Dangantaka tsakanin Misra da Chadi
Lahadi, Maris 17, 2019
Dangantaka tsakanin Misra da Chadi

Dangantaka tsakanin Misra da Chadi

Gabatarwa:

Akwai kyakyawar dangantaka tsakanin Misra da Chadi. A hukumance da kuma al'umar kasashen guda biyu, yayinda Chadi tayi kwadiyin kiyaye dangantakar ta da Misra duba da rawar da Misra ke takawa da kuma matsayin a nahiyar Afrika, hakan ya kasance tun lokacin da Misra ta samu 'yancin kai a shekara ta 1952.

Dangantaka tsakanin Misra da Chadi tana da dogon tarihi, kasancewarta kasa mai mahimmaci dangane da tsaro al'ummar kasar Misra, tana da iyakoki tsakanin da Sudan da Libya, tarihin kasar Chadi yana komawa ne zuwa lokacin manya manya masarauta, yayin da aka samu kafuwar masarauta Musulunci kuma ta kasar Larabawa ta farko a Chadi a karni na biyu bayan hijira da karni na takwas bayan miladiyya, sunanta "Masarautar kanimi" a arewa masa gabas da tafkin Chadi, sannan mulki ta ya fadada a karni na uku bayan hijira, har sai da ta mamaye yankin Sudan ta tsakiya gaba daya, har zuwa lokacin da ta fada karkashin mulkin mallakar Faransa daga shekara ta 1920 har zuwa lokacin da samu 'yancin kai shekara ta 1960.

Musayar ziyarori:

Ziyarar shuga Abdulfattah El-Sisi zuwa Chadi a watan Agusta shekara ta 2017.

  • Ziyarar injiniya Sharif Isma’il mai taimaka wa shugaban kansa akan ayyukan kasa da kuma dabaru, kasancewarsa dan aike na musamman daga shugaban kasa a 16/ 10/ 2018 & a ziyararsa zuwa Chadi. Ya samu tarba a yayin ziyarar daga Ashta Salih Damini sakatariyar kasa ta al'amuran kasashen waje da ci gaba Afrika da kuma taimakekeniyar kasa da kasa ta Chadi, haka kuma ya gana da ministan man fetir na kasar Chadi.
  • Shugaban kasa Chadi Idris Debi ya kai ziyara zuwa Misra a watan Disamba 2014. Ziyarar ta samu sa hannun kasashen biyu akan takardar fahimta dangane da taimakekeniya a bangarorin noma da kuma lafiya.
  • Mai girma tsohon shugaban majalisar ministocin kasa Misra ya kai ziyara zuwa Chadi, akan watan Afrilu 2014 ziyarar ta sa hannu akan yarjejiniya a bangaren noma.

 Musayar kasuwanci

  • Bangaren man fetur: Kasashen biyu sun kulla yarjejeniya akan shirya ziyarar aiki ta wasu masana na kasar Misra, domin duba bukatun kasar Chadi don shirya da kwasa kwasai domin koyar da mutanen Chadi wadanda suke aiki a ma'aikatar man fetur.
  • Bangaren yawon bude ido: Kasashen biyu sun tabbatar da hanzarta karanta ayyukan yarjejeniya domin taimakekeniya bangaren yawon bude ido wanda aka gabatar a Chadi.
  • Banagare kasuwanci: Bangaren kasuwanci kasar Misra ya mikawa abokansa na kasar Chadi aikin daftarin fahimta dangane da hadin gwiwar kasashen biyu a kasuwannin baje koli na kasa da kasa.
  • Bangare kwangiloli: Kanfanin kwangiloli na Arab Contractors yana da matukar kari a Chadi.

 Danganta ta fuskar Ilimi da kuma Al'adu

Danganta ta fuskar Ilimi da kuma Al'adu:

  • Chadi ta kasance kasa mafi girma a Afrika dangane da malaman da ake tura wa kasar daga jami'ar Al Azhar wanda adadinsu ya kai malami 40. Wanda Al Azhar din ke kula da su domin karantarwa, haka  Al Azhar din tana biyar da tallafin karatu a matakai biyu, matakin sakandire dana jami'a, haka kuma kasar Chadin tana samun wani kasa na tallafin karatu gaba da jami'a.
  • An zabi malamai uku daga jami'o'in Misra domin aiki a kasar Chadi domin karfafa tsangayoyin ilimi, hakan ya zo ne domin bukatar ma'aikatar ilimi mai zurfi ta kasa Chadi.