Dangantaka tsakanin kasar Misra da Habasha (ETHIOPIA)
Talata, Fabrairu 19, 2019
Dangantaka tsakanin kasar Misra da Habasha (ETHIOPIA)

Abubuwa guda biyu ne suka kulla dangantaka tsakanin al'ummun kasashen Misra da na Habasha, wadannan abubuwa kuwa su ne: Dangantakar tarihi da kuma Dangantakar taswira na kasashen biyu.

A bangaren tarihi kuwa, gogayya da juna tare da zumunta tsakanin al'ummomin kasashen biyu na tsawon tarihi su ne suka kara kusanto da su wuri daya, domin kuwa duka kasashen biyu, wato Misra da Habasha suna da tsohon tarihi da wayewa, sannan kuma dangantakar addini ta kara hada al'ummun kasashen biyu wuri daya, wanda hakan yake bayyana ta fuskar alakar majami'ar Habasha da majami'ar Kibdawa da take Misra, tun karni na hudu bayan haihuwar Annabi Isa (A.S), sannan bayan haka dukkanin Musulmai da suke kasar Misra da sauran kasashen Duniya na jinjina ga Habashawa bisa gudunmawar da suka bai wa Musulmai na kariya, bayan da suka yi hijira zuwa kasarsu a lokacin Musulunci na bako, inda Sarkin Habasha ya karbi bakoncin Musulmai yayin hijirarsu a karo na farko.

Amma a wannan lokacin da muke ciki, dukkanin kasashen biyu suna da rawa da suke takawa sosai wurin cigaban kasashen Nahiyar Afirka, babu mamaki a kan haka domin kuwa gamayyar kungiyar hada kan kasashen Afrika ta yi aiki da Misra wurin fafutukar samo 'yancin kasashen Nahiyar, bugu da kari ma, cibiyar kungiyar tarayyar kasashen Afirka na zaune ne a Adis Ababa na kasar ta Habasha.

Amma a sashen Dangantakar taswirar kasashe kuwa, dangantakar kasashen biyu na da matukar karfin gaske ta wannan sashe, domin kogin Nilu ne mabubbugar ruwan Misra da rayuwarta, wanda kuma shi ke alamta wayewarta a tarihinta, to akwai wani sashen na ruwan da yake biyowa ta kogin Habasha inda yake gangarowa ta sashen Nile Al'azrak har zuwa cikin kasar Misra.

A cikin shekaru na baya bayan nan kuwa, an samu cigaba sosai na dangantaka tsakanin kasashen biyu domin kuwa babu wata kasa (wacce ba ta Larabawa ba) da shugaban Misra Abdulfattah Elsisi yake yawan kai mata ziyara akai-akai kamar kasar Habasha.

Dangane da madatsar ruwan Nahda kuwa da kasar Habasha take ginawa, hakan ya sanya kasashen biyu a layin ziyarce ziyarce domin kuwa an sanya tsare tsaren aikin tare, da tuntubar juna tsakanin kasahen Misra da Sudan, da kuma Habasha, haka nan an cigaba da tattaunawa irin ta diplomasiyya tsakanin wadannan kasashen guda uku, a karkashin taron kolin kwamitin tuntubar juna tsakanin wadannan kasashe uku da suka hada da ministocin kasashen waje, da na ruwa da noman rani tare - kuma - da shugabannin leken asirin kasashen biyu.

SASHEN KASUWANCI :

Shi ma na daya daga cikin hanyoyin da suka kusanto da kasashen biyu wuri daya, domin kuwa musanyen cinikayyar da ke tsakanin Misra da Habasha na shekarar 2017 ta zarce dalan Amurka biliyan daya, har wala yau hannayen jarin Misra sun karu sosai a Habasha musamman a sashen wutan lantarki da kuma ruwan sha.

ZIYARCE ZIYARCEN SHUGABA ELSISI ZUWA HABASHA DAGA SHEKARAR 2014 ZUWA WATAN FABRAIRUN SHEKARAR 2019 :

Kasar Habasha ta rabauta da ziyarce ziyarcen shugaban kasar Misra Abdulfattah Elsisi a matsayin ta farko cikin kasashen Afirka, domin kuwa shugaban sau biyar (5) ya kai ziyara kasar Habasha, akwai wacce ya kai domin dangantakar kasashen biyu, ko kuma domin halartan taron kungiyar tarayyar Afirka, wannan ya dinga faruwa musamman a zangon shugabancin Elsisi na farko cikin shekaru Hudu (4) da ya fara daga watan Janairu na shekarar 2015 a taron koli na shugaban kasashen Afirka karo na 24, da kuma kammalawa a  watan Janairu na shekarar 2018, a taron kolin kasashen Afirka karo na 30.

JERIN LOKUTAN ZIYARCE ZIYARCEN :

1 - Ziyarar ranakun 29\30 na watan Janairu na shekarar 2015, domin jagorantar tawagar kasar Misra a taron kolin kasashen Afirka karo na (24) na tsawon kwanaki biyu wanda aka bai wa taken (Shekarar bai wa mata dama da kuma bunkasar yankuna kafin ajandar Afirka na shekarar 2063).

2 - Ziyarar ranakun 23\24 ga watan Maris na shekarar 2015, ita ce ta biyu zuwa Habasha, manufarta ita ce sanya hannu kan yanda ya kamata taswirar madatsar ruwar Nahda da Habasha ke ginawa ya kamata ya kasance, wannan ziyarar ta shugaban Misra ta zo ne bayan ta Sudan da shugaba Elsisi ya kai.

3 - Ziyarar ranar 30 ga watan Janairun 2016, ita ce ta uku, domin kuwa shugaban Misra ya jagoranci tawagar kasar Misra zuwa Adis Ababa domin halartan taron kolin kasashen Afirka karo na (26).

4 - Ziyarar ranakun 30\31 na watan Janairun shekarar 2017, ita ce ta hudu, domin a cikinta ne shugaban Misra ya jagoranci tawagar kasar Misra domin halartar taron kolin kasashen Afirka karo na (28) a Adis Ababa, inda shugaban Misra ya jagoranci shugabannin kasashen Afirka ma su kula da gurbacewan yanayi.

5 - Ziyarar ranakun 27\29 ita ce ta Biyar, manufarta kuwa ita ce halartan taron kolin kasashen Afirka karo na (30) wanda ya gudana a Adis Ababa, a yayin wannan ziyarar shugaban Misra ya jagoranci taron koli na majalisar tsaron kasashen Afirka.