyar gudummawa wajen bunkasa rumbu kalmomin Hausa. Yadda suke kirkira da aro da zabi da tsirar da kalmomi da kwaskwarima ga wasu kalmomin da sautuka duk abubuwa ne da suke taka muhimmiyar rawa a wajen nazari irin na kimiyyar harshe. Saboda haka, akwai matukar bukatar maida hankali ga yawaita bincike da rubuce-rubuce a wannan bangare na rukunin al’umma mai muhimmancin gaske ga harshen Hausa da al’adunsa. Akwai tsoro da damuwa sosai ta la’akari da cewa lokaci na tafiya Malaman Zaure na shudewa, in har masana da manzarta masu bincike ba su maida hankali ba ga wannan janibi mai muhimmanci, to akwai yiwuwar a yi hasara mai dimbin yawa, kuma wannan bangare mai ba da gudummawa da ya shafi nazari harshe da kimiyyarsa zai kai karshe ya mutu murus. 

Sorce: hausa.leadership.ng