Dangantaka tsakanin kasar Misra da Algeria
Lahadi, Afrilu 07, 2019
Dangantaka tsakanin kasar Misra da Algeria

Dangantaka tsakanin kasar Misra da Algeria

Tarihi:

Daddaden tarihi ya shaida dangantaka tsakanin kasar Misra da Algeria ta fuskar musayar goyon baya da kuma taimamakekeniya, kasar Misra ta taimaka wa kasar Algeria a babban borenta na juyin juya hali na neman 'yanci daga mulkin mallakar kasar Faransa a shekara ta 1954, kasar Misra ta gamu da musgunawa daga kasashe uku, kasar Faransa da Isra'ila da kuma Burtaniya, a shaekara ta 1956 saboda matsayanta na taimaka wa Boren kasar Algeria. Algeria ce kasa ta biyu da ta goyi bayan kasar Misra a lokacin yakin 1973.

Dangantaka mai fadin gaske ta hada kasar Misra da Algeria ta fuskar masalahohin da suke tsakaninsa, a dukkanin fagagen siyasa da tsaro da tattalin arziki da zamantakewa da kuma al'du. Algeria ta kasance ita ce kasa ta farko da shugaba Abdulfattah El-Sisi ya ziyarta tun lokacin da ya zama shugaba zababbe, a watan Yuni na shekara ta 2014, al'amarin da ya samar da cigaba mai kyau kuma mai girma a dangantakar kasashen biyu.

Dangantakar siyasa:

Kyakkyawar dangantakar siyasa tsakanin kasashen biyu ta bayar da kyakkyawar dama domin bunkasa dangantaka a wasu bangarori daban daban, musamman a halin da ake yanzu, akwai cikakken daidaito a mahangar kasashen biyu dangane ta abin da ya shafi kasar Libiya, dangane da muhimmancin samun kwanciya hankali a Libiya.

Kasashen biyu na bukatar gudanar dangantaka da hadin kai a tsakaninsu domin bibiyar dukkanin batutuwan kasashen Larabawa da kuma cigaban da yake gudana a kasashen Larabawa da na Afrika, na farko shi ne Batun kasar Falasdin da kuma halin kasar Iraki da Siriya da Yamen, da kuma aiki a kan samar da kwanciya hankalin ta fuskar siyasa a kasashen Larabawa da kasashen Musulumai da kuma kasashen Afrika.

Tattakin arziki:

Akwai dangantakar tattalin arziki mai karfi sosai ba ta kafu ne kadai akan girman musayar kasuwanci ba, haka kuma ta shafe samar da kudaden shiga tsakanin kasashen biyu, ana kwatanka girman samar da kudaden shigar kasar Misra da Algeria da kwatankwacin Dala biliyan dubu 3.6, girman musayar kasuwanci a tsakanin biyu ya kai sama da dala milyan dubu, yayin da girman samar da kudin shigar kasar Algeria a Misra bai wuce dala milyan 90 ba.

A Algeria akwai kimanin kamfanoni 32 na kasar Misra, suna aiki a bangaren: sadarwa, da kera kayayyakin noma. Misra tana da manya manyan kamfanoni tare da hadin gwiwar kasar Algeria.

Akwai babban nauyi da aka dora wa majalisar ayyukan kasar Misra da Algeria, domin dude kasuwanni da kuma gudanar da ayyukan bai daya a dukkanin bangarori, haka kuma kasashen biyu suna bukatar karfafa taimakekeniya da kuma harkar musayar yawon bude ido musamman an samu karuwar adadin masu yawo bude ido 'yan kasar Algeria a Misra a shaekara ta 2018.

Dangantakar tattalin arziki tsakanin kasar Misra da Algeria ta samu yin karfi tun shekara ta 2014 bayan taron kwamitin dattawa tsakanin kasar Misra da Algeria karo na bakwai karkashin shugabancin ministocin kasashen biyu. Ibrahim Muhallab da Abdul Malik Salal, a lokacin taron an sanya hannu a yarjejeniya 17 tsakanin kasashen biyu wadda ta kunshi abubuwa da dama. Abubuwa da ake fitarwa da ga kasar Misra zuwa Algeria sun hada. Kayan Alminiyom da karafuna, da wayoyi da sauransa da kuma siminti da nau'o’insa da magunguna da na’urar sanyaya daki, da kuma naurar aski da irin shuka, da kayayyakin kera kuka gas da injin wanki da firji da kuma kayayyakin gyaransu da batuta da karafuna da kayan wutar lantarki da injina da kwayayen wutar lantarki da nau'ukan kwalabe, da abubuwan da ake yin takarda da rabobi da littattafan makarantar da jaridu da mujallu da kayayyakin gyaran mota. Yayin da kayayyakin da ake shiga wa da su daga Algeria zuwa Misra suka takaitu a abubuwan da ake samarwa daga man fetur.

Al'adu da kuma sadarwa

Akwai musayar al'adu mai zurfi tsakanin kasar Misra da Algeria, hakan na faruwa ne a halartar kasashen biyu wasu bukukuwa a tsakaninsu, ko kuma wanda wani garin ya shirya, daga cikin halarta mai shahara, ita ce halartafr kasar Misra. Kusdandaniyya hedikwatar al'adun kasashen Larabawa da halartar kasar Misra bikin baje kolin littattafai na kasa da kasa a matsayin bakuwa ta musamman, da kuma halartar kasar Algeria bikin baje kolin littattafai na kasa da kasa a birnin Alkahira a watan Fabarairu shekara ta 2018 a matsayain bakuwa ta musamman, da kuma halartar kasar Misra a kowane lokaci a dukkan bukukuwa.

Al'adun da ake yi a kasar Algeria, kamar:

Bikin "waharan na sinimar kasashen Larabawa" yayin da ake karrama wasu fannanai yan kasar Misra a koda yaushe duk lokacin da bikin ya zagayo.

Ta fuskar Addini:                                                       

Haka kuma taimakekeniya ta fuskar Addini a tsakanin kasashen biyu tana cigaba wadda ta shafi sha'anin Addini, wanda ya kasance fage mai muhimmanci tsakanin bangarorin biyu, yayin da kasar Algeria take halartar dukkanin tarukan Addini da Al'azhar da hukumar bayar da fatawa ta kasar Misra da ma'aikatar addinin Musulunci ta kasar Misra suke shiryawa, kamar ita kasar Misra take halartar tarukan Addini na kasar Algeria.