Dangantakar tsakanin kasar Misra da kasar Kamaru
Laraba, Janairu 09, 2019
Dangantakar tsakanin kasar Misra da kasar Kamaru

Dangantaka tsakanin kasar Misra da kasar Kamaru tana da karfin gaske, ta kowace fuska, kasar Misra daya ce daga cikin kasashen da suka fara bude ofishin jakadancinsu a kasar Kamaru domin karfafa dangantakar diplomasiyya da kasar, tun bayan samun 'yancin kai a shekarar 1960. Misra tana da muhimman abubuwan da take gabatarwa a Kamaru ta hanyar kamfanonin Misra da suke aiki a sassa daban-daban na Kamaru kama daga sashen ayyukan raya kasa, makamashi, da kuma cinikayya, bugu da kari akwai kimanin malamai 35 na Jami'ar Al-Azhar da ko’ina cikin birane da ƙauyuka 22 na kasar Kamaru.

Dangantakar da take tsakanin kasashen biyu ta dauki wani sabon salo na bunkasa a cikin shekaru hudu na baya bayan nan; sakamakon samun gwarzon shugaban kasa irin shugaba Abdul Fattah El' Sisi wanda ya yi fice cikin shugabannin Afrika.

Dangantakar Siyasa:

Dangantakar siyasa tsakanin kasashen biyu tana da kyau sosai, domim kuwa kasar Misra ta kasance cikin kasashe na farko da suka bude ofishin jakadanci tare da tura ma'aikatan diflomasiyya zuwa Kamaru, sannan kasar  Kamaru na nuna goyon bayanta ga duk wani kudurin kasar Misra tare da manufofinta a kungiyar tarayyar Afirka da na Majalisar Dinkin Duniya, sannan kasar Kamaru tana nuna goyon bayanta ga duk wani dan takarar da Misra ta gabatar a matakan kasa da kasa.

Musayan ziyarce ziyarce:

Ziyara tsakanin jami'an kasar Misra da na kasar Kamaru ta kasance mai muhimmanci gare su, domin akwai jami'an Misra da suka kai ziyara Kamaru, kamar yanda aka samu jami'an Gwamnatin kasar Kamaru da su ma suka ziyarci kasar Misra, wanda hakan ya kara karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.

A ranar 4 ga watan Satumba na shekarar 2010, mataimakin Ministan Harkokin Waje na kasar Misra mai kula da al'amuran kasashen Afrika, jakada Hamdi Sanad Loza, ya ziyarci kasar Kamaru, dauke da sakon shugaba Abdul Fattah El' Sisi, zuwa shugaban kasar Kamaru Paul Biya. Sakon ya kunshi abubuwan da za su inganta dangantaka tsakanin kasar Misra da Nahiyar Afrika, tare da manufofin kasar Misra game da al'amura da suka shafi yankuna da ma kasashen Duniya baki daya.

A watan Afrilu na 2017, Ministan  Kasuwanci da Ma'adinai na Kamaru ya ziyarci Misra. A lokacin ziyarar tasa ya samu daman hanawa da Ministan Masana'antu da Kasuwanci, da na Ciniki, da kuma Ministan Man fetur da Ma'adinai na kasar Misra.

A Ranar 17 ga watan Aprilu na shekarar 2017 Ministan Man fetur da Arzikin kasa na Misra Tarek El-Molla ya karbi bakwancin Ernest Gabon Abobo Ministan  Ma'adinai Masana'antu da Cigaban Kimiyya na Kasar Kamaru, Kasashen biyu sun tattauna ne akan yanda za su bunkasa dangantaka tsakaninsu ta fuskar man fetur da ma'adinai da kuma sufuri da albarkatun kasa, bugu da kari tattaunawar tasu ta shafi musayar kwarewa akan abubuwan da suka shafi yanda kasashen nasu za su ci gajiyar  albarkatun ma'adinan da suke da su.

A ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2017, ministan tsaron kasar Kamaru Joseph Beti Assomo ya ziyarci Misra, A lokacin ziyararsa ya gana da Janar Sudqi Sobhy, babban kwamandan sojojin kasar Misra kuma ministan tsaro da kera kayan yaki. Kasashen biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu tare da kokarin inganta dangantakar da take tsakaninsu. 

Tattalin Arziki :

Dangantakar cinikayya tsakanin kasashen biyu tana da matukar rauni sakamakon rashin sanin  gurabun da kasashen biyu ya kamata su rinka zuba hannayen jari cikin kasashen nasu, bisa kiyasi hada-hadan kasuwancin da take tsakanin kasashen biyu ba su wuce Dalan Amurka miliyan Bakwai ba, mafi yawan kudin sun fito ne daga sashen kasar Misra. Kamfanin 'yan kwangilar Kasashen Larabawa suna taka-rawa a kasuwar Kamaru inda yanzu haka kamfanin yake gudanar da wasu muhimman ayyuka biyu a kasar, wanda na farko ya fara daga Yaounde - Kribi, wanda yana gab da kammaluwa, sannan kuma gina babbar kofar shiga fadar Gwamnatin kasar Yaounde ta yammaci. Akwai manyan damammaki ga Kamfanonin 'yan kwangilar kasashen Larabawa idan aka yi la'akari da yanda  shugaban kasar Paul Biya yake da shi na gabatar da wasu muhimman ayyaukan raya kasa kafin zaben shugaban kasa a shekarar 2011, baya ga ayyukan shimfida hanyoyin da za su hada tashar jiragen ruwa na Douala da yankunan kasashen da suke tsakiyar Afrika.

Bugu da ƙari, kamfanin El Sewedy Cables na taka-rawa a kasuwar Kamaru ta hanyar aikin gine-ginen madatsar ruwa domin samar da makamashi har guda uku a garuruwan Bloba, Balmayo da Bamenda wanda zai samar da kimanin migawat 40, wanda hakan zai lakume kudi har Dalan Amurka Miliyan 40.

Tsarin kwangila:

 • Sanya hannu a wata Yarjejeniyar ta kasuwanci tare da biyan kudi a ranar 19 ga watan Yuli ta 1961, wacce ta fara aiki tun 19/12/1961.
 • Sanya hannu akan yarjejeniyar zirga-zirga tsakanin kasashen biyu a ranar 3/6/1966, sannan ta fara aiki a ranar 07/05/1967. 
 • Sanya hannu kan Yarjejeniya a sashen al'adu da fasahar fanni wanda aka sanya hannu kan haka ranar 22 ga watan Nuwamba ta shekarar 1969, wanda ta fara aiki a ranar 22 ga watan Janairun shekarar 1977. 
 • Sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci a ranar 17 ga watan Nuwamba ta shekarar 1977, sannan ta fara aiki a matsayin doka ranar 20/3/1979. 
 • Sanya hannu kan Yarjejeniyar hadin kai ta hanyar fasaha tsakanin Ƙasar Masar don Sadar da Harkokin Kasuwanci tare da Afirka da Gwamnatin Kamaru, an sanya hannu kan haka a shekarar 1995. 
 • Sanya hannu kan Yarjejeniyar zirga zirga tsakanin kasashen biyu da aka sanya hannu a shekarar 1998, sannan dokar ta fara aiki ranar 5/3/2002. 
 • Kulla Yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a sasehn yawon bude ido a ranar 24/10/2000 amma kasashen biyu ba su sanya hannu kan hakan ba.
 • Kulla Yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kasashen biyu a ranar 24 ga watan Oktoba na shekarar 2000, sai dai sassan biyu ba su sanya hannu kan hakan ba.
 • Sanya hannu kan yarjejeniyar ayyukan Sadarwa a ranar 24/10/2000, wanda ya fara aiki a matsayin 24/10/2000. 
 • Sanya hannu bisa yarjejeniya kan al’amuran al'adu da Harkokin Kasuwanci tsakanin shekarun 2000-2002, sannan an sanya hannu kan haka ranar 24/10/2000, sannan ta fara aiki doka ranar 24/10/2000. 
 • Sanya hannu kan Yarjejeniyar ƙarfafa zuba jari tare da sanya ido kan haka a ranar 24/10/2000, sai dai Gwanatin Kamaru ba ta sanya hannu kan hakan ba. 
 • Sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a fannin makamashi da lantarki tsakanin gwamnatin kasar Jumhoriyyar Masar ta Larabawa da gwamnatin Jamhuriyar Kamaru, sun sanya hannu kan haka ranar 4/12/2010. 
 • Sanya hannu kan Yarjejeniyar hadin gwiwar fasahar tsakanin Gwamnatin Misra da Afirka tare da gwamnatin Kamaru, an sanya hannu kan haka a ranar 21.04.2010
 • Ƙulla yarjejeniyar fahimtar juna kan tsarin kimiyyar siyasa tsakanin Misra da Kamaru, an sanya hannu kan haka a ranar 21 ga watan Afrilu ta shekarar 2010. 
 • Sanya hannu kan yarjejeniya yin aiki tare tsakani Hukumar cin gajiyar yankuna masu fadi da zuba hannayen jari ta kasar Misra tare da Hukumar karfafa zuba hannayen jari ta kasar Kamaru (CIPA), an sanya hannu kan haka ranar 21 ga watan Afrilu na shekarar 2001. 

Dangantakar Al'adu:

Jami'ar Al-Azhar na taka muhimmiyar rawa a bangaren raya al'adu tsakanin kasashen biyu, haka kuma ta samu nasarar kulla yarjejenita tare da Ma'aikatar kula da Ilimin firamari na Kamaru kan aikawa da malaman koyar da Harshen Larabci kimanin 20 domin karantarwa a makarantun koyar da Larabci da Faransanci ta kasar. 

Har ila yau, akwai tawagar malamai har guda 32, daga Jami'ar Al-Azhar, da suke a ko’ina a cikin garuruwa 10 na Kamaru da suke aikin koyar da ilimin Addinin Musulunci, haka kuma Jami'ar ta Al-Azhar ta bai wa 'yan asalin Kasar ta Kamaru gurabun karo ilimi tare da tallafi ga dalibai har 10 don koyon Harshen Larabci da nazarin kan ilimin Addinin Musulunci a Jami'ar ta Al-Azhar Al-Sharif.

Dangantaka a sasehn Fannonin ilimi da fasahar al'adu:

Hukumar bayar da tallafi akan fasaha da fannonin ilimi ta kasar Misra tare da ta Afirka a Kamaru: 

Wannan Hukuma ta bayar da tallafi kan fasaha da fannoni ta kasar Misra tare da Afirka ta bai wa Kamaru gudunmawar wasu kwararrun malamai guda 7, domin yin aiki a kasar, da suka hada da (likitoci hudu da malamai uku na Larabci), har wala yau, Kasar Kamaru ta bukaci karin yawan malaman Larabci a jami'oin Buea da Marwa bayan haka, sannan ta sake neman karin yawan likitoci kamar yanda ta nemi karin malaman Larabci a farko.

A shekarar 2008 an bayar da kayayyakin aikin asibiti kyauta ga wani asibiti na gidauniyar matar shugaban kasa Chantal Biya. Haka nan Daraktan kula da Asibitin ya bukaci karin tallafi daga Hukumar bayar da tallafin fannoni da fasahar al'adu na Misra tare da Afrika don samar da karin kayayyakin aikin asibiti a kasar.

Haka kuma Asusun  na bayar da tallafin ya amince da bayar da wasu kayayyakin bukata ga Makarantar kasa da kasa na koyon lamuran Tsaro a kasar ta Kamaru tare da wasu kayayyakin kimiyya da fasaha.

Sannan Asusun ya shirya bayar da horo na musamman kan wasu darussa da dama da suka hada da fannin diplomasiyya, shari'a, tsaron cikin gida da waje, unguwar zoma, da kuma sashen haihuwa, da tsarin noman shinkafa na zamani da kuma yawon bude ido.

Tushen wadannan bayanai :

Runbun adana bayanai na Hukumar kasar Misra.