Nazarin Kan Masana’antar Kannywood A Shekarar 2019
Lahadi, Janairu 05, 2020
Nazarin Kan Masana’antar Kannywood A Shekarar 2019

Shekarar da mu ka yi bankwana da ita ta 2019, shekara ce da ta samar da abubuwa mabanbanta, wadanda za a iya rarraba su zuwa gida biyu, wato nasarori da kuma kalubale a fannoni daban-daban na rayuwa. Haka abun ya ke a masana’antar fina-finai ta Kannywood, domin a shekarar da ta gabata ta 2019, wannan masana’anta ta shaida abubuwa da yawa wadanda su ka hada da abubuwan yabawa, abubuwan alhini, rikice-rikice, da sauransu.

ABUBUWAN YABAWA.

JARUMI ADAM ZANGO YA DAUKI NAWUN KARATUN DALIBAI GUDA 101.

A watan Oktoba din shekarar 2019, fitaccen jarumin wannan masana’anta ta Kannywood wato Jarumi Adam Zango ya biya sama da Naira Miliyan 46 domin daukar nawin karatun wasu yara su dari da Daya(101) har na tsahon shekara uku(3). Mafi yawan wadannan yara dai marayu ne. Wanda hakan ya janyowa jarumin samun yabo da kuma addu’o’in fatan alkhairi bisa wannan abun alkhairi da ya yi. KASASHEN INDIYA DA AMURKA SUN KARRAMA JARUMI ALI NUHU. A watan Ogustan shekarar 2019, Kasar Amurka ta karrama Jarumi Ali Nuhu. Jarumin ya samu wannan karramawar ne a ofishin jakadancin Kasar Amurka da ke garin Abuja a Najeriya. Bugu-da-kari, a cikin watan Oktoba din shekarar dai, wasu dalibai da kuma malamansu a Kasar Indiya sun kara karrama Jarumi Ali Nuhu da lambobin girmamawa a chan Kasar Indiya.

AN KAWO KARSHEN TAKUN SAKAR DA KE TSAKANIN JARUMI ALI NUHU DA KUMA JARUMI ADAM A.

ZANGO

Hadaddiyar Kungiyar mashirya fina-finan Hausa wadda a ka fi sani da MOPPON, ta samu nasarar kawo karshen rikice-rikice da kuma takun saka da ya dauki tsahon lokaci ya na faruwa a tsakanin fitattun jaruman guda biyu wato Ali Nuhu da Adam A. Zango. Hukumar ta samu nasarar yin sulhun ne a tsakanin su a watan Afrilu na shekarar da ta gabata, a cikin birnin Jihar Kano.

JARUMA HAFSAT SHEHU TA SAKE AURE

Fitacciyar jarumar nan Hafsat Shehu, wadda tsohuwar mata ce ga jarumi marigayi Ahmad S. Nuhu, ta sake aure a watan Oktoba din shekarar da ta gabata. Wannan dai shi ne aure na biyu da jarumar ta sake yi tun bayan rasuwar mijinta na farko marigayi Ahmad S. Nuhu, wanda ya rasu a shekarar 2007 a sakamakon hatsarin mota a hanyarsa ta zuwa Maidugurin Jihar Borno daga Jihar Kano. Wadannan su ne kadan daga cikin muhimman abubuwan yabawa da su ka faru a cikin wannan masana’anta a shekarar 2019 da ta gabata.

ABUBUWAN ALHINI

Jaruma Binta Kofar Soro Ta Rasu Fitacciyar jarumar nan Hajiya Binta Kofar Soro ta rasu a ranar Asabar 4 ga watan mayu a gidanta da ke unguwar Filin Samji da ke Jihar Katsina. Jaruman masana’antar sun nuna alhinisu bisa wannan babban rashi da su ka yi. An Yankewa Jarumi Sani Idris (Moda) Kafarsa Guda Daya Fitaccen jarumin nan Sani Idris Moda ya rasa kafarsa guda daya, wadda a ka yanke sakamakon tsananin rashin lafiyar da ya yi fama da ita. Shi dai wannan jarumi ya dade ya na fama da rashin lafiya, wanda hakan ya janyo wasu su ka fara yada labarin cewa ya rasu tun a shekarar 2018. Sai dai jarumin ya fito ya karyata rade-radin da kansa.

RIKICE-RIKICE SIYASAR SHEKARAR 2019 TA RABA KAN JARUMAN KANNYWOOD

Ra’ayin siyasa ya kawo rikice-rikice a tsakanin jaruman masana’antar kannywood. Wannan na zuwa ne yayin da wasu jaruman su ke bayyana ra’ayinsu na goyon bayan jamiyar APC mai mulkin Najeriya, wasunsu kuma suna goyon bayan jam’iyar adawa ta PDP. Sai dai masu goyon bayan jam’iyar adawa na zargin wasu jarumai ‘yan uwansu da hada kai da gwamnati mai ci domin cin zarafinsu, saboda rashin goyon bayan da su ka nuna mu su musamman a lokacin kakar siyasa. Wadannan dalilai da wasunsu ne su ka saka wasu jaruman ficewa daga wannan masana’anta ta Kannywood kamar su jarumi Adam Zango da Mustafa Na Buruska, kamar yadda su ka bayyana a kafafen yada labarai

AMINA AMAL DA HADIZA GABON

A farkon shekarar 2019 an samu ballewar rikici a tsakanin Jaruma Amina Amal da kuma Jaruma Hadiza Gabon. Shi dai wannan rikici ya samo asali ne sakamakon wani rubutu da ita Jaruma Amina Amal ta yi a shafinta na sada zumunta, ta na bayyana Hadiza Gabon a matsayin ‘yar madigo, wanda hakan ya janyo cece-kuce ga mabiya shafukan sada zumunta. Sai dai bayan wasu kwanaki jaruma Hadiza Gabon ta saki wani bidiyo, inda aka nuno ta tana dukan Amina Amal, ta na mata tambayoyi a kan rubutun da ta yi a kanta. A sanadin hakan ne Jaruma Amina Amal ta maka Jaruma Hadiza Gabon a kotu, ta na neman kotu da ta nemo mata hakkinta a kan cin zarafin da HadizaGabon ta yi mata a cewarta.

HUKUMAR TACE FINA-FINAI TA JIHAR KANO TA KAMA DARAKTA SUNUSI OSCAR DA MAWAKI NAZIRU SARKIN WAKA

Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano karkashin jagoranci Isma’il Na’abba Afakallah, ta maka fitaccen mai bada umarni na Kannywood wato Sunusi Oscar (442) a gaban wata kotu a Jihar Kano, bisa zargin sa da sakin wata waka ba tare da hukumar ta tace ta. sanda a karshe kotun ta mika daraktan zuwa gidan maza. Shi ma dai fitaccen nawakin nan wato Naziru M. Ahmad wanda a ka fi sani da Sarkin waka, wannan hukumar ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin sa da sakin wata waka ba bisa ka’ida ba. Hakan ne ya tilastawa Naziru Sarkin waka yin wasu kwanaki a gidan Yari, kafun daga baya kotun ta ta bayar da shi beli. Sai dai wasu jaruman masana’antar da kuma masu fashin baki sun bayyana cewa, kamun Oscar da Sarkin waka ya na da alaka ne da ra’ayi na siyasa. Wadannan su ne kadan daga cikin muhimman abubuwan da su ka faru a shekarar 2019 a masana’antar fina-final ta kannywood. Bugu-da-kari, Jaridar Leadership Hausa A Yau Lahadi, ta samu nasarar kawo muku tattaunawa da wasu Jarumai, daraktoci, masu shiryawa, mawaka fiye da guda goma sha biyar (15) na masana’antar kannywood a shekarar da ta gabata.

Source: Leadership A Yau